BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Da mamaki Mari ta kalleta tace “Kenan ke ba korarki sukayi ba? Amma me yasa ba zaki koma ba tunda suna so ki koma? Sannan meye sana’ar da kike anan d’in?”
Duk wata tambaya da Mari ta mata saida ta bata amsar ta, amma sai Mari ta k’yamaci abun ta nuna ba zata iya ba, dan haka Iklima tace “To idan kina ganin yanzu a duniyar nan ana taimako dan Allah ki fita ki jaraba nema ki gani, mace dai ba zata iya miki taimakon da a yanzu kike buk’ata ba sai namiji, to ki jaraba neman taimakon mazan ki gani idan basu miki kallon sama da k’asa ba.”
Mik’ewa tayi zata fita tace “Ki samu ruwa kiyi wanka, idan kin gama ki rufe min k’ofar d’akin dan ba ni kad’ai ke zaune ciki ba, idan har baki samu taimakon ba zaki iya dawowa ki same ni tunda kinga inda nake.”
Da kallo ta bita harta fita, tana fita ita ma ta d’auki jakar kayanta ta fito ta kama hanya, ina zata je? Wa zata nema taimako? Abinda ya sameta dalilin neman taimakon ne fa, tana cikin tafiyar ta tsaya bakin titi kamar wacce zata tsallaka amma tunaninta ba nan yake ba, tana haka kuwa wani matashin saurayi da alama irin yaran nan ne masu jiran shago ya mata magana, maganar ma bata alkairi ba saita banza, wai a nawa zata siyar zai biya? Jin haka saita tsorata ta dawo baya gidan Iklima, a gurguje dai nan suka had’e suka fara wannan rayuwa ta k’ask’anci, kamar yanda Mari tace ita k’aramar karuwa ce, domin kuwa duk kud’in da zata samu basa wuce na yan buk’atu abin ci abin sha yar sutura marar tsada, ciki kuma na girma tana rainonshi tare da tunanin irin tarbiyar da zata bawa wannan cikin idan ya fito, saida cikinta ya tsufa ta daina fita sai Iklima kad’ai, a wannan lokacin sai take jin Iklima kamar yer uwa da suka fito ciki d’aya, tana haihuwa ma Iklima ce tsaye kan komai kamar ita akawa haihuwar, har akayi suna sai dai *Nurul Huda* bata samun gatan da aka yanka mata rago ba har yau maganar da ake tana shekara shida da haihuwa, bayan haihuwarta tayi arba’in suka ci gaba daga inda suka tsaya, bata sake waiwayar gida ba bare tasan meke faruwa, sai dai tana had’uwa da yayan Khadi a cikin gari har ma su gaisa, lokacin da suka samu kud’i ne sai suka kama gidan hanya wanda duk matan aure ne a gidan, mace d’aya suke abin arzik’i da ita maman Husna, ita ma bata nuna musu tsana ko kyara shiyasa, ana haka Junaid ya ganta wajen bikin wani abokinshi sunje d’aukar abinci gidansu k’awar amaryar wacce ita ta asassa taron suna tsakiyar fili suna rawa, ita ba abokiyar ango bace bare kuma amarya, kawai mawak’in ne mutuminsu shine ya gayyace su kuma suka je, dama kuma in zasuje irin wannan shiri ake na musamman, dan ko rigar nono basa sakawa bare wando saboda ana so komai yasan an motsa shi, haka kawai yarinyar ta mishi yaji ta birge shi, ya kasa gajiya da kallonta, daga ranar ne fa yake bibiyar rayuwarta kuma har yanzu bai daina ba duk da yasan wacece ita, tak’aitaccen labarin Maryama kenan.
*Ci gaban labari*
Ya jinjina sosai da jin labarin, shirun da yayi yana tunani barkatai yasa Iklima mik’ewa tace “Na tafi ni saida safe.”
Bai iya kallonta ba har ta wuce, da k’yar shima ya tashi ya shiga motarshi sai dai babu kuzari a tare da shi, gida ya nufa cike da k’warin gwiwar jin wani hukunci daya yanke yana daf da isa gidan.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Tun yamma Hamna ke son amsar wayarta a hannun Ammar amma ta rasa yanda zatayi, har saida akayi sallah isha’i sannan ta shirya cikin shiga irin ta Amna sak ta nufi b’angaren na samari, tana isa bakin k’ofar ta tsaya tana k’wank’wasawa tare da yin sallama, Ammar da ke zaune falo shi kad’ai yana latsa wayarshi sai wayar Hamna aje gefenshi, a hankali ya d’ago kai ya sauke kan k’ofar, take kuma ya mayar da kallonshi kan wayarshi duk da dai muryar da Hamna keyi tayi sak data Amna, saida ya d’auki kusan minti biyar bai sake d’agowa ba kafin yace “Shigo.” A hakan ma ba tare daya kalli k’ofar ba.
Cikin nutsuwa kamar yanda tasan yer uwarta nayi ta shigo tana sake wata sallamar, bai amsa ba bai kuma kalleta ba har ta tsaya tsakiyar falon, a sanin data mishi yasa bata tsaya b’ata lokaci ba ta fara bayani kamar haka “Yaya Ammar, dama zan kira Mamanmu ne a wayar Hamna saboda tawa babu kati a ciki, sai tace wayar tana hannunka kuma kaga idan akayi sallah isha’i ba’a barinmu fita ko yara bare…”
Wannan bayani da take jin shi yake kamar saukan ruwan sama da k’ank’ara a tsakiyar kanshi, k’aguwa tasa ya d’auko wayar dan dama ta ishe shi saboda wayan kiran da ake ya mik’o mata, hannu ta zuro ta karb’a tace “Nagode.”
Sai lokacin kad’ai idonshi suka kalli na ta idon, gabanshi ne yaji ya fad’i da sauri ya d’auke idonshi daga kanta, juyawa tayi zata fita a lokacin kuma Jibril ya shigo falon da kular abinci a hannunshi, saida ta kusa kaiwa k’ofa ta juyo ta kece da dariya tace “Allah sarki boss, a hakane kake cewa kana son zama soja bayan baka iya gane waye wannan waye wannan, to kai fa ina ganin ko namiji ya zo maka a shigar mace saika yarda.”
Tunda ta fara magana yake hasosho irin muguntar da zai mata, hakan yasa shi kallon Jibril da suka fi kusa cikin kaushin murya yace “Wallahi kai zai ci wa uwa idan har baka rik’e min ita ba.”
Tsuru Jibril yayi ya juya ya kalli Hamna data tattare zanin atamfarta, to shi taya ma zai fara rik’e ta ne? Juyowa yayi ya kalli Ammar daya had’e fuskar nan kamar hadarin gabas, sai kawai ya juya da sauri ya nufi k’ofa, Hamna na ganin haka ta rufa a guje da tunanin ita zai kama, shi kuma yasan sai Ammar ya cuce shi, tunda kuma ba zai iya kamota ba gwara ya bar masa gidan, da kallo duka ya bisu kafin yayi k’wafa yace ” *Kankana* kenan, zaki shigo hannu na ne, zaki gane shayi ruwa ne.”Jibril kam k’ofar gidan ya zauna a teburin mai gadi yana cin abincin suna ‘yar hira.
Iyayen na zaune a falo suna hira k’asa kasa saboda Hajia na d’aki kar a dameta, wayar Zeinabu ce tayi k’ara tana neman agaji, d’auka tayi ta duba mai kiran hakan yasa gabanta tsinkewa ya fad’i, datse kiran tayi kafin ta mik’e tace tana zuwa ta shiga d’akin ta, maida kiran tayi da sauri kuwa aka d’auka ana fad’in “Eh lallai Zeinabu kin cika ‘yar halak, yanzu har ni zan dinga kiranki amma kina kashewa? To yayi kyau, ni dama ba wani abu yasa na kiraki ba na kira ne inji ya ake ciki? Wata kusan biyu kenan ba sak’onki bana mijinki, shine nake so naji ina aka kwana?”
Har yanzu gabanta bai bar fad’uwa ba a haka ta amsa mata murya k’asa k’asa da ” *Inna* Dan Allah kiyi hak’uri, wallahi bana shareki bane, abubuwa ne suka min yawa, colonel kuma nasan ba wai bai nemeki bane aiki ne dai yasha kanshi, amma kiyi hak’uri insha Allahu gobe zan aika miki da kud’in wata d’aya kafin colonel ya dawo.”
Da k’arfi tsohuwar tace “Duba Zeinabu, kinfi kowa sanin bana son ana min wasa da maganar kud’i, ki tabbatar gobe kin aiko min kud’in da zanyi cefanai dasu dan kayan abinci na sun k’are, sannan ba zan iya tsayawa jiran mijinki ba, ki kirashi a waya ki fad’a masa ya aiko min da sak’on kamar yanda mukayi yarjejeniya da ku, idan kuma ba haka ba wallahi wallahi *asiri zai tonu*, ehe!”
Da sauri tace “A’a Inna ba sai anyi haka ba, insha Allahu zan tura miki nawa sak’on gobe nan, yanzu ma dan dare yayi ne, colonel kuma zan kirashi yanzu na tuna mishi dan nasan sha’afa yayi.”