BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Da kai kawai ya masa alamar toh kafin ya wuce ya zagaya ta baya, saida ya tabbatar babu mai ganinshi kafin ya sulale ya nufi b’angaren uwar d’aki, cikin sauk’i ya had’u da wata baiwar ta fito daga falonta da wani abu mai kama da k’warya da kayan marmari a ciki, nan ya fad’a mata yana son ganin uwar d’aki, bata b’ata mishi lokaci ba ta juya ta koma ciki ta fad’awa uwar d’akin sak’on dake tafe da ita, tana kishingid’e jakadiyarta na gefe tana matsala mata k’afafu sai lumshe ido take tace “Ki shigo da shi.”
Mik’ewa tayi cikin ladabi ta nufi k’ofa, a hankali ta bud’a ido ta kalli jakadiyar tace “Ki jira mu a waje, karki bari kowa ya shigo har sai *Kullu* ya fita.”
Cikin girmamawa da kirari ta mik’e ta fita ta zauna falo shi kuma ya shigo, har saida ya samu wuri ya durk’usa ya gaisheta tare da mata kirarin matar sarki uwar sarki kuma kakar sarki insha Allahu kafin cike da isa da k’asaita tace “Kullu meke tafe da kai a daren nan? Baka san mutanen gidan nan zasu iya saka mana ido ba?”
K’ara sunkuyawa yayi yace “Tuba nake ranki shi dad’e, akwai abinda ke shirin faruwa ne a gidan nan da na ga ya kamata ace kinyi gaggawar saninshi.”
A hankali tace “Me yake faruwa?”
“Ranki shi dad’e yanzu haka daga wajen takawa muke tare da mai martaba, sun tattauna sosai, kuma ba akan komai ba sai akan maganar auren mai martaba, takawa yace zaiyi magana da liman kan ya bawa mai martaba auren ‘yarsa Safiyya, ya kuma ce ba za’a d’auki lokaci ba.”
Da sauri ta tashi zaune ta fito da idonta wanda ada take k’ank’ancesu tace “Kuma mai martabar ya amince?”
Sake sunkuyawa yayi yace “Ranki shi dad’e sanin kanki ne da wuya takawa ya umarci mai martaba abu kuma ya tsallake baiyi shi ba, sai dai in takawa ne ya janye umarninshi.”
A harzuk’e tace “Idan kuma bai janye ba fa?”
Cikin ladabi yace ” Aure zai tabbata ba fashi, tuba nake ranki shi dad’e, Allah ya ja zamaninki, kinyi taki kinyi ta rago.”
Da k’arfi ta katseshi da fad’in “Ya isa, je ka kawai, ka ci gaba da saka min ido akan duk wani motsin mai martaba, kafin nan zanji da wannan al’amarin.”
Saida ya mata kirari ya fita daga d’akin ya sake zagayawa ya koma wajen aikinshi, yana fita ta d’auki wayarta ta mik’e tsaye tana dannawa waziri kira, har saida kiran ya tsinke ta sake kira na biyu kafin ya d’auka, cikin hargagi tace “Duk abinda kake gobe ka zo ka same ni zamuyi magana.”
Cikin girmamawa yace “Uwar d’aki lafiya? Meya faru ne?”
“Akwai babbar matsala nake fad’a maka, kawai ka zo ka same ni gobe da safe, kuma bana so ka bari wani ya ga lokacin da zaka shigo nan.”
“Angama ranki shi dad’e, Allah ya kaimu gobe da safen.”
Datse kiran kawai tayi ba tace komai ba, jakadiya da ita ma ko da Kullu ya shigo ta biyo bayanshi ta lab’e tana saurarensu, tsaf ita ma ta kwashe komai da suka fad’a ta shirya fad’awa d’aya daga cikin kishiyoyin uwar d’aki mai sunan *Hannatu*.
Ta k’ofar da babu mai shigowa sai ita kad’ai tasa makulli ta shigo cikin shigar alfarma ta alkyabba, babu kowa falo kai tsaye tukarar ta wuce ta k’wank’wasa k’ofar, sarki Imran da a lokacin yake kwance kan makeken gadonshi na alfarma yana kallon sama, tunani yake akan abinda ke tunkaro shi, yanda zai fara fad’awa sarauniya Ameera yake tunani, k’wank’wasa k’ofar ne yasa ya kalli k’ofar har saida gabanshi ya d’an fad’i, dan yasan ita ce ta zo, umarnin shiga ya bata ta bud’a ta shigo, zaune ya tashi za zuro k’afarshi daya k’asa ya tankwashe d’aya akan gadon yana kallonta harta k’araso kusa da shi, cikin murmushi da girmamawa tace “Barka da warhaka gwarzona, sarkin Basraba sarkin sarakuna, buhun k’aya kake ba’a cikaka a tausa, kwalli mai sa ido shek’i, d’awisu ne kai ko a dawa namanka sai sarki, na Ameera bada kanka a sare kaje gida ka ce ya fad’i, rugum babban motsi, daji ba’a maka k’aure ko da mahaukacin kafinta, d’an sarki, jikan sarki, kuma uba ga sarkin Basraba da yardar Allah, kaga Abban *Ja’afar* da *Safna*, gaba ka bawa mak’iyanka ba baya ba, da baya ka basu da tuni sun cimma ka, na…”
Fizgota yayi ta fad’o kanshi suka fad’a saman gadon suna dariya yana fad’in “Kin gama fasa min kai na yau, ki adana sauran har gobe sarauniyata.”
Kwance sukayi ya kalli fuskarta yace “Wai ina kike koyon irin wannan sai kace sarauniyar marok’a ta duniya.”
Murmushi tayi tace “Tun ranar dana auri sarki na shiga makarantar koyon wasa mutum, dan ina so na dinga kod’a mijina.”
Cikin jin dad’i yace “In kuwa hakane to ya kamata a k’arawa malamin nan albashi, ke kuma miki albishir dana baki kyautar alkyabbata wacce nafi ji da ita.”
Dafe k’irji tayi cike da murna tace “Wow my King, godiya nake masoyina, Allah yaja zamaninka, Allah ya k’ara maka nisan kwana da lafiya.” Da haka suka gudanar da darensu cikin soyayya da k’aunar juna.
*Abuja*
Rana ta hantse sosai Harira ta zo da yan kayanta, nan Sameera ta gabatar da ita wajen sauran ma’aikatan gidan da kuma Ammie, d’akunan yaran ta nuna mata inda zata dinga kula da shi, fitowa tayi ta barota a d’akin Khalifa da Diya’u tace zata gyara musu duk da Sameera tace ta bari harta huta, tana fita ta juya ta kalli d’akin da kyau, tab’e baki tayi tace “Humm! Sameera kenan, wato yanzu nan ke duk zaman da mukayi tare dake amma ki rasa sakayyar da zaki min sai had’a ni da aikin kula da d’akin yaranki? Ba damuwa, da sannu nima sai nayi iya k’ok’ari na wajen ganin na shigo gidan nan a matsayin kishiyarki, wallahi daga lokacin zata k’are miki.”
*Da abinda kika shigo kenan? To takwara aiki ya samemu ashe, su Harira nasan sai dai in wajensu lamma za’a fara durk’usawa.*
Sameera wajen Ammie ta koma ta nemi alfarmar tayi shiru da bakinta kar Abbanta ya sani, dan inhar yasan wacece Harira to akwai matsala, alk’awari Ammie ta mata na ba zai ji ba.
*BASRABA*
Da sassafe Waziri ya shigo b’angaren uwar d’aki bayan ya tabbatar babu wanda ya ga shigarshi, waya na ga ta ya fiddo a aljihu ya danna camera ya saita wayar a jikin k’ofa ya tangaleta a bayan murfin k’ofar, saida ya kalla ya ga tana hasko mishi inda yake da tabbacin nan uwar d’aki zata zauna sannan yayi murmushi ya shigo, jakadiya na mishi iso ta bar part d’in zuwa na Hannatu dan kai mata tsegumi, a falon uwar d’aki ya zauna yana kallonta fuska a had’e, cikin ladabi yace ” Hushi bai dace da uwar sarki ba, uwar d’aki ko zan iya sanin meke faruwa?”
Kallonshi tayi tace “Waziri da matsala babba, takawa yana so ya kaini bango har yasa nayi abinda banyi niyya ba.”
Yana d’an kallonta yace “Ranki shi dad’e lafiya? Me takawa yayi kuma yanzun?”
Cikin hushi tace “Na samu labarin takawa yana son had’a sarki aure da yar gidan liman, ni kuma ba zan lamunta ba dan ita ma yarinyar bana k’aunar ta kamar yanda bana k’aunar matarshi Ameera, shiyasa na ce ka zo dan musan abinyi tun wuri kafin lokaci ya k’ure mana.”
Fuskarshi a had’e shima ya kalleta yace “Yar liman kuma? Amma meyasa takawa zaiyi mana haka?”
Shiru tayi sai kumbura da take hakan yasa yace “To shi mai martabar me yace akan lamarin?”
A d’an fad’a ta kalleshi tace “Me kuwa zai ce? Ai kafi kowa sanin sarki Imran baya tab’a kaucewa umarnin mahaifinshi, ya amince d’ari bisa d’ari zai aureta, kuma ina tabbatar maka inhar liman da takawa suka had’u yau har suka tattauna, to babu shakka auren sarki da yar liman zai zauna daram, dan ba zasu tab’a jan al’amarin da tsayi ba.”