BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*Bayan shekara hud’u* sai gashi Raihan Fadila da Ma’awa sun fara jarabawa ta zangon k’arshe a ajinsu, lokacin fa masha Allah yan mata an girma sosai kowace hallitarta ta fara bayyana ta zama budurwa yar shekara sha-biyar, musamman Raihan wacce tayi k’aramin jiki kamar na Sameera sai tsayi wanda ya dace da ita, ga farar fatarta ta gama bayyana kyau da shek’i, haka ma dogon gashinta wanda yafi ma na uwarta, domin kuwa ita tun tana yarinya ana gyara mata shi sab’anin Sameera data girma a k’auye, sam bata da wadatar k’irji dan kusan Raudat dake k’anwarta ta biyu ma kuma ko balaga batayi ba har nonuwanta sun kusa na Raihan d’in, lik’e suke a k’irjin ta sosai ba su da wani girma na azo a gani, dama idan Allah ya hanaka wani abun saiya baka wani abun, kamar yanda take da shafaffen ciki mai fad’i haka k’ugun ta yake a bud’e, kuma masha Allah tana da mazaunai daidai gwargwado, k’irarta abar birgewa ce da d’aukar hankalin maza, kamar yanda mahaifiyarta take haka ita ma take, gashi dama Sameera har yanzu ba wata k’iba bace tayi shiyasa ma idan kaga fuskokinsu sai kace wata yaya da k’anwa ne, yanzu haka sun kammala jarabawar sakamako kawai suke jira sai islamiyya da suke zuwa, ba jimawa kuma Abdul shima ya dawo daga madina hutu dan *doctor* yake sha’awar zama na musulunci, a yanzu ne kuma Abbas ya fara tunanin yi mishi gwajin jinin, amma rasa hanyar da zaibi yasa ya shirya shawartar su Bashir da Naseer.
*K’auyen Gwagwa*
*Harira* ce ta fito cikin shirin tafiya birni ita da yayanta, *Baaba mai wake* (k’anwar mahaifiyarsu) ce ta k’are musu kallo kafin ta tab’e baki tace “Tafiyar ce zakuyi?”
Harira ce ta amsa da “Eh Baaba, zamu tafi sai mun dawo.”
Sake tab’e baki tayi tace “Humm.” Juyawa sukayi sai yayanta daya fito da naira d’ari a aljihu ya bata yace “Baaba ga wannan, idan su *Karime* sun taso daga islamiyya saiki basu wake dashi.”
Nan ma dai sake tab’e bakin tayi tace “Yanzu d’ari ce zata isa su ci abinci su k’oshi? Kasan su da shegen cin tsiya fa.”
Cikin taushin murya yace “Kiyi hak’uri Baaba, kud’in mota kad’ai suka rage mana anan, suma wallahi aro su nayi wajen *Halidu* mai tebur, ko na abinci ba zamu samu ba.”
Cikin jin haushi tace “Naji dan Allah, ca-ca-ca-ca kamar carbi ta tsinke, kuje sai kun dawo.”
Mik’ewa tayi ta nufi wajen bisashen da take kiyo tana fad’in “Ba gaira ba dalili na d’auko wa kaina jaraba, shegen jaraabben son kud’in iyayenku ne ya ja muku ai, yanzu gashi a banza a wofi suna d’aure a magark’ama suna neman k’are rayuwarsu can, jaraba kawai.”
Duk abinda ta fad’a akan kunnuwansu, dan haka suka juya jiki a sanyaye suka fita daga gidan, cikin nutsuwa suke tafiya inda *Adamu* yace “Harira kina ganin idan muka je zasu sauraremu har su taimaka mana kuwa? Dan ni har yanzu a tsorace nake.”
Saida Harira ta share hawayen dake zubowa a idonta tace”Ban sani yah Adamu, iyayenmu sun cutar dasu sosai ta yanda ko basu yafe musu ba basu da laifi, matar yallab’ai Abbas kuma Sameera bana tunanin zata iya kallon fuskata ma, domin kuwa a lokacin da muke aiki a gidan na lak’a mata sharrin sata, kaga kuwa banda tabbacin zasu sauraremu.”
Rik’e k’ugu Adamu yayi suna tafiya a hankali yace “Wannan fanti da iyayenmu sukayi mana Allah kad’ai zai iya wanke mana shi, nifa yanzu duk da ina namiji har kunyar fita waje nake, har bana iya fad’in cewa ni d’an *Bukar* ne saboda abinda suka aikata.”
Da ire-iren wannan maganganun suka k’arasa tashar shiga mota, cikin sa’a suka sauka lafiya suka samu adaidaita suka lula unguwar zone 2, fadar Sameera aka ajesu inda mai gadi ya tambaye su “Wa ku ke nema?”
Harira ce tace “Munzo ganin Sameera ne.”
“Me? Hajia kike kira haka gatsau?” Cewar mai gadin, Adamu ne yace “Kayi hak’uri yallab’ai, munzo ganin Hajia Sameera ne.”
K’asa da sama ya kallesu yace ” Tasan da zuwanku ne?”
Adamu ne yace “Gaskiya bata sani ba, amma ka taimaka mana mu ganta dan Allah, wallahi daga nesa muke.”
Saida ya sake kallonsu kafin yace “Ku bari na sanar mata tukun.” Yana fad’a ya juya ya fito da wayarshi ya danna kira, a tabkekiyar kitchin d’in *Razeena* mai aiki ta ji kyakyawar wayar mai kama da masarrafin telebijin tayi k’ara, d’auka tayi tare da fad’in “Razeena ce akan layi.”
Mai gadin ne ya fad’a mata zuwansu Harirar tare da wanda suke son ganin, a cewarta “Zan fad’a ma Hajia yanzu.”
Aje wayar tayi kafin ta nufo falon Sameera, zaune ta sameta da *Ameer* (Mus’ab sunan mahaifinta) d’an shekara hud’u yana wasa saboda yau yan rigimar ne akanshi shiyasa ban je islamiyyar ba, sunkuyawa tayi tace “Hajia kinyi bak’i a waje, sunce ke suke son gani, su biyu ne mace da namiji, macen sunanta Harira sai namijin Adamu, sunce sun zo ne daga k’auyen gwagwa.”
Cike da jin dad’in yanda Razeena ta gama fahimtar halayyarta ta kalleta da mamaki, ta jima tana kallon fuskarta kamar tana son gano wani abu kafin ta zaro ido tace “Harira, k’auyen gwagwa?”
Cikin ladabi tace “Eh madame.”
Tsaye ta mik’e ta kama hannun Ameer tace “Ki musu iso Razeena, na gane wace Harira.”
“Ok.” Ta fad’a tana nufa k’ofar fita, ita ta bud’e musu k’aramar k’ofar suka shigo ta shigo da su, tana gaba suna biyarta suna k’arewa gidan kallo, Harira na tsananin mamaki wai Sameera ce a wannan gidan, wacce a lokacin da sukayi aiki ake mata kallo tsintacciya marar gata, saida ta shigo da su har falon anan Sameera dake tsaye har yanzu ta kalli Ameer tace ” Ameer Kaje wajensu Ammie kuyi hira.”
Harari ta kalla tace “Ki kawo musu abun tab’awa.”
“To.” Ta fad’a ta fice da shi, kallon Harira tayi wacce ta kafeta da ido tana kallo, sosai ta saki fuskarta d’auke da murmushi tace “Harira ku k’araso mana, ku shigo ku zauna.”
Saida taje ta kama hannunta ta zaunar da ita akan kujera inda shima Adamu ya zauna kamar akan wuta, kallon falon yake sai kace falon shugaban k’asa, a ranshi yace “Wasu na fafutukar neman abinda zasu ci, wasu kuma sun wadatu sunyi birgima a cikin kud’i, burinsu shine su tara dukiyar da har jikokinsu zasu mallaka.”
Muryar Sameera ce ta dawo dashi tana fad’in “Sannu ko, ya hanya?”
Da “Lafiya lau.” Suka amsa ta d’ora da “Harira dama kina nan? Ina kika shige haka ko labarinki babu?”
Cikin sanyinjiki tace “Ina nan mana Hajia, ina k’auyen mu.”
Zaune Sameera tayi a kujerar data tashi tana fad’in “Amma shine kika b’uya kuma?”
Murmushi kawai Harira tayi saboda fitowar wata mai aikin d’auke da faranti da kayan tab’awa da masu sanyi ta aje gabansu, saida ta zuba musu ta bawa kowa kafin ta juya zata tafi Sameera tace “Ku shirya mana wajen cin abinci saboda bak’i.”
Saida ta sunkuya tace “To Hajia.” Ta fice, kallonsu Sameera tayi tace “Harira wannan mijinki ne?”
Kallon Adamu tayi tace “A’a, yayana ne, uwar mu d’aya ubanmu d’aya.”
“Ayyah, Allah sarki, sannu ko.” Ta sake fad’a tana kallonshi, da d’an murmushi ya amsa da “Barka Hajia, ya yara?”
“Lafiya k’alau.” Ta fad’a da murmushi sosai, maida kallonta tayi ga *Wassila* dake shirya kayan abinci a dinning duk da ba lokacin cin abinci bane, mik’ewa tayi ta kallesu tace “Bismillah Harira, ku zo ku ci abinci.”
Daga ita har Adamu babu wanda yace a’a saboda dama basuyi karin kumallo ba suka fito, k’arasawa sukayi suka zauna akan kujerun suna jinsu kamar akan wuta, suna kallo Wassila ta gama shirya komai ta zubawa kowa ta aje masa gabanshi kafin tace “Aci lafiya.”