BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallonshi tayi a sagale, na iya girki? Me yake nufi? Kafin ta bashi amsa ya nufi wajen abincin yana fad’in “Na ga dai waccen kakar taku tafi damuwa da al’amarin tsaronku ta yanda bata barinku fita, amma kulawa daku kuma wannan bata ma san me takeyi ba.”

Bin bayanshi tayi ya zauna kan kujera ita kuma ta fara zuba mishi farar shinkafar da tayi warwara gwanin kyau, sai kabeji data zagayeta da su sannan ta kuma zagayeta da karas wanda duk ta gurzasu, sai dunk’ulallen naman data jera shima kafin ta zuba sauce d’in albassar a tsakiya, tab’e baki yayi ya janyo farantin ya d’auki cokali ya kai lomar farko, kallonta yayi ya mata alama da hannu cewa komai yayi, murmushi tayi ta ja kujera ta zauna cikin d’ard’ar tace “Ai ba ido kawai Hajia take saka mana ba, har yanda zamu kyautata rayuwarmu tasa an koya mana.”

Murmushin baki da hankali ya mata ba tare daya kalleta ba, saida yayi loma bakwai har ta manta da zaiyi magana sannan taji yace “Amna.”

“Um.” Ta fad’a tana mayar da hankalinta kanshi, saida ya kalleta yayi kalar tausayi sosai yace “Dan Allah ki dinga girka min abinci kullum ina ci, ina yawon zama da yunwa, ki min wannan alfarmar kinji?”

“To amma yah Ammar me yasa baka san cin abinci?”

Kallonta yayi babu annuri a fuskarshi, har zai bata amsa sai kuma ya canza maganar yace “Bana da wanda zai rik’a bani a baki ne.”

Sunkuyar da kai tayi a zuciyarta tace “Uban wani kakan wani ka zauna sai an baka abinci a baki? Lallai ma mutumin nan.”

Kafin wata magana ta sake shiga tsakaninsu aka bud’a k’ofar d’akin aka shigo, dukansu kallon k’ofar sukayi a tare, da sakin fuska Amna tace “Autan Ummy ne?”

Bai ce komai ba kamar yanda bai saki fuskarsa daga had’ewar daya mata ba, saida ya zo inda suke yace “Zuba min nima zan ci.”

Murmushi tayi tana kallonsa ta fara k’ok’arin zuba masa tana fad’in “Autan Ummy kamar ranka a b’ace? Waya tab’aka ne?”

Kujera yaja zai zauna Ammar ya sauke mishi jajayen idonshi, kallo ne da zai iya saka fitsari a wando, kallo ne dake tattare da aika sak’onni dayawa, ba kayi sallama ba, baka gaishe da mutane ba, sannan kana wani d’aurawa mutane fuska, baka ga wurin zama ba sai a nan? Sannan me ma ya kawo ka? To bashi Amsa Kamal.

Kallon Amna yayi wacce ita ma ta kalleshi dan ta lura da kallon daya mishi, murmushi ta sake yi tace “Wai waya tab’a ka ne Kamal?”

Turo baki yayi yace “Tonton Gambo ne zai koma Niamey yanzu, shine na ce zan bishi Hajia tace a’a, wai sai dai su tafi da Hamna.”

Dukansu sake bashi hankalinsu sukayi inda Ammar ya d’ora da cewa “Saboda me?”

“Nima ban sani ba.” Ya fad’a yana zaunawa kan kujerar, kallonshi Amna tayi da mamaki tace “Me yasa Hajia zata tura Hamna can kuma?”

“Ba haka kawai tayi ba.” Yana fad’a ya mik’e da hanzari zai bar falon, da sauri Amna ta bi bayanshi tace “Yah Ammar zan iya zuwa na ga yer uwata? Wallahi nasan ba’a son ranta zata je ba, daga ni har ita babu mai son zuwa wajen Abba saboda tanti Aissata ba k’aunarmu take ba.”

Hannunta ya kamo kawai suka fita, ta k’ofar dake cikin gidan suka shiga, kai tsaye falo suka nufa ba tare daya saki hannunta ba, suna shiga Amna tayi sallama amma banda gogan, hankalinshi na kan mutanen dake cikin d’akin yana kallonsu d’aya bayan d’aya, a hankali ya saki hannunta ta gaishe da mutanen wurin, kowa ya amsa amma banda Hajia dake kallonta a hargitse, kallon mahaifinsu tayi dake zaune kan. kujera tace “Abba yanzu zaku tafi?”

“Yanzu zamu koma auta ta, amma tare da Hamna zan tafi.” Duk yayi maganar ne jiki a sanyaye, da d’an mamaki tace “Amma Abba me yasa zaka tafi da ita yanzu? Kai fa kake cewa kafi son zamanmu anan.”

“Yanzu kuma ya sauya, zai tafi da ita tunda anyi hutu, kuma ba aure ne da ita ba tunda ta k’i aure.”

A tare suka kalleta ita da Ammar, kallon ladabi da tsoro ta mata, yayin da shi kuma ya bita da kallon to sai akayi yaya kuma? Hajia kifa kiyaye ni, meye na wani d’auketa daga nan d’in? Jin bbu wanda yace wani abu yasa Amna ta tunkari d’akinsu na sama da sauri dan ta samu Hamna, tana shiga ta sameta zaune bakin gado da alama kuka take, k’arasawa tayi ta zauna kusanta ta dafata tace “Rabin jikina, kuka kike? Na sani dama ba zaki so tafiya ba, amma me yasa Hajia tace a tafi dake?”

D’an d’ago kanta tayi ta kalleta tace “Nima bansan dalilinta ba rabin jiki, kawai dan bata son gani na a gidan nan.”

Da sauri tace “A’a rabin jiki, karki fad’i haka mana, kinfi kowa sanin yanda Hajia bata san muyi nesa da ita, ina ga dai ko dan baki amince da auren yah Junaid bane.”

Tab’e baki tayi alamar ko oho, jin ba tace komai ba yasa Amna mik’ewa tsaye ta kamata tana fad’in”Taso, tashi muje ki bata hak’uri dan Allah, ba zan yarda ta rabani dake ba a lokacin da nafi buk’atarki a kusa da ni.”

Mik’ewa tayi cike da kasala tace “Amna ba zata hak’ura ba, kefa kin sani.”

Janta tayi da k’arfi suka nufi hanyar fita, a lokacin ne wani tunani ya zo ma Hamna, a take sai taji tana buk’atar yin nisa da gidan ma ko dan yer uwarta, dan har yanzu bata iya kallon k’wayar idonta idan ta tuna tasan mijinta kafin ita, duk da tursasata akayi amma abun kunya ne a wurinta. Sai dai kuma Ummy na buk’atar zamanta anan ko dan abinda ke cikinta, *ciki?* Shine abinda ta sake maimaitawa, hawaye taji sun taho mata a wannan lokacin, bata ankara ba sai ji tayi sua sauka kan matattakala suna sauka k’asa, yanayinta ne ya sake canzawa gaba d’aya, sanyin jijiyoyinta suka rub’anya ta yanda suke daf da tsinkewa, tun daga nesa take kallon mutanen dake k’asa, hawayen ne ke ci gaba da zubo mata saboda tasan a halin yanzu yer uwarta ba zata ji dad’in abinda zata mata ba, dan kuwa k’aryata ta ne zatayi a gaban mutane, tasan za taji zafi sosai sai dai zata fahimci dalilinta, sai dai kuma bata san yaushe ne ba?.

Tunda suka taho ya k’ura mata ido, kallon k’wak’waf ne yake mata na son gano yanayin da take ciki, sai dai garin kallon nan na jaraba ne ya fara hango wani abun, canji ne sosai wanda shi dai bai santa da shi ba, amma ganin baida hujjar da zai tabbatarwa kanshi yasa shi faa fafutukar neman hujjar, bai daina binta da wannan kallon mai firgita wanda ake ma ba suka k’araso, Amna na rik’e da hannunta suka tunkari wurin Hajia da niyyar mata magana, amma sai Ammar yasha gabansu kamar sojon da zai bincikesu, idon Hamna ya kalla sosai tare da mata wani tuhumammen kallo ya nuna idonta da yatsa kamar zai tsoneta yace “Sai kace wata mai ciki sai k’yak’yabta ido kike, ko tafiyarce ba kya so?”

Wandon dake jikin Ummy ne kawai ya mata shamaki da saurin b’allowar fitsari, sai dai ta tabbatar kayan cikinta zamansu ya sauya, dan juyawar da sukayi mota ce kawai za tayi wannan harurun da kai yayin da ta jirkice ta fantsama katantawwa da kai. Hamna kuma numfashinta ne taji ta nema ta rasa, hakan ne ya haddasa mata rufe ido sai k’wayar idonta dake juyawa, Amna kuma kallonshi tayi ba tare da tunanin komai ba tana murmushi, dan ita yanzu ta fara fahimtar mijin nata, sannan da yace yana sane yake komai yasa tayi damarar shanye duk wata katob’ara tashi, kowa madale wajen abinda yayi tunani kenan ba Hajia kad’ai ba, wato rashin kunyar ce ko? Kamar a mafarki sai gani sukayi yasa hannu ya tallaba kanta yana k’ok’arin bud’e mata ido, dan shi dai a matsayinshi na likita duk da ba abinda ya karanta ba kenan, amma da kallo da kuma ji zai iya gane larurar wani majinyacin, yana cikin kiciniyar nan Ummy dake kallonsa kamar mahaukaci ganin yana neman b’alle mata lik’i yasa ta tahowa da k’arfin tsiya, k’arfin da yafi k’arfin kuzarinta da d’ab’iarta, tana zuwa gabanshi ta d’aga hannu iya k’arfinta ta wanke fuskarshi da mari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected