BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallonta yayi da mamaki, wato ta kira shi ne dan taji idan zab’in ya birgeshi, idan har yace bai mishi ba yasan dole zata canza mishi kuma cikin dubara, ganin kallon da yake mata yasa tayi murmushi tace “Kasan wani abu shalele? Ina matuk’ar k’aunar ka a zuciyata, kaine jin dad’i na da rayuwata, na zab’ar maka Umaima ne saboda kaga tafi sauran yan matan wayewa da ilimi, bata da kwaramniya da shiga abinda bai shafeta ba, sannan kaga tana koyon aiki a inda kaima kake aiki, shiyasa na maka wannan zab’in.”
Shi dama baida matsala da zab’in data mishi, matsalar shi kawai yan uwanshi dake cikin damuwa saboda zab’in nata, dan haka yace “Hajia, ni banda matsala da zab’in da kika min, kin sani nima ina sonki kuma ina son farin cikinki, saidai Hajia ‘yan uwa na ba duka ne suka gamsu da zab’in nan ba, idan zai yiwu dan Allah ki bar kowa ya zab’i wacce yake so.”
Wata hamshak’iyar dariya tayi tace “To meya shafeka da su? Ai ka barsu kawai babu abinda zai faru, duk wanda aka kaiwa macen d’akin shi ba zai fasa kulata ba.”
Cikin butsuwa yace “Hajiata, aure fa rayuwa ta din-din-din, ya kuke tunanin zasuyi farin ciki idan basa son junansu? Wallahi dukansu zasuji basu da maraba da marasa ‘yanci, Hajia dubeki mana ke da Alhaji, a shekarun nan da kuka d’auka tare kina ganin da babu soyayyar junanku a zuk’atanku da zaku iya zama da juna ne? Ko da kun zauna Hajia dole d’aya daga ciki yana jin an takura shi, wannan rayuwar ce bana so yan uwana suyi, Hajia Junaid yana da wacce yake so, wacce yasa mukayi doguwar tafiya dominta, haka ita ma Hamna tana da burin da take so ta cimma, lokacin auren da kika saka yayi daidai da lokacin daya kamata ta fara zuwa koyon darasin zanen ta, yanzu haka kuka na barota tanayi saboda tana ganin kamar an ruguza mata burinta ne, shi kanshi Junaid d’in yana can kukan ne kawai baiyi ba saboda shi namiji ne ya fita dauriya da juriya, dan Allah Hajia ki taimaka ki musu wannan alfarma.”
A hankalce ta kalleshi tace “To yanzu shalele sun turoka ne ka samar musu abinda suke so?”
Murmushi yayi yace “Hajia ban isa su turo ni ba? Na d’auka yanzu kika gama fad’in nine rayuwarki, hakan da suka bai isa yasa su turo ni ba? Sannan ni babu wanda ya turo ni, na fahimci damuwar kowane ne kuma nake rok’a musu alfarma a wurinki, idan kuma ba zan samu ba saina hak’ura, amma dai abun zai tsaya min a zuciyata ace na kasa samun wannan yar alfarmar a gurin kakata da nake da yak’inin babu mafi soyuwa a zuciyarta sama da ni.”
Shiru tayi ta zurfafa tunani akan buk’atar shalelen ta, ya zatayi Allah ya d’ora mata k’aunar shi, shi kuma jin shirun yasa ya mik’e yace “Saida safe Hajia.”
Tana kallo yake tafiya harya kusa kaiwa bakin k’ofa, da sauri tace “Shalele na.”
Cak ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, da murmushi a fuskarta tace “Na amince da buk’atar ka saboda jin dad’in ka, ka fad’awa Junaid zanyi magana da iyayenshi suje su nemo mishi auren yarinyar, amma karku d’auka zata samu karb’uwa a zuciya ta dan karuwa ce ita, sai kuma Hamna, ita ma ka fad’a mata zata iya tafiya duk inda take so indai ba zai kai ga fita k’asar waje ba, amma kuma ya zama dole ta zauna ta halarci bikin nan, dan yer uwarta ma na buk’atar ta a kusa da ita, idan sun amince da hakan to shikenan.”
Dariya yayi sosai ta nuna tsantsar farin cikinshi, da sauri ya zo gabanta ya durk’usa ya kamo hannunta ya sumbata yace “Allah ya bar min ke Hajia ta, nagode sosai da wannan alfarmar.”
Shafa kanshi tayi da hannu d’aya ta tallabo hab’arshi ta kalli farin cikin dake kan fuskarshi tace ” *Amar*.”
K’ura mata ido yayi dan bai cika jin sunanshi a bakinta ba, d’orawa tayi da “Ka ci gaba da farin ciki irin haka ko da bayan raina ne, wannan shine burina a kan ka, kuma ina fatan Umaima ta zamo macen da zata dinga saka ka farin ciki irin wannan, in tayi haka zata zama suruka ta farko data fara shiga zuciyata saboda kyautatawa, zan so ta, zan k’aunace, zan faranta mata rai, duniya zata mata dad’i, zan so duk abinda ya fito daga cikinta, suma ‘ya’yanku zan so duk abinda zai fito daga garesu, kaji ko?”
Murmushi ya mata sosai hakan yasa ta kama dogon hancinshi taja tana fad’in “Ka tashi kaje ka kwanta dare yayi, saida safe.”
Da haka ya baro mata d’akin, bai bi takan d’akin su Ummy ba dan yasan mahaifinsu na nan, a inda ya bar Hamna ya same ta tayi shiru, yana mata albishir taji dad’i, amma daya fad’a mata dole zata kasance a duk wata sabga sai kuma ta marairaice tace “Amma yah Amar ai kamar ba’a rabu da bukar bane aka haifi Abu.”
Dariya yayi yace “To yanda zamuyi shine, bara na samu Hajia na fad’a mata kin amince da auren ma kawai.”
Da gudu ta nufi falon tana fad’in “A’a yah Amar ba sai munyi haka da kai ba.”
A gurin Junaid ma farin ciki ba’a magana, Jibril ya tayashi murna sosai inda Ammar yayi gum yana kallonsu, da wannan kawai suka samu suka kwanta da huta gajiya.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Ko da Zeituna ta shiga gidan yau ma babu wannan hantarar da kyara, abun mamaki ne shine wanka da Jumma tace tayi saita kwanta dan taji dad’i, haka ta shiga wanka amma bata jima ba ta fito, ta zo aje bokitin hannunta ne ta bukkar kawu Mamu taji suna hira a harshen fulatanci, kawu Mamu taji yace “Ki dinga matsa mata fa tana wanka akai akai, dan ni dai ba zan iya fitar da wasu kud’i ba dan gyaran jikinta, shi kuma Alhajin yace baya son k’azanta da tsami.”
Jumma ce tace “To yanzu ma ba a gabanka ba nace taje tayi wankan ba? Ni wallahi gar yanzu ina d’an d’ard’ar da lamarin ne, bana son mu shiga bakin duniya, ina gudun azo mutumin nan kashe ta ma zaiyi.”
Cikin fad’a kawu Mamu yace “Ke wai wace irin jahila ce? Na fad’a miki ba kasheta zaiyi ba, buk’atar shi kawai yace zai biya ta duburarta fa saboda akwai aikin da yake so ya cimma, kullum ina gaya miki amma kina wane baud’ewa kamar ke ce za ayi abin da ita.”
Shiru dai Jumma tayi dan bata iya masifar, wannan batu da Zeituna taji shine yasa taji k’afafun ta na rawa jiri na fizgarta, cikin wani mawuyacin hali ta kai kanta bukkarsu, zaune tayi a k’asa inda ta shinfid’a tsohon hijabinta a kai, kasa fahimtar halin da take ciki tayi tsabar rud’un data shiga, tunda ta d’ora idonta wuri d’aya ta kasa d’aukewa, hakan yasa hawaye bin fuskarta wani bayan wani, tambayoyi ne jere reras take wa kanta kuma ta kasa samun amsarsu, kawunta karuwa yake son mayar da ita? Karuwar ma wacce za’a dinga mu’amula da ita ta bayanta? Nawa ya karb’a domin wannan lalatattar harkar? Wanene mutumin? Meyasa sai ni da ban tab’a iskanci ba zai zab’a? Me nayi kawu Mamu har haka da k’iyayyarshi tayi tsamari a kaina? Ya Allah gani gareka! Allah ka dubi halin da nake ciki ka kawo min d’auki? Domin kuwa da nayi wannan rayuwar da yake son jefa ni har gwara na mutu ace bana raye, tana gama wannan tunanin kuma saita fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yanda taga safe haka taga wannan dare bata rintsa ba tana sak’ada warwara, ta rasa mafita akan yanda zatayi, da wannan har ta wayi gari tayi abinda ya sawak’ata nufi wajen aikinta.
*Gaga’s family*
Kamar kullum dai Hajia na zaune kan kujerar data saba zama, inda yara da ma wasu daga cikin iyayen ke zaune gefe sai maganganu k’asa k’asa, ko karyawa ba ayi ba bare kowa ya kama gabansa, Hamna da Amna da Jamila ce suka fito tare cikin shirinsu na uniforme (tenue) d’in makaranta, dukansu da Hijabi amma banda Hamna da siririn d’an kwali ne kawai ta d’ora, kayan nasu komai ido d’aya ne ita da Amna hijabi kawai ya banbanta su, yanda suka saba haka suka gaishe da Hajia da kuma Sa’ada da lieutenant dake kusa, ganin Amna da Hamna zasu fita yasa Sa’ada cewa “Yan biyu na tafiya zakuyi ko karyawa bakuyi ba?”