BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bata uya juyowa ba sai kai data girgiza masa alamar a’a, sakinta yayi zata shige yace “Tare da Shureim zamu tafi, Ummy ma ta amince.”

Juyowa tayi da sauri ta kalleshi sai hawayen suka taho mata, da sauri ta matso kusanshi kamar zata fad’a jikinshi sai kuma ta tsaya, marairaicewa tayi duk tayi kalar tausayi tana matsar ido cikin raunin muryar kuka tace “Ammar ka hutar dani dan Allah da zuciyata, na gaji wallahi Allah ba zan iya jura ba, ka daure ka dinga yin nesa dani kaji.”

Shi kanshi saida ya lumshe ido yanda ta k’arashe maganar, kallonta yayi da idon fahimta da kuma basira, idan ya fahimta daidai abinda ke d’awainiya dashi shi yake galabaitar da ita, to amma ya zasuyi? K’addararsu ce haka, yanda suke kallon juna ne yasa Hamna saurin kawar da kanta ta juya da gudu ta shiga ciki, saida Hajia ta bita da kallo ita dake zaune wurin, tana shiga d’aki ta fad’a kan gado ta fashe da kuka, sosai take ruzgar kuka kamar wacce aka wa mutuwa, ko wanka bata iya tashi ba saida taji wayarta na kuka, fito da iya tayi a jaka ta duba, wani Alhaji ne da yake matuk’ar sonta yake bibiyarta amma Allah yasa ta kasa bashi ajiyar zuciyarta, ba wai shi kad’ai ba akwai irinshi bila adadin da suke bibiyarta amma ta kasa bawa ko d’aya dama, aje wayar tayi ta ci gaba da rera kukanta da tunanin mafita a rayuwarta.

*Da safe* tsaf suka shirya dan tafiya, kaya kala d’aya Ammar yasa tare da yaran har Shureim, Amna ma cikin wani had’add’en leshe ta shirya kalar kwalliyar aikin kayansu, suna gaishe da iyayen suka musu sallama suka fito, har zai bud’a motarshi yaji Amna na fad’in “Yer uwa dama baki fita ba? Ai na d’auka kin tafi shiyasa ban shiga d’akinki ba.”

Ko kallonta ba tayi ba tace “Amma ai da kin tambayeni da an fad’a miki ina nan ko bana nan.

Juyowa yayi ya kalleta, kamar dai yanda yanzun tafi zama yanzu ma hakane, doguwar rigar bak’in leshe ce jikinta d’inkin simple amma ya hau jikinta sosai musamman wajen mazaunanta, d’aurin d’an kwalin ma kawai tayi shi ne simple, fuskarta ma tayi fes da ita babu komai data shafa mata, amma k’amshin tattausan turarenta kad’ai zai iya kwantar maka da hankali, wayarta gyalenta da makullin mota duk a hannunta suke, Shureim ne ya tafi wajenta ta d’aukeshi tana mishi magana, matsawa tayi kusanta tace “Yer uwa idan baki da aiki sosai me zai hana ki zo muje tare, Mama zatayi farin cikin ganinmu gaba d’aya a tare.”

Kallonsu tayi dukansu, Ammar k’arami ne ya zo kusanta shima yana d’aga hannu sai Amna dake mak’ale wajen Mamanta, murmushi tayi ta kalli Ammar tace “Sai dai muje a mota ta, bansan ko mijinki ya lak’a min bom d’in da zata tashi dani ba.”

Kallon daya mata tare da cije leb’enshi yana wani shegen murmushi yasa ta kallon Amna dake dariya tace “Taya kike tunanin zai tasar min yer uwa, kuma ko ba komai ai ni da yaranshi duk muna cikin motar.”

Motarta ta nufa tana mik’a masa makullin tace “Bismillah.”

Hararanta yayi yace “Drebanki ne ni da zan tuk’a ki?”

Jefa mishi makullin tayi ta bud’a gidan baya ta d’auki yaran d’aya bayan d’aya duk ta zaunar dasu, har zata zauna ya jawo ribom d’inta daya fito waje ya shiga wajen yaran ya zauna yana fad’in “Ba inda zan tuk’aki kinji yarinya.”

Cikin jin haushi ta kalleta ta cire d’an kwalin ta mayar da ribom d’inta ta d’aura kallabin, zatayi magana Amna ta zagaya wajen mai tuk’i tana fad’in “Ya isa dan Allah, zauna nan ni saina tuk’a.”

Lek’owa yayi daga ciki yace “Ke duniyata fita a idona in rufe, ai da kinga kina tuk’i to ki tabbata tukunyar tuwo ce ko kuma kan gado kike kina wainani son ranki, amma ba dai mota ba.”

Sunkuyar da kai Amna tayi ta dawo gaba inda Hamna ta kalleshi tayi tsaki tace “Anji sanyi ba’a rufa ba Ammar, wai kai yaushe zaka girma ne?”

Ko kallonta baiyi ba yace “Ranar dana samu isasshen nono nasha.”

Wani kallo ta masa mai nuni da cewa ashe ni ce banda hankali, saida ta shiga ta zauna tana mak’ala mad’aurinta tace “Yace baya so ki tuk’a mota mana saboda yana takaicin ya siya miki.”

Saida ya d’auki Ameera ya d’ora kan k’afarshi yace “To banda kud’i, yan gidan nan naku kuma kowa taurin zuciyar tsiya ne dashi, k’aramin abu baya sa zuciyarsu ta kusa tsayawa bare na samu kud’i ta hanyarsu, dubi kakar nan taku kwanan baya mun d’auka zata shek’a ne amma ta tashi da ranta kuma.”

Dariya suka bushe da ita Hamna har da rik’e ciki, tayar da motar sukayi taja suka fita, tun kafin ta hau titi yace “Ke kin tabbata dai kin iya tuk’i ko? Karki zo ki jawo min mutuwa, burina nan gaba duniyata ta haifa min yara goma sha d’aya.”

Kallon Amna tayi tace “Ki ce mijinki ya min shiru akwai abubuwa da nake so su zauna min a kai, dan in ya ci gaba da surutun nan na tabbata saina manta har sunana ma.”

“Haka kawai malama saina rufe baki na, babu wanda ya isa ehe.”

Tafiya suke sosai cikin farin ciki dan dariya kawai yake basu suna karb’a, duk yanda Hamna take son ta dake ta fita shirginshi abun ya gagara, idan yayi wata katob’arar dole take darawa, yanzun ma yara duk sunyi bacci, kallon Hamna yayi ta madubi yace “Kankana wai ina budurwata ne?”

Saida ta nuna alamar b’acin rai tace “Wallahi Ammar karka sake kirana kankana, na fad’a maka bana so ko.”

Amna kuma tana juyowa tace “Wacece kuma budurwarka?”

Kallonta Hamna tayi tace “Amie, ita yake so ita kuma bata da lokacin shi, ya addabeta nima kuma ya addabeni, na fad’a masa idan ya k’ara min maganar ta zan fad’a miki dan ba zai yiwu na ci amanarki ba.”

Dariya yayi ya kalli Amna yace “Ya kike kallona? Ki fad’a mata mijinki mai lafiya ne ire irenku goma ma zan iya ji daku.”

Juyowa Hamna tayi baki bud’e tace “Bala’i, ire irenmu ko ire iren matarka?”

Saida ya kalli tsakiyar idonta yace “Ku nace, dukanku dake da ita da takwas kamar ku.”

Sun d’auki awa d’aya a k’alla kafin suka isa dan ba gudu take ba, kamar yanda suka yi tunani kam hakane ya faru, Hadiza da Chua’ibu sunyi farin ciki sosai na ganinsu tare, sunyi walwala sunyi hira da mahaifiyarsu sosai, inda daga k’arshe Hadiza ke tambayar Hamna ya labarin aure, kamar dai yanda ta saba yanzun ma cewa tayi kawai tayi ta mata addu’a, har yanzu bata samu wanda ya dace bane, amma data samu zasu ji labarin aurenta ita ma, Amna ce ta kalli mahaifiyarsu tace “Mama wallahi tana da samari masu nutsuwa da hankali, kawai bata shirya aure bane, amma kar kiga manyan mutanen dake zuwa wajenta gida.”

Cikin jin haushi tace “K’arya nayi kenan? Ina ruwanki da maganarmu? Karki koma saka min baki.”

Kallon mahaifiyarsu tayi zatayi magana Hadiza tace “Dakata Hamna, inhar kinsan gaskiya ne abinda ta fad’a to kiyi gaggawar tsayar da mijin aure, Hamna ba zan ji dad’i ba yau idan kika lalata mana sunan zuri’a, duk da ba a hannuna kuka tashi ba amma Hajia zata d’ora min laifin gurb’atarki, dan haka ina rok’onki dan Allah ki fitar da miji kiyi aurenki ki huta tun kafin girma ya k’ara kamaki, mace ce ke d’an lokacinki k’alilan ne, sannan idon mutane dayawa zai iya komawa kanki duba da aikinki da kuma abinda kike hawa yanzu, ki taimaka kinji ki rufa mana asiri da ma kanki.”

Saida tayi k’ok’arin had’e kukanta tace “Naji Mama.”

Hararan Amna tayi da take ganin ita ta had’ata da Maman, dariya ta mata ta mik’e ta fita daga d’akin, cikin nutsuwa Hadiza ta sake kallonta tace “Hamna, ki tabbatar min da wani abu d’aya mana.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected