BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hararanta tayi tana d’an kai mata duka a kafad’a tace “Haihuwata ko haihuwarki dai.”

“Me?” Ta fad’a da k’arfin bala’i, ba iya gabanta bane kawai ya fad’i har jinin jikinta ma saida ya matuk’ar hawa, dariya ta mata tace “Idan Amna ta haihu ai Hamna ce ta haihu.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Wai Allah, amma dai cikin nan naki yan biyu ne ko? Wannan abu haka.”

Cikin shagwab’a tace “Shiyasa na so nayi éco (scanning) amma yah Ammar yace sam bai yarda ba, yanzu haka gobe zan koma awo har na cinye sati biyun da aka bani, nak’udar tsaye kawai nake fama da ita.”

“Karki damu, ai da sati biyu biyu ma kina iya cinye wata biyu, kawai ke dai karki zama lusara mai son jiki, ki dinga tafiya mai tsayi saboda ko nak’uda ta taso miki ma zata zo miki da sauk’i, amma kin fara zubar da ruwan zak’i?”

Waro ido Amna tayi a hankali sai kuma ta k’ank’ance su tana kallonta da mamaki, ba tare data daina mamakin ba tace “A ina kika san haka ke kuma sai kace wacce ta tab’a haihuwa?”

Tsuru Hamna ta mata da ido, saida ta k’ak’alo abinda zata fad’a kafin tace “Kiji
sai kace ba mace ba, to wannan ne sai mace ta haihu zata sani.”

Jakarta ta d’auka suka nufi falon Hajia tana fad’in “Muje ki gaishesu sai muje b’angarenmu musha hira.”

Sallamarsu tasa wanda ke falon suka kallesu, yan biyu ne dai gasu amma duk sun canza, Hamna ta k’ara haske kan wanda take da a farko, jikin nan nata duk da tana shan wahala a wurin Aissata amma ya kwanta luf dashi, Amna kuma ta k’ara duhu sai kuma cikin yasa tayi muni ba kamar kafin ta d’auki cikin ba tsaf da ita, ana gaisawa ana mamakin tahowarta katsam haka babu sanarwa, Ummy na d’aki take jin kamar maganarta, tana lek’owa ta ga dai ita ce da gaske, saida suka gaisa da kowa sannan ta wuce d’akin Hajia dan tun sallah la’asar bata fito ba jikin ya d’an k’ara nauyi sosai bata san dai nunawa ne, kamar mai sand’a ta shiga tana sallama har ta zaune kusanta a k’asa ba tare data yarda sun had’a ido ba, bata amsa sallamarta ba bare gaisuwarta tana mamakin dawowarta bada izininta ba.

Cikin wani irin amon murya tace “Meya dawo dake? Waya baki izinin dawowa ba tare dana amince ba? Ke ce kika zab’i dawowa ko kuma shi Gambon ne yace ki dawo?”

Cikin sanyin murya tace “Gaskiya Hajia basu san da fitowa ta ba, kawai na gaji da zaman can ne saboda tanti Aissata ta mayar dani kamar wata baiwarta, kuma Abba ma har Allah ya isa ya min idan na b’ata mata rai, jiya ma mun samu sab’ani ne shiyasa na tahowa ta dan nasan Abba na iya dukana idan ta fad’a masa na mata rashin kunya.”

Kallonta Hajia tayi ta mik’e tsaye cikin b’acin rai ta gaura mata mari a fuska, dafe kunci tayi da sauri ta k’ara sunkuyar da kai, cikin masifa tace “Hamna kinsan dalilin da yasa na turaki can? To saboda ina so nasan abinda ke faruwa acan d’in ne, ina so naga abinda yasa bata so kowa ya rab’eshi sai ita kad’ai, amma da yake mahaukaciya ce ke shine kika dawo min haka ko? To tashi ki bani wuri, ni kuma zanje da kaina nayi aikin dan ba zan haifi d’a a cikina ba kuma wata ta fini cin moriyarshi ba.”

Fita tayi ita kuma ta shiga masifa tana fad’a, tana fita d’akin Ummy ta shiga, tana ganinta bata tsaya komai ba tace “Hamna meya dawo dake? Ya akayi kika zo baki sanar min ba?”

Marairaicewa tayi tace “Ummy wallahi Tanti Aissata ta addabeni, kawai ta b’ata min rai ne jiya shiyasa na baro mata gidan.”

“Amma me Hajia tace miki da kika taho ba da umarninta ba?”

Tab’e baki tayi tace “Tana can tana masifa mana, wai zata je da kanta Niamey d’in ta ga wace irin rayuwa suke, wallahi da za taji tawa da sai nace karta tafi, dan matar nan da gangan ma zata iya d’ora mata hawan jini.”

Murmushi tayi tace “Hamna ince dai ba yaron nan yasa kika dawo ba ko?”

“A’a Ummy, kawai na dawo ne.” Ta fad’a idonta akan Shureim dake bacci, fitowa tayi ta d’auki jakarta ta kai d’akinsu, saida tayi sallah magriba tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar kanti da d’an kwalinta sannan ta fito, Farisa tasa ta gyara mata d’akinta ita kuma ta sauko k’asa, saida ta shiga ta ga Zeituna da Fatima masha Allah yarinyar kamar ka fizge a hannunta ga uban gashi, suna gaisawa ta fito ta nufi wajensu Umaimah.

Mamaki ne ya kusa kasheta data shiga d’akin, yarinya ‘yar k’walisa uwar kwalliya da tsabta, amma wai ita ce zaune k’asa da d’aurin k’irji tana cin ‘ya’yan tsamiya tana tofar da yawu, kan nan nata yayi daud’a ya tsufa abun ba kyan gani, daga tsaye take k’are mata kallo tana mamaki, tafin k’afarta abinka ga farar fara yayi duhu, a take a wurin taji Umaimah ta fita a ranta, dan duk yanda kake ji dai zaka daure ka gyara jikinka tunda har kana iya cin abu kuma kana taka k’asa, ko baka gyara dan komai ba ka gyara dan kar namiji ya ga makusarka. Daga nan tsaye suka gaisa ta wuce b’angaren yer uwarta, ba wai son kai ba ko dan tana yer uwarta, amma tana dosa b’angaren ma k’amshin turaren tsintsiya ne ya mata maraba.

Tana shiga ita ma zaune take k’asa ta mik’e k’afafu da suka kumbura sumtum, cikinta yafi na Umaimah girma nesa ba kusa ba, cikin nutsuwa take cin bredinta mai yanka nan tana shafeshi da la vache qui rit, zaune tayi ta fizge bredin tana fad’in “Sakarya kawai, kina da ciki kina ta fama da abubuwan da zasu bud’a miki yaronki a cikin cikin, ki zo kisha wahala kafin ki haihu.”

Hannu ta tara mata tace “Taimaka ban wannan na k’arasa to.”

“An k’i.” Ta fad’a tana d’auke d’an kwalin ta aje bayanta ta kalleta tace “Jamila wace asibiti take?”

Cike da shak’iyanci ta wani murgud’a mata baki tace “Asibitin mijina mana.”

Sai kawai taji gabanta ya fad’i daga anbaton mijinta, da mamaki ta kalleta tace “Anya kuwa Amna bai koya miki iskanci ba, ke ma fa kin lalace yanzu.”

“A’a ni bai koya min ba, kawai dai abun ne kamar a karatu, yana biya min ni kuma na hardace shi a kaina.”

Tab’e baki tayi tace “Lallai mai miji.” Amna ce tace “Yer uwa dama ina so ki zo, akwai matsala fa…”

Duk da ta kai k’arshen abinda take son fad’a amma saida ta juya ta kalli k’ofar da taji sallamarshi. Yana shigowa ya tsaya kamar wanda aka dakatar dashi, idonshi cikin nata wacce k’afafunta ke tank’washe tana jujjuya wayarta dake hannunta, *sanyin idaniya*, yau ne ya tabbatar da kalmar sanyin idaniya da ake fad’a, domin kuwa sanyin nan bai tsaya iya idonsa ba saida ya zarce har k’ark’ashin zuciyarsa ya isar da sak’on cewa wata mai matuk’ar mahimmanci ta iso wacce akayi kewarta na wani lokaci, dawowa yayi hayyacinshi ya fara takowa yana sauke jakarshi daga kafad’a ya kalli Amna yana fad’in “Duniyata bak’uwa kikayi?”

Kallon Hamna tayi tana dariya tare da bata gefen fumcinta da taga ya nufota tasan me zaiyi, sumbatarta yayi tana cewa “Sannu da zuwa, ya aiki, kayi hak’uri nayi nauyi ba zan iya tashi tarbanka ba.”

Jakar ya aje kan kujera ya zauna daf da Amna yana rik’ota jikinshi yace “Je sais ma chérie, ya kika wuni?”

Cikin shagwab’a tace “Lafiya lau, kai fa?”

Hamna ya kalla wacce a taswirar zaman nasu suna kusan juna ne dukansu inda shi da ita suke fuskantar juna Amna ce kawai ta shiga tsakaninsu, yana kallon ita kuma tana dalla masa harara, wani bala’in haushinshi taji saika mata yake, yanda har taji ya fara tasiri wajen jin haushin yer uwarta ma data biye masa, akan me zasu raina mata wayo haka? Dan ita bata da auren ko me? D’auke idonta tayi daga kansu sai Ammar ne da yace “Ke baki iya gaishe da mutane ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected