BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*Jumare* ce yau ta kawowa Zeituna ziyara, tunda suka shiga d’akin ta dama ta fad’a mata kawu Mamu ne ya turota yace ta zo ta karb’ar mishi kud’i zai siyi magani bashi da lafiya, hankalin Zeituna ya tashi jin ance bashi da lafiya, can bayan gidan b’angaren ajiyar bak’i taje ta samu lieutenant ta fad’a mishi, kud’i ya bata masu yawa yace ta bata kuma zasu zo duba shi anjima da dare, ko da ta kawo mata kud’in ta bata zata tafi saida ta tsaya gaban kayan shafe shafenta ta d’auki wanda take so kafin ta fito, tare suka fito ta rakota tana fad’a mata cewa “Jumare dan Allah ki rik’e kud’in nan da kyau karki jefar a hanya, dan na sanki da shiririta da son wasa.”
Daidai suna kawowa farfajiya daidai tana fad’in “Dallah ni ki rabu dani ko, me kika d’auke ni to da zan kasa rik’e wannan kud’in? Kawai gani kike kin haifeni saboda kin auri mai kud’i kin ci kin sha kinyi taib’a.”
Zeituna bata ji dad’in abinda ta fad’a ba, musamman da farfajiyar akwai mutane cikin bak’in da suke shirye shiryen komawa garuruwansu. Duk abinda ta fad’a kan kunnuwan *Ammar*, jar bala’i, wannan wace yarinya ce? Uban waye ubanta a duk area nan? Har cikin gidanta kuma take fad’a mata haka? Tana cikin tafiya ya taho cikin takon isa yana fad’in “‘Yan mata ji mana.”
Cak Jumare ta tsaya tana kallonshi har ya zo kusanta, Zeituna da tasan yau yar uwarta ta had’u da daidai ita matsowa tayi ita ma tana kallonsu, saida ya kalleta sama da k’asa ya rik’e hab’a yace “Ke bafulatana ce?”
Fuskar mutumin dake tattare da haiba da kwarjini ta bala’in firgitata, da k’yar ta iya cewa “Eh.”
Ta fad’a a hankali, jinjina kai yayi yace “Kina jin hausa sosai?”
Zeituna ce tace “Tana ji ita ma.”
Ba tare daya kalli Zeituna ba yace “Kina iya gane kowane yare?”
Jumare ce ta d’aga kai alamar eh, dan haka ya gyara tsayuwa yace “Alhamdulillah.” Nuna Zeituna yayi yace “Wannan ya kike da ita?”
Kallon Zeituna tayi tace “Adda Zeitu? aunty na ce.”
Cikin kafeta da ido yace “Kina nufin dai ita ke gaba da ke?”
Da sauri ta kalleshi tace “Eh.”
*Gauuuu* ya d’auketa da wani bahagon mari, k’ara ta saki tare da sakin kayan hannunta ta durk’ushe, da sauri Zeituna ma ta durk’usa ta dafata, d’ago kai tayi ta kalleshi da nufin fad’a mishi wannan fa ita ba komai bane a wurinta, amma sai taji ya d’ora da “In kika bari na sake ganin wannan guntulallar k’afar taki a gidan nan wallahi sai kin gane kurenki, na kuma mareki kije ki turo ubanki kowaye shi, a shirye nake dana tsaya da kowa a gaban alk’ali indai akan uwata ne.”
Saida ya zuba hannun dama a aljihu ya fara takawa ya nufi falon Hajia, kamar an kirashi sai kuma ya tsaya ya sake dawowa ya sunkuya kusan fuskokinsu yace “Ke kalleni nan.”
D’agowa Jumare tayi ta kalleshi da jajayen idonta, saida ya mata alama yace “Kin fara hak’oran hankali ne?”
Duk da tana jin hausa amma yanzu saiya gindayar da ita, kallon Zeituna tayi da alamar tambayar me yake nufi? A harshen fulatanci Zeituna ta mata magana, hakan yasa ta kalleshi cikin muryar kuka tace “Eh sun fito min.”
Murmushi ya mata yace “To nan gaba idan kika sake mata rashin kunya Allah su zan zubar miki, kin gane.”
Tsaye yayi yana kallonta yace “Ya sunanki?”
Cikin kumburo baki da tsantsar fulatanci a bakinta tace “Jumare.”
Yatsina fuska yayi yace “Jumare kuma? Juma’a aka haife ki? To me yasa ba’a saka miki Jumma ba?”
D’an zaro ido tayi ta kalleshi, Jumma? Uwa ta fa kenan? A tunaninta yasan sunan mahaifiyarta ne shiyasa ya mata wannan shagub’en, ganin kallon da take masa yasa shi kallon Zeituna yace “Uwa ya gajiyarku?”
Bai kuma jira me za tace ba ya sa kai falon Hajia d’aukar magana, Zeituna kuma lallab’a Jumare tayi ta tafi gida, saida ta tafi ne tayi murmushi tana fatan hakan da yayi ya zama silar daidaita tsakaninta da Jumare.
Inda Maryama ta bar Hajia nan ya sameta shima, sai dai akwai mutane a falon wanda wasu ke shirin tafiya wasu kuma sai anjima, daga ciki akwai dangin Ummy, gaba d’aya yayi jam’i yace “Ina gajiyarku?”
Duka d’akin da lafiya lau suka amsa tare da d’orawa da “Ya taku gajiyar?”
K’ala babu wanda yace ma sai zaunawa da yayi kusa da Hajia yana kallonta tana kallonshi ita ma, ganin kallon da suke ma juna yasa Hajia k’ara had’e fuska tace “Da wane rashin mutumcin ka shigo kuma yau? Dan wannan murmushin na ka ya bayyana shegantaka ta kawoka.”
Hannunta ya kamo ya sumbata sannan ya kalli idonta yace “Hajia ina godiya, Allah ya saka miki da alkairinsa, Allah ya zundumaki aljanna bayan kinsha ruwan khausara, Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki kamar yanda kika saka rayuwata farin ciki.”
Cike da shewa ‘yan cikin d’akin suka saka tare da amsa mishi da “Ameen.”
Bai kulasu ba sai d’orawa da yayi da” Hajia ni kam babu abinda zan saka miki da shi a gidan duniyar nan, amma duk da haka zan sakawa ‘yata ta farko sunanki.”
Kallonshi kawai take bata tanka masa ba, matsowa yayi sosai kusa da ita cikin tattausa murya yanda babu mai jinsu yace “Hajia maganar al’adar nan ce na zo k’arasawa, ance a rana irin ta yau namiji yana bayar da rak’umi ne ko kuma wata kyauta mai tsoka, to gaskiya ni na zauna nayi tunani na kasa tunano abinda zaiyi daidai da dank’waleliyar jikar nan taki, shiyasa nace bara na kawo kaina saiki fad’i abinda kike so nayi.”
Dai lokacin tayi murmushin zaka raina kanka tace “Komai idan na fad’a za kayi?”
Cike da tabbatarwa yace “A shirye nake Hajiata.”
Ita ma saida ta sassauta murya tace “Jan rak’umi zaka kawo lafiyayye, saika had’o da kud’i million d’aya, sannan ka siya mata sark’a da d’an kunnai na zinariya, idan kayi haka ma ya wadatar.”
Tana fad’a ta d’an kawar da kanta alamar zaka gane kurenka, shi kuma murmushi ya mata yana shafa sumar kanshi, kafin yayi magana Allah ya kawo lieutenant d’akin, mik’ewa yayi da sauri ya tarbeshi yana fad’in “Yawwa Abba barka, kud’i nake so ka bani.”
Saida ya harareshi kafin ya mayar da hankalinshi kan mutanen d’akin suka gaisa sosai, daf da Hajia ya zo ya duk’a ya gaisheta, yana mik’ewa ya juya ashe Ammar na daf dashi a baya sai kuwa suka had’e, tsabar k’arfi yasa lieutenant yin baya yana neman fad’uwa, da azama Ammar ya tallaboshi baya, kallon jua sukayi ya sakar masa murmushi, d’aga shi yayi lieutenant kuma cikin fad’a yace “Meye haka wai? Yanzu dana fad’i kaji dad’i kenan?”
“Amma ai baka fad’i ba, Abba ina tare da kai fa, haka ba zai faru ba sai in k’asa ce tarufe min idona.”
Cikin fad’a yace “To yanzu uban me kake so da kake biyata a baya kamar wutsiya?”
Saida yasa hannaye aljihu kamar wani k’aramin yaro yace “Kud’i zaka bani?”
Da mamaki yace “Kud’i kuma? Gashi kuma ban iya tuna ranar daka bani ajiyar kud’i ba.”
Turo baki yayi irin shagwab’a yace “Abba ba fa ajiya na baka ba, kai ne kawai zaka bani kyauta.”
Hanya ya kata zai fita yace “To bana da.”
Bin bayanshi yayi yana fad’in “Ni dai ka bani kawai, idan ban tambayeka ba wa zan tambaya? Kai kad’ai ne fa ubana a garin nan, kuma duk hidimar nan da akayi sisinka ban nema ba.”
Juyowa yayi yace “Amma uban wa ya biya maka sadaki?”
“To ai kai ka biya na kowa da kowa, kaga kenan ba zanyi lissafi da wannan ba.”
Har saida ya kai bakin mota zai shiga ya rik’e murfin mota yace “Allah saika bani, in kuma kace ba zaka bayar ba zan je wajen abokaina nace su bani bashi, kaga ku za ama dariya ace d’a kuma jika ga ahalin Gaga amma ya rasa million biyu.”