BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallonshi tayi cikin wani kukan tace “Kana cewa ba zai barni ba kuma gashi kace sai mutuwa ce zata raba mu, to idan fa lokacinta ne yayi?”
Saida ya k’ara matse hannunta sosai yana kallon k’wayar idonta yace “Hajia, ke da Alhaji kun ci nasarar rayuwa, kun zo duniya kun rayu tare da iyayenku, kun girma kuka rayu da ‘ya’yanku cikin gata da kulawa, sannan yanzu kuna tare da jikoki da yaran jikokinku, kun ci ribar rayuwa sosai, ku godewa Allah daya baku arzik’i na gidan duniya, wasu sun rayu da kud’i babu ‘ya’ya, wasu sun rayu da yara babu kud’i sanadiyar talauci yasa yaran fad’awa mummunan rayuwa, wasu kuma ya basu komai kamar ku, Hajiata, a familynki babu irin mai matsayin da babu, colonel na soja, kina da lieutenant na douanes, kina da babban k’usa a cikin siyasa, kina da babban professeur da da likita, kina da ma’aikacin ga wanda yake karantar shari’a, ga k’anwarmu dake son zama yar sanda, ga mai kwalliya ga yar kassuwa ga wacce ke son fitowa a alk’ali, sannan ga k’aramin k’ananmu wanda tun yanzu ya zama ustaz kuma yake burin zama babban malami da dai sauransu Hajia, kuma duk k’ok’arinku ne ya janyo hakan, ni kam Hajia me zaisa kuyi bak’in ciki ne a sanda zaku bar duniyar nan wacce ko ba dad’e ko ba jima dai sai an barta.”
Kallon idonshi tayi sai kayi ta saki murmushi, ita ma rik’e hannunshi tayi sosai tace “In fad’a maka gaskiya Ammar?”
Kai ya d’aga mata alamar eh, cikin rad’a tace “A gaskiya da bana son mutuwa ko kad’an, amma yanzu daka tunasar dani yawan zuri’ata da kuma matakai na rayuwa da suka taka a rayuwarsu sai naji ko yanzu na mutu banda damuwa, saboda nasan ko ba dukanku ba dole zan samu tsirarun da zasu bini da addu’a ta alkairi.”
Murmushi yayi sosai tare da sakin hannayenta yace “Bari na duba jikin Alhajin.”
Jinjina kai tayi ya shiga ciki, Alhamdulillah kam jikin a lokacin yayi dama, sai dai dukansu babu mai tunanin su bar wurin nan da Alhaji, dan kuwa su manya ne sun san komai shi kuma Ammar likita ne yasan yanayin, yanda suka ga Alhaji yayi yasa duk suka sare da al’amarin, tubarkallah wani kyau ne aka zubo mishi yayi jawur dashi, ga kumburi da k’afafunsa sukayi, haka dai daya farka suka sha hira shi da Ammar har da dariya sukeyi, da dare iyayen sun fita sai Ammar da Hajia zaune, da hannunshi ya bashi abinci yana idawa ya aje plate d’in, har zai kwantar dashi sai kuma yace “Alhaji zauna ka ci gaba da kallon Hajiarka, na yau dai kawai na danne kishina.”
Dukansu murmushi sukayi sai Alhaji daya kamo hannunshi yana sauke numfashi, saida ya saisaita nutsuwarsa da numfashinshi kafin yace “Ammar, dan Allah ku kula da kanku sannan ku rik’e zumunci, kai ne babba a yaran nan ka zama mai tsayawa kan lamuransu, Ammar ka rage zuciya da saurin hushi, sannan ka ci gaba da biyayya wa iyayenka, sannan ka…”
Sai kuma yayi shiru, dukansu ido suka sakar masa hakan yasa yayi dariya ya kalli Hajia yace “Ka kula min da Hajia Zeeya’atu na, kakar nan taka babu wanda ya iyata sama dani, ni ne mijinta anan kuma ni zan zama mijinta a lahira ma, ta dace dani, nima kuma na dace da kayata.”
Cike da tabbatarwa yace “Insha Allah zanyi Alhaji.”
Yanda ya k’arashe yana dariya yasa Hajia fashewa da kuka, d’ora kanta tayi kan k’afafunshi dake mik’e, dafa kanta yayi yace “Bana son ganin kukanki Zeeya’atu, ki daina kinji karki sani kuka nima.”
Ba tare data d’ago ba cikin kuka tace “Tun bayan rasuwar iyayena a bakinka kad’ai nake jin sunan Zeeya’atu, Alhaji bana so na daina jin sautin nan, ka ci gaba da kirana haka dan Allah, hakan zaisa naji a raina akwai mutum d’aya daya isa dani kuma yake da iko a kaina.”
Kallon Ammar yayi sukayi murmushi, k’ara shafa kanta yayi yana fad’in “Zeeya’atu na, Zeeya’atu na ki daina kuka kinji, bana son ganin hawayenki Zeeya’atu.”
D’agowa tayi ta kalli tace “Zan iya yanzu Ammar?”
Fahimtar inda maganarta ta dosa yasa shi d’aga mata kai yace “Yanzu ne lokacin daya dace Hajia.”
Jinjina masa kai tayi sannan ta kalli Alhaji, a hankali ta mik’e daga kan kujerar ta tureta baya, *me zai faru? Wace rana ce yau? Wane babban tarihi ne haka?* Hajia Zeeya’atu da kanta ce k’asa akan gwiyoyinta biyu a gaban Alhaji Suley, ko kuma nace muku Suley, hawaye a idonta cikin nadama da neman yafiya ta k’ara fashewa da kuka tace “Ka yafe min Alhaji na, ka yafe min dan Allah ba dan halina ba, in dan halina ne wallahi ko kallo ban isheka ba, na muzguna maka a rayuwa, na cutar da kai fiye da kima, na wulak’antaka na tozarta darajarka ta d’an adam, na ci zarafinka tare da yaga rigar mutumcinka, na yi wasar kura da rayuwarka, na…”
Hannunta ya rik’o da sauri yace “Zeeya’atu, ya isa haka kinji, na yafe miki duniya da lahira, Zeeya’atu ban tab’a rik’eki duk abinda kike min ba, da farko ina miki uziri da d’aga miki k’afa saboda hallacin mahaifinki gare ni, amma daga sanda na bud’a idona naga duk girman gidan nan a cike yake da mutane, kuma kaso biyu daga cikin uku duk ke ce tushen samuwarsu sai kawai naji na k’ara k’aunarki, sannan naji na yafe miki komai da kika min, dan haka karki damu kan wannan Zeeya.”
Kallonshi tayi sai yace “Tashi dan Allah kar yaran nan su shigo su ganki haka, sai kisa su d’aureni na gurfanar musu da uwa, kinsan fa babu muk’amin da babu a ‘ya’ya da jikokinki.”
Cikin turo baki na shagwab’a ta mik’e tana fad’in “Ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, kuma sun samu matsayin da suka samu ne saboda samun jajirtaccen uba kamar ka.”
Saida ta zauna ta kalli Ammar tace “Na fad’a maka dama shi d’in na musamman ne, hak’uri ne dashi kamar damo.”
Dariya sukayi sai Alhaji daya mata wani kallo yace “Ke kuma akwai hauka a kanki Zeeya.”
Dariya Ammar yayi yace “Hum! Ashe gado nayi, shiyasa har matata ke min kallon mahaukaci.”
Dariya Alhaji yayi sai Hajia data mishi dak’uwa, hannu Alhaji ya mik’awa Ammar ya rik’e gam yana murmushi yace “Ko mutuwa ta zo min yanzu babu sauran k’unci a tattare da zuciya ta, kana tare dani ka min alk’awarin kula da yan uwanka, sannan yau Hajia ta nemi affuwata, alamu ne na ta d’auki hanyar gyara halayenta marasa kyau, hakan ya sani farin ciki, zan tafi gidana na gaskuya ba tare da tunanin zata ci gaba da takura kowa ba, ta mulki yaran kuma tana so ta mulki jikoki, abu ne ba mai yiwu ba, shiyasa ina jiye mata ranar da zata fara kuka kan rashin cikar burin da wani baiyi ba, Alhamdulillah Allah.”
*Da asuba* mazan duk sun tafi masallaci sai Hajia a d’akin tayi sallah, a hankali ta d’ago kai ta kalleshi kwance ido rufe, ta d’anyi mamaki jin bai nemi ta taimakasa ya tashi yayi alwala ba, dan ko ranar da suka zo jikin ma babu dad’i saida aka tayar dadhi yayi sallah, ci gaba tayi da jan carbinta har zuwa wani lokacin, da sauri ta juya jin n’aurar nan ta canza k’ara daga yi d’aya bayan d’aya zuwa da sauri babu k’akk’auci, sam sai bata damu ba kawai ta ci gaba da abinda take, suna shigowa suka shiga kallon n’aurar suna kallon juna, Ammar daya kafe shi da ido ne ya d’an matsa kusan gadon, wani kallon tsoro ne yake masa har saida ya kamo wuyan hannunsa ya rik’e yana sauraran harbawar jijiyarshi, da sauri ya juyo ya kallesu ya musu alama da su fitar da Hajia waje, colonel ne ya d’an fita saiya lek’o yace “Hajia ana magana.”