BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Dreba ta samu ta bashi takardar da aka rubuta mata abun buk’atarsu tace “Ka samu Hassan zai baka kud’i ka siyo mana duk abinda ka gani rubuce anan.”
Da ladabi ya amsa da “To Hajia, insha Allahu.” Juyowa tayi shima ya juya ya fita dan isar da sak’onta.
*Zuwa yamma* gida ya fara nuna alamun ana hidima kuma babba, domin kuwa kujeru ne aka cika gidan dasu aka jerasu gwanin sha’awa, sannu sannu mutane suka fara hallara har gida ya fara batsewa, b’angare d’aya babbar redio ne aka kunna yana tashin kid’a, ana cikin haka amare suka dawo daga wurin wunin k’umshi, tubarkallah yanda gidan ya cika kai kace yau ne bikin, a haka kuma wankan amare ne kawai za ayi, kuma yawan mutanen ya samo asali ne saboda kowane b’angare da na shi dangi, dan haka gida ya cika mak’il har aka shirya amare aka tafi wurin wanka a gidaje daban daban, sai bayan magriba aka dawo da amare gida. Shiri na musamman aka musu kowace a cikin tsadadden leshe na gani na fad’a, Amna dake cikin leshenta kalar pink tayi masifar kyau, a haka aka fito dasu wajen bidirin bayan an turaresu da turaren jiki, duk da rincab’ewar da wurin yayi ana fitowa dasu kowa ya mayar da kallonshi kansu, Umaimah ce a gaba sai Jamila tsakiya, Amna na baya tare da Hamna wacce ita ma ke cikin leshe kalar na Amna sai dai d’inkin ya banbanta da kuma shirin, amma daga d’aurin kallabi da jaka da takalama sark’a da yan kunnai duk iri d’aya ne, amma kwalliyar fuskar Amna da kuma ashaokin dake kafad’ar ta ya banbantasu, Hamna kuma yanda d’inkin ya fito da ita da manyan d’uwawunta ga uwar atach d’in data gabza akai kamar tayi magana tasha kitso, d’aurin d’an kwalin kusan saman rabin kanta ne kawai yake, hakan yasa zaka iya gane kitson dake kanta da kuma kitso k’waya d’aya da alayi da kalar bleue d’in atach.
Akan kujeru aka zaunar dasu inda Hajia ke tsaye gabansu ta kalli su Zeinabu tace “Ku fito da yayanku.”
Wani kallo Zeinabu ta mata a ranta tace “Kaji wai mu fito da yayanmu , mazan fa take nufi.” A zahiri kuma jinjina kai tayi tace “To Hajia.”
B’angaren samarin ta nufa ita kad’ai, tana zuwa ta shiga da sallama saboda k’ofar bud’e take da abokanansu ciki, tana shiga suka gaisheta kafin tace su fito, nan suka fito suna ta ihuce ihuce da tsokanar angayen irin dai rahar nan ta samari, suna zuwa Junaid ya tsaya ya turo Amar gaba yana fad’in “Ku wuce ku, ni ina nan tunda babu sarauniyar sai sarki kawai.”
Gwalo Amar ya mishi yace “Gwauro kenan, mu dai munji dad’in mu.”
Ammar dake bayansu ya k’urawa Hamna ido haushi na kashe shi a wurin, tambaya ya ma kanshi “Akan me Hamna zata fito haka babu mayafi? Me yasa za tayi shiri kamar amarya ita ma?”
Hajia ce ta juyo garesu tana musu kallon ku taho mana, dukansu k’arasawa sukayi suka zauna har da Junaid d’in dan har da kujerarshi a ciki, haka suka jera su bakwai a wurin masha Allah, kamar yanda Hamna ke bayan yar uwarta tsaye kamar wata mai tsaronta, hakanne yasa Ammar d’ago kanshi ya kalleta yace “Ke dan ubanki fita daga kaina, kin min wani k’arere dake a baya.”
Amna da kanta ke k’asa a hankali ta saci kallonshi, masha Allah ta fad’a a ranta ganin wani kyau da yayi cikin chadda kalar ruwan k’asa, karin hular shi da yanda ta zauna mishi a kai sun masifar dacewa da fuskarshi, ga uwar k’asumbarshi dake ta k’yalli alamar tasha gyara, mayar da kanta k’asa tayi yayin da taji Hamna na fad’in “Malam babu ruwanka da tsayuwata anan, dan kai na tsaya ba dan yer uwata ne, idan zan tsaya anan dan kai ne wallahi sai dai dan na zama ajalinka ne.”
Lumshe ido Amna tayi jin har yar tsamarsu ta kai haka, inda Ammar ya gumtse baki yana mata murmushin iya shege ya sake kallonta yace “Idan naje lahira zan siyo miki kankana, nasan ta can tafi tanan komai, asha a k’ara zak’i.”
Kashe mata ido d’aya yayi tare da yi mata gwalo, haushi ne yasa Hamna tunzura ta zura hannu ta ture hular dake kanshi ta fad’i, da fari a hassale ya kalleta da niyyar aikomata ashar, amma ganin fuskarta a had’e sai kawai yayi niyyar yin maganinta cikin ruwan sanyi, Husseina ce tace “Ke Hamna lafiyarki kuwa, ya zaki ture hular ango?”
Hassana yar uwar Husseina ce ta d’auko hular zata saka mishi tana fad’in “Ai kinsan halinsu, in suka had’u kamar b’era da mage suke.”
Da sauri ya janye kanshi yana wani shak’iyin murmushi yace “A’a Hajia bana so, tunda dai k’anwar matata tace hular nan bata min kyau ba to na hak’ura da ita.”
Hassana ce ta kalli Hamna data saki baki tana kallonshi tace “Ke kuma ina ruwanki da shirinshi to? Kika sani ko ya ma amaryar ita?”
Ammar ne yace “To ai Hajia nasan ita ma bata mata ba, ko kin manta yan biyu ne? Zuciyarsu ma d’aya ce.”
Tsaki Hajia tayi ta matso kusansu ta dungurar mishi kai tace “Shege uban surutu, a wajen hidimarku ma ba zaka rufewa mutane baki ba, idan ka b’ata min rai sai dai ka bar wurin nan ba tare da an maka wankan turaren ba.”
Murmushi ya mata yana dafe da inda ta rank’washeshi yace ” Babu fargaba a tare dani, a cikin dangina nake wanda nasan zasu iya yi min.”
Wani tsakin ta kuma yi ya bi bakinta da kallo yace “Hajia, Allah ja-leb’en nan da kika shafa ya miki kyau, ki daure dan Allah ki sumbace ni ko sau d’aya ne, kar ya fita a banza baki sumbaci baki na ba.”
Husseina da Hassana dariya suka saka hakan yasa ran Hajia b’acewa dan har yanzu ba k’aunarsu take ba, kwalaben turarukan dake hannunta masu matuk’ar tsada da k’amshi ta jefa mishi a k’irji ta juya da sauri ta bar wurin rai a b’ace, ganin haka da Ummy tayi ta tabbatar Ammar yayi halin, duk da bata ji me ya faru ba amma tasan aikinshi ne, girgiza kai tayi ta wurgo mishi da harara daga inda take, Hamna da har yanzu ke bayansu ce tace “Kaga bak’in halinka ya fara shafar yer uwata tun yanzu, gashi kasa Hajia ta tafiyarta bata fesa muku turarukan ba, anji sanyi dai wallahi.”
Ba tare daya kalleta ba tace “To ai bana da bargon rufa ne, kuma kinga kune da jin takaici bani na ba, tunda babban abun kunya ne ace babban jikan Alhaji Suley baya da bargon rufa idan yana jin sanyi.”
Hannun Amna ya kamo ya matse sosai yana murzawa ya kafeta da ido yace ” Amna, nasan kinsan wanene ni, kuma a haka kika amince da zaki aure ni, hakan na nufin kenan zaki iya zama dani a duk yanda nake?”
Kallonshi Amna tayi yayin da take lumshe idonta a hankali wanda suka sha dogon gashin daya dace da idonta ganin sha’awa, wani sauk’akk’en murmushi tayi ta d’an gyad’a mishi kai alamar eh, murmushi ya mata wanda ya k’ara bayyanar da kyawunshi yace “Karki damu to, *insha Allahu da sannu zamu samu masu son mu a duk yanda muke*.” Yana fad’a ya juya kanshi a hankali ya kalli inda Ummy ke tsaye, suna had’a ido ta kawar da kanta tana jan tsaki, murmushi yayi ya d’auke kanshi, duk abinda ya faru a idon Zeituna, da sauri ta matso ta d’auki turarukan da suka fad’i k’asa ta mik’awa Husseina tace “Hajia ke ki fesa musu mana tunda Hajia ta tafi.”
Girgiza kai tayi tace “Aa ‘yar nan rufa min asiri, a gaskiya ina so ayi bikin nan lafiya a gama lafiya, bana son abun magana.”
Hassana ce tace “Kira Sa’ada mana saita fesa musu, ita ya dace ai dama.”
Husseina ce tace “Ko kuma Zeinabu ba ko Soueiba.”
Kallon inda su Zeinabu suke tayi ta taka da niyyar zuwa ta kai musu turarukan amma abun mamaki sai Zeinabu ta dakar da ita tace “A’a gaskiya, su Hajia ma sun saka bare kuma mu, auren ‘ya’yanmu ne za ayi, gaskiya karki ja mana jarfa.”