BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna fitowa a falo ta samu Ameera kwance yanda ta barta tana ta latsa remonte tana canza tasha, kusanta ya matsa ya sunkuya yace “Gimbiya Ameera, yarinyar mamanta da babanta, yarinya yar baiwa mai sa’a, shalelen Ummy da Abba, zaki sha bonbon (alawa)?”

Kai ta girgiza mishi tare da cunno baki gaba cikin muryarta ta yara tace “A’a ni madaya na ke co.”

D’agowa yayi ya kalli Amna yace “Duk yanda akayi ke kika sa mata akai ta daina yarda duk wayon da za’a mata.”

Dariya tayi tace “Banda abun uban yan biyu waye zai shiga tsakaninka da yaranka?”

Ameera ya kalla yace “Muje to ki raka ni na siyo ko.”

Tsil ta diro daga kujerar tana jujjuyawa inda zata ga takalminta, tana ganinsu ta d’auka tasa ta rik’e hannunshi, saida ta juyo ta ma Amna bye bye tace “Ummy sai mun dawo.”

“A dawo lafiya.” Ta fad’a tana zama, kallonta yayi yace “Me kike so na taho miki dashi?”

D’an d’aga ido tayi alamar zatayi tunani yace “Zaki sha ayaba?”

Kallonshi tayi saita yamutsa fuska tace “Bana jin dad’inta yanzu.”

Tsayawa yayi yana mata wani shu’umin kallo yace “Tunda kika samu tawa ko?”

Bushewa tayi da dariya tare da rufe fuskarta da hannu d’aya tana fad’in “Ba haka bane.”

Hararanta yayi yace “Ba haka bane kamar ya? Kin samu lafiyayya kina ta moreta tana zazzaga miki yara bigu biyu biyu dole ki ce wannan ta fita a ranki, to kiji da kyau ita wannan d’in da kika raina sanfirin aubangiji ce.”

Tsayar da dariyarta tayi tace “To ai ita ma waccen d’in hakane.”

Juyawa yayi yana fad’in “Tunda kince haka bari na dawo yau zan sake baki ajiyar wasu yaran, amma wannan karan uku zan ajiye.”

Murmushi kawai tayi ta bisu da kallo, wannan magana kamar ya fad’a ne daidai amsawar mala’ikun rahama, a ranar ta gama al’adarta ta kimtsa kanta dan farin cikin mijinta, dama magani ne Ummy ke d’orata akai wanda shi tafi so, a ranar ma tasha zuciyarta babu tunanin komai, amma da yake akwai tsananin rabo sai gashi duk da babu tabbacin a wannan dare ya shiga amma daga lissafi za’a gane a wannan lokacin ne.

Sanda ta fara jin alamu ta d’auka ucler d’inta ce kawai ta zo mata da sabon salo, amma sai abun ya fara damunta ganin tana shan maganinta kuma a banza, saida taji bata son warin gas d’in da take aiki dashi ta fara tunanin ciki ne da ita, da sauri ta d’auki tsinken gwaji ta ma kanta, ai kuwa dai ta tabbata abinda take tunani, zaune tayi kan gado jiki a sanyaye ta dafe kai da hannaye biyu, k’walla taji sun cika mata ido tana shirin yin kuka, shigowarshi tasa ta zabura tana goge hawayen, b’oye tsinken tayi a hannunta tana kallonshi, shi ma wani tuhumammen kallo yake mata har ya tsaya gabanta yace “Lafiya?”

Kai ta girgiza masa kawai tana shirin fita daga d’akin, rik’ota yayi yana kallon fuskarta yace “Fad’a min me ya faru?”

Fuskarshi ta kalla sai kawai ta fashe da kuka ta fad’a jikinshi, cikin tashin hankali yace “Ke Amna lafiya? Me ya faru ne wai? Me aka miki? Ni ne na tab’a ki?”

Share hawayen ta fara yi hakan yasa shi tallabo fuskarta yana fad’in “Kiyi hak’uri idan nine na b’ata miki rai kinji, ban sani ba wallahi.”

Girgiza kai tayi alamar a’a, had’e girar sama da k’asa yayi yace “To me ye kike ma kuka?”

A hankali ta nuna masa hannunta ta bud’eshi daga dunk’ulewar data masa, hannu yasa ya d’auki tsinken ya duba sai kawai ya kalleta yana murmushi yace “Kice min har na cika aiki?”

Cike da damuwa tace “Yah Ammar bana so? Ciki ne fa?”

Da mamaki yace “Ba kya so Amna? Cikin na wa?”

Marairaicewa tayi tace “Yah Ammar ka fahimta mana, duka fa aurenmu har yanzu bamuyi shekara hud’u ba.”

Ba alamar wasa yace “Sai akayi me?”

Turo baki tayi tana d’an juyawa tana fad’in “Ni gaskiya bana so, haba kamar wata kaza.”

A hankali ya juyo da ita gabanshi yana kallon idonta yace “Shin ni ne kike so ki kira zakara a fakaice ko me? Amna miye na damuwa dan kin haihu sau uku a cikin shekaru hud’u? Haihuwar ince ba Allah bane ke bayarwa ba?”

Kamar za tayi kuka ta kalleshi tace “Eh hakane yah Ammar, amma kuma ai ana so a d’an huta, ka dubi su Alhaji fa ba suyi wayo ba har yanzu.

Saida ya gyara tsayuwa yace “Amna ince dai ni na miki cikin?”

D’aga kai tayi alamar eh, d’orawa yayi da “Kuma ni zaki haifa ma yaran ko?”

Nan ma kai ta d’aga sannan yace “To indai nine uban ina son kayana, ko duk wata ne ki bultso min su zan karb’a, duk wanda kika ga ya miki kallon rashin mutumci kallon daya nuna ana mamakin haihuwarki, to ki kalli k’wayar idon mace ki fad’a mata duk macen da mijinta ke sonta ita ke rirritsa.”

*To fa kunji wanda basa son haihuwa*

Cire kayan jikinsa ya fara yi zai shiga wanka yana fad’in “Ke ba ma dan baki da hankali ba sakarya ce ke, to miye na ki na damuwa ke da bake kika ma kanki cikin ba, ba saida na tab’a ki ba sannan kika yi cikin, wacce miji bai damu da ita ba zai tab’ata ne, yanzu fa da a shekara hud’un nan bamu samu haihuwa bane saiya zama tashin hankali har ana nuna mu da baki, a’a ka na daddage nayi cikin shima sai an min uya shege da buru-uba, to naje nayi d’in kiyi abinda za kiyi idan kin isa.”

Ban d’akin ya shiga tana ganin haka ta fito daga d’akin bata zame ko ina ba sai b’angaren Hajia, dan in ta zauna ya fito ma d’orawa zaiyi har jarabar ta motsa ya tattausheta a banza, dan yanzu ya fad’a mata ba duka ba zagi amma taji a jikinta, ita kuma a yanda Allah ya halliceta har tafi son dukan ma kan irin wawurar daya mata wani lokaci wacce ta kwana tana amai ga zazzab’i, duk da dai tasan yafi ta ma damuwa da kanta indai aka ce tana da ciki ko tana shayarwa, tanan b’angaren kam sai san barka.

Ai kam dai kamar yanda tayi tunani ne, dan ko da ya fito da masifar ya fito yana fad’in “Ke ni ban ma yarda dake ba, wallahi sai kin fad’a min ni ne ba kya so ko yaran ne kike bak’in cikin haifa min, in kuma raino da shayarwa ne baki iyawa fad’a min na ji.”

Shirun da yaji yasa ya d’auka ko tana falo, haka ya fito da towel d’in niyyar shi in tayi wasa ta sha matsa, amma sai bai same ta ba, murmushi yayi ya jinjina kai yace “Wato ta bar min gidan ma gaba d’aya ko, ga dodo wanda baisan ciwon kansa ba, ga mahaukaci idan nayi na gaji na bari kenan.”

Komawa yayi ciki yayi k’wafa yace “Zaki dawo ai zan ritsaki ne.”

*Sati uku* ya rage bikin Hamna, yau kuma ta tashi da shagalin bikin k’awarta da ita ma zatayi aure, ta shirya ma bikin sosai saboda a cewarta shine fitarta na k’arshe kafin ta fara gyaran jiki, d’aya daga cikin abokan Ammar ne na gaban goshinshi zaiyi mata ta biyu, dan haka babu abinda bai shirya halarta ba shima dan saka mishi da alkairin daya mishi. Rana ta farko anyi k’umshi, ta ganshi ya ganta sanda suka je d’aukar abinci, amma kai ka rantse wasu abokan hamayya ne dan babu wanda ya nuna yasan wani ma, a daren ranar akayi kamu inda aka rak’ashe sosai, ya kalleta yafi sau cikin carbi, tana wahalar da zuciyarshi sosai, tana gigita lissafinshi, tana sage mishi duk gwiwoyinshi, yana kishinta fiye da hangen mai tunani, yana jin zafin ganin tana bayyanar da abinda ya kamata ace ta mayar dashi sirrinsa shi kad’ai, sai dai babu ta yanda zai fahimtar da ita haka, baisan ta wace hanya zai bi ya nuna mata yafi kowa son ganin ta killace kanta, amma ya zaiyi da abinda yafi k’arfin wuta inji kishiyar k’onanniya, ya zuba mata ido tayi abinda take so, ko ba komai ma ai ta kusa zama ta wani, mallakin wanin shi ce ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected