BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Sosai ta sake rik’e ta tace “To me zamuyi? Idan kin shiga zaki rama mata ne? Ko kuma zaki masa magana ne yaji? Kawai ki barshi idan ya gaji da dukanta ai zai dakata.”
Cikin b’acin rai da tafasar zuciya ta zauna k’asa dab’as ta fashe da kuka ita ma, kuma har lokacin Hassan bai daina dukanta ba har ta kai tayi shiru, suna haka cirko cirko suka ga ya fito daga d’akin yana ta bambami, Husseina kam da harara ta bishi ta mik’e suka shiga d’akin da gudu, zaune suka sameta rakub’e da bango sai shashek’a da take yi, kamar yanda suka saba Hassana ce ta rulgumota tana jijjigata tana fad’in “Kiyi hak’uri Iyya, kiyi hak’uri dan Allah komai zai zama tarihi wata rana.”
Suna haka kuma Suley ya shigo da sallama d’akin jiki a matuk’ar sanyaye sai ledar dake hannunshi, Hassana kad’ai ta amsa mishi kafin ya zauna gefensu ya mik’awa Husseina ledar hannunshi, sai lokacin Hassana tace “Suley kana lafiya? Na ganka kamar baka lafiya?”
Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yace “Lafiya ta lau Hassana, na zo zan shigo ciki na ji hayaniya da sautin Iyya, shiyasa ban shigo ba tunda banga abinda zan iya yi ba.”
Husseina ce ta kalle shi tace “Wai har kaima dake namiji baka tab’a ji a zuciyarka ba kana so ka d’auki tsohon nan ka nunawa sama shi sannan ka sauke k’eyar shi k’asa? Gaskiya ni na fara gajiya.”
Kallonta yayi zaiyi magana Saratu ta mik’e saboda tuna abinda ya fad’a mata da zai fita cewa ta kai mi shi abincin shi yanzun nan, ganin ta fita ta bar musu d’akin yasa sukayi shiru kawai.
Sai bayan kwana biyu Delu ta shirya tare da su Hassana suka tafi wajen malamin nan, shima kuma aradu Saratu ta tara da kai domin ba barinsu ake suna fita ba, haka Delu ta tafi dasu wajen malam Rabi’u, sam a ranta babu mummunan nufi sai na son taimaka musu, amma sai gashi tunda malamin ya d’ora idonshi akan Husseina sai yawunshi ya tsinke, ta wani fannin ya fad’a musu gaskiya kam da yace asiri ne aka musu dan kar suyi aure, ta wani b’angare kuma b’atar da su yayi da yace akwai maganin da zai bayar suyi aiki da shi amma dole Husseina ce zata dawo gobe ta karb’a, ba musu suka juyo suka dawo gidan, yau ma Hassana da Husseina shegen duka suka sha wajen Babansu saboda fitar da sukayi, amma hakan bai hanata komawa ba washe gari da magriba kamar yanda sukayi da malam, wannan zuwan kuma shine ya wargaza duk wani tanadi da tattali data jima tanawa kanta, duk yanda ta so bijere masa bai bata dama ba saboda ya nuna mata k’arfi, kuma tun farko ya riga daya ci galaba a kanta, a wannan zuwan ne malam rabi’u ya rabata da mutumcinta ta hanyar yin kaca-kaca da shi.
Da k’yar ta kawo kanta gida tana kuka, amma kuma sai ta k’i yarda Saratu tasan abinda ya faru sai yar uwarta kad’ai abokiyar shawararta ta fad’a ma, Hassana ma ta shiga damuwa har ta kusa ta fita tashin hankali, amma haka suka dinga b’oyewa har lokaci ya dinga gangarawa, cikin hukuncin ubangiji kuma sai Allah ya fito musu da maza, d’aya d’an abokin Babansu ne yace yana son Hassana, sai wani mai mata biyu dake nan unguwarsu yace a bashi auren Husseina, dama mahaifinsu ya gaji dasu kamar yanda yake fad’a, dan haka ba’a d’auki lokaci ba aka d’aura musu aure kowace ta shiga d’akin aurenta.
_K’alubalen har yanzu bai fara ba, yayin da *BADAK’ALAR* yanzu ne zata soma._
*See u guy’s*
05/06/2020 à 20:36 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_12_
Zaha ta d’an shawarci mai gidan nata cewa ya za ayi aure haka kawai basu san waye shi ba, sannan ka d’auki ‘ya ka bashi a sadaka, sanin dama sai anyi wannan cecekucen yasa yace shi zai yi wa ‘yarshi duk wani abu da akewa kowace yar gata, haka lokacin ya ya fara tafiya dama kuma ba wani lokaci bane mai tsayi, har lokacin Zeeya da suley basu had’u ba dan k’iyayyarshi ce zalla a zuciyarta, shi kuma bai ma san ainihin me yake ji a game da ita ba, ana haka juma’a ta zo kuma aka d’aura aure, inda Alghabit ya wa suley wakilci liman kuma ya wa Zeeya, sadaki mafi girma da daraja ya biya wanda sai wane da wane, duk wata al’ada saida akayi ba’a bar komai ba, kafin nan amarya ta tare ita da halinta.
Zaman *doya* da *manja* suka fara, Zeeya dai banda gori da rashin kunya babu abinda take wa Suley, kullum ita ce fad’in bashi da kowa bashi da komai, da dukiyar ubanta yake duk wani abu na rayuwa, tunda sukayi aure basu kwana d’aki d’aya ba, dan lokacin shigowarshi nayi zata rufe na ta d’akin, abunci kam dama iya bakinta take dafawa, Suley yasha wahalar Zeeya fiye da tunanin mai karatu.
Ni kaina da ana bani labari na yaba da hak’urin shi, dan kad’an daga iskancin Zeeya yana iya d’iban ruwan wanka ta zubar da gangan ko kuma ta zuba wasu ruwan masu datti a ciki, ko kuma ta d’ibi k’asa ta zuba, ya kan shiga wanka ya rataya kayanshi a katanga da gangan ta d’auke kayan ta musu shark’af da ruwa, ankai matakin da saida Zeeya ta d’auki kayan Suley masu kyau wanda yake fita da shi tasa sabuwar wuk’a ta yagasu, Zeeya na iya ganin Suley zaune yana alwala ta d’auki sharar iskanci ta dinga bad’a mishi k’ura a jiki, wallahi wallahi yanda mai bani labarin ta fad’a min tace duk wannan iskancin idan tayi sai dai ya kalleta ya girgiza kai yace “Allah ya kyauta, ya ganar da ke gaskiya.”
*Bayan wata d’aya* ya shirya tafiya gida dan ganin me ake ciki tunda yanzu Allah ya hore mishi kud’in mota harda ma na guzuri da tsaraba, haka ya sa kai ya tafi Zeeya bata damu ba dan dama nesa take so suyi da juna, bayan yaje ne ya samu labarin rasuwar mahaifiyarshi da ita kad’ai ta rage mi shi, hakan yasa shi dasa nashi kukan harya gode Allah, abin duniya ne ya taru ya mishi yawa, ga rashin uwa ga rashin sanin inda Husseina take, dan har yanzu babu wanda yace ya ganta da idon shi, haka Hassana ta bashi labarin rabon gadon da akayi tare da nuna masa yan dabbobin da aka basu, hakan ya b’ata mi shi rai sosai ta yanda har ya fara ikrarin cewa sai an sake wannan rabon gadon, dan son zuciya yayi yawa cikin wanda akayi, kuka sosai Hassana ta dinga yi tace yayi hak’uri kawai ya share ya barwa Allah, tunda gashi a cikin watannin da basu kai shekara ba har sun had’a garke, haka ya hak’ura badan ya so ba ita kuma tasan ko yanzu sai wani abun ya faru idan yayi maganar, haka ya shirya sake komawa wajen iyalinshi cike da burin son zama a mahaifarshi, sai dai abu d’aya ba zai yiwu lokaci d’aya haka yace zai dawo da Zeeya garin nan ba a yanda take, dan haka ya shirya ya shirya ya tafi ya kuma ce Hassana ta ci gaba da saka ido wajen neman yer uwarsu, idan an samu labari to taje kasuwa ta samu fatake dake yawon fatauci har zuwa Agadez ta bayar da sak’o za’a sanar da shi, sannan ta ci gaba da kula da duka gadon na su, haka ya koma ya samu Zeeya suka d’ora daga inda aka tsaya.