BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Saida ya sauke b’oyayyar ajiyar zuciya yace “Ok Dady, a fito lafiya.”
Jinjina kai yayi ya fita daga motar ya shiga ciki Abdul na kallonshi harya b’ace mishi, bayan ya shiga ne yake fad’awa *Dr Kabir* sun zo tare da yaron da za mishi gwajin jini, kuma kamar yanda ya fad’a baya so yasan da an deb’i jininshi ne dan ayi wani abu da shi, saida ya sake tabbatar mishi da babu matsala, saida yayi kira a waya ba jimawa ya datse kiran kafin suka fito tare, Abdul na ganinsu ya fito daga mota cikin girmamawa ya gaishe da Dr Kabir, amsawa yayi cikin raha kafin Abbas ya kalli Dr Kabir yace “Muje na gani ko?”
Da girmamawa yace “Yes sir, zamu iya tafiya.”
Wani b’angare na musamman suka nufa inda Abbas yace Abdul ya zo su tafi, suna cikin tafiya wani mutum ya fito daga cikin gurin da zasu shiga, saidai mutumin a matuk’ar firgice yake wanda zaka ita gani k’arara, suna kusa da juna shi da Abdul sai kawai yayi saurin dafe hannunshi tare da sakin ‘yar k’ara, da sauri Abbas ya rik’e shi yana kallonshi yana fad’in “Son lafiya? Meya faru?”
Murmushin yak’e yayi yace “Nothing Dady, wani abu ne naji ya soke ni a hannu na.” Ya fad’a yana d’aga hannunshi tare da kallon wurin, da sauri dr Kabir ya matso yana fad’in “Oh my goodness, yana zubar da jini fa.”
Juyawa Abbas yayi ya kalli mutumin da yayi kamar baisan tsiyar da suke ba saboda tafiyarshi kawai yake, da nuna reaction d’in takaici yace “Kabir waye wannan? Ina kuka samu mahaukata irin haka?”
Cikin jimami dr Kabir yace “Sorry sir, maybe ko ya karb’i result d’in shi ne kuma sakamakon ciki ne ya d’aga mishi hankali, ko kuma dai wani ne babu lafiya ana neman jini ba’a samu a lab d’in mu ba.”
Kama hannun Abdul yayi suka shiga ciki da niyyar ya duba shi, suna shiga ya zaunar dashi akan kujera, wata yar roba ya d’auko mai haske wacce tsayinta ba zai wuce d’an yatsa manuniya ba ya tara jinin, Abdul na kallo baiyi tunanin komai ba, saida ya gama ya shafa mishi magani a wurin tare da rufe mishi ciwon dan dama komai a tsare take ba wani babban ciwo bane, fitowa sukayi duk da haka saida ya bashi magani dan kawar da duk wani zargi yace yasha saboda kar yayi zazzab’i ko hannun yayi kumburi, a haka suka d’auko hanyar dawowa gida, wannan karan Abbas ne ya tuk’a motar har suka iso layinsu.
Kamar yanda Salma ta fad’a musu haka suka aiwatar da komai, Ma’arufa na ganin motar Abbas ta danno cikin layin ta taho a guje ta shiga gaban motar har saida ta bugeta kuma taji zafi, take ta fad’i a wurin tayi kamar ta suma amma tana jin duk abinda zai faru, jakar kayan dake hannunta ce ta fad’i gefe, inda d’an kwalinta kuma ya rufe mata fuska, cikin tashin hankali Abbas ya fito tare da Abdul suna salati da sallalami, suna zuwa gaban budurwar da ke kwance suka ganta kamar babu rai, amma kuma babu alamar rauni a jikinta ko d’aya, a hankali Abdul ya sunkuya yana kiran ” Baiwar Allah, baiwar Allah kinji ciwo ne?”
Jin shiru yasa Abbas d’agowa ya kalli Abdul sukayi ido hud’u yace “Ko dai ta mutu ne?”
Ido waje Abdul yace “Ban sani ba Dady, mu kaita asibiti to.”
Da sauri ya d’ago ya juya ya ga babu alamar mutane a wurin dan unguwar silent ce, dan haka ya tak’ark’are zai kamata yace wa Abdul “Help me mu sata mota.”
Da sauri suka kamata suka nufi mota da ita zasu saka ta gidan baya, k’aramin kallabinta ya fad’i k’asa fuskarta ta bayyana, dammm! Abbas yaji gabanshi ya fad’i saboda kallon fuskarta da yayi, har suka sakata a ciki Abdul ya d’auko jakarta Abbas bai daina kallonta ba, tabbas babu kama a fuska, amma dai yana jin kamar zai tuna wani abu a game da yarinyar, wani yanayi yake ji da bai iya fad’in takamaimai abinda yake ji ba lokaci gida, har Abdul ya saka jakarta bayan inda take zaune ya rufe Abbas na tsaye, Abdul ne yace “Dady ko ka santa ne?”
Da d’an sauri ya kalleshi, maimaita tambayar yayi a ranshi *ko na santa?* to a ina? Ya tambayi kanshi, cikin sanyin jiki da rashin kuzari ya rufe motar hakan yasa Ma’arufa farkawa, a zabure, saida ta juya da k’arfi ta ganta a mota sai kawai ta fashe da kuka da k’ok’arin bud’e motar tana fad’in “Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ku rabu dani karku cutar dani, dan Allah kuyi hak’uri kunji ku sauke ni anan, zan koma gidanmu ma.”
Jin ta bud’e motar yasa su zagayawa wajenta da sauri suna son suji akan su wa take magana, fitowa tayi amma saboda iya shege saita durk’ushe alamar k’afar ta ba zata taku ba, Abbas ne yace “Kinga baiwar Allah, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, babu abinda zamu miki, asibiti ne zamu kaiki kinji.”
Sake mik’ewa tayi tana kuka tace “A’a wallahi bana so, dan Allah ku barni na tafi kafin su riskeni a hanyata, wannan ba komai bane a wajena, nasha wahalar da tafi wannan ma kuma ban mutu ba.”
Zata taka k’afar ta sake cijewa ta d’yangasa ta da k’yar tana cije baki, lura da hakan da Abbas yayi yasa yace “Saurare ni baiwar Allah, da alama k’afar ki ta bugu sosai, ki zo mu kaiki asibiti daga nan saiki fad’a mana inda zaki je sai mu kaiki.”
Kamar gaske cikin kuka mai ban tausayi tace “A’a ba zanje ba, dan Allah ku barni na tafiya ta, na so ace had’arin nan da mukayi da ku ya zama silar mutuwa ta, amma gashi har ita kanta mutuwar ma bata son d’auka ta, ya Allah! Sai yaushe ne wannan azabar zata yaye?”
Yanda take magana da kuma yanda take rera kukan yasa jikinsu duk yin sanyin, a hankali Abbas yace “Baiwar Allah yanzu ina zaki je?”
Girgiza kai tayi tace “Ban sani ba.”
Abdul ne yace “To ina ne gidanku?”
Kallonshi tayi cikin share hawaye tace “Da nisa, ni ba ‘yar garin nan bace.”
Abdul ne ya sake cewa “Kuma kin tabbatar baki san inda zaki je ba?”
Cikin kuka tace “Kwana na hud’u a garin nan ina yawo bansan inda zan nufa ba.”
Abbas ne yace “To amma baki kowa anan ne?”
“Bana da.” Ta fad’a a tausashe, da mamaki yace “Amma kinsan baki da kowa me yasa kika zo nan?”
“Bani ce na zo ba, k’addara ce ta kawo ni nan.”
Ajiyar zuciya Abbas ya sauke yana tunanin abinyi, ya d’an jima a haka har Ma’arufa ta jawo jakarta tace “Sai anjimanku.”
Ta fara tafiya da k’yar tana d’yangasa k’afa Abbas yace “Dakata baiwar Allah.” Tsayawa tayi ta juyo shi kuma yace “Idan ba damuwa ki zo muje gidana, saina kira dr ya duba ki tunda kin k’i yarda muje asibiti.”
Shiru tayi tana jin wani farin ciki na shigarta na samun nasara, dan a yanda suka shirya dama shiga gidan ne zai musu wahala, amma tana shiga babu abinda zai tsayar da ita aikin daya kaita kawai zata fara, jin shirun yayi yawa hakan yasa Abdul cewa “Ki zo muje kinji, kar kiji tsoro, Abbanmu mutumin kirki ne, ki d’auka daga yanzu har zuwa lokacin da zaki bar fadarshi zaki kasance cikin aminci ne.”
Jim ta sake yi alamar tsoro kafin tace “Na yarda zan biku, Allah yasa va zaku cutar dani ba kamar yanda wanda na zo domin shi garin nan ya nemi cutar dani.”
Tabbas akwai labari mai ban tausayi a cikin rayuwarta, amma kuma ba yanzu ne lokacin da zasu sani ba, dan haka ta taho ta shiga da k’yar kafin suma suka shiga suka tayar, bata fi tafiyar minti biyu ba suka tsaya k’ofar gidan, horn yayi mai gadi ya bud’e mishi k’ofa tare da musu barka da zuwa, suna ratsawa suka shiga Ma’arufa ta saki baki tana kallon gidan, cab’! Ashe dama wannan masarautar ya gina ya shiga shi da iyalinshi? Gaskiya gurguwar nan ta cuce mu da bata bari wannan ya zama ubanmu ba, da wannan tunanin da take taji motar ta tsaya sun fita, fitowa tayi ita ma inda tabi bayansu tana sake k’are ma gidan kallo, kai kasan maganar ma ace an kashe kud’i a wurin b’ata yawun baki ne, dan ko a k’asashen waje ka gida wannan gida dole asan ka tara masu gidan rana, ji tayi kamar zata fad’i a daidai lokacin da ta taka k’afarta a teress d’in falon, ga wani masifaffen sanyi da k’amshi daya daketa, a lokacin suna kan dinning suna cin abinci dan haka suka zarce can, a tak’aice dai ta samu tarba sosai a gurin kowa da kuma sakin fuska banda Abba wanda har yanzu ranshi a b’ace yake, abincin ma ya fito ci ne saboda yaran karsu damu da damuwarshi tunda haka aka saba, nan Ma’arufa ta zauna aka yi serving d’in ta ita ma tana ji kamar tace wayyo ta wayyo kanta, abincin dare d’aya amma kai kace wata walima ce tasa aka shirya, nan suka ci abinci aka gama sai cewa tayi zata tafi, duk yanda suka so da ita ta bari a kira likita ta k’i, aka suka hak’ura Ammie tace bai kamata ta tafi ba tunda dare yayi kuma tace bata san kowa ba, a haka Ma’arufa ta samu yanda take so ma’ana masauki a gidan.