BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Bed d’in shi ya shiga Sameera tayi kan Raihan dake kwance tana kuka, kamata tayi cike da tausayi tana kallon jikinta da duk ya canza ya fita hayyacinshi, tashinta tayi suka tafi d’akin ta ta kwantar da ita, zage mata zuf d’in rigarta tayi ta cire mata ya rage sai bras d’in ta da pant kawai, kallonta Sameera tayi da kyau tace “Raihan ki fad’a min gaskiya, shin kin watsar da tarbiyyar da muka baki ne?”
Zaune tayi ta janyo blanket d’in kan gadon ta rufe jikinta tana kuka tace “Wallahi ban zubar ba, Ammie bansan ya akayi hoton tsiraici na ya fito ba, Ammie ki yarda dani dan Allah.”
Sunkuyar da kai tayi tace “Ba zan iya yarda dake ba Raihan, domin kuwa yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba.”
Ammie dake tsaye ne cike da jimami tace “Ki had’a mata ruwa tayi wanka.”
Mik’ewa Sameera tayi inda Ammie ta kalli Raihan da duk jikinta ya sauya tace “Kinsan da gobe yace zai d’aura aurenki da Abdul?”
Da sauri ta kalleta kamar zatayi magana sai kuma tasa kuka tace “Ammie ba damuwa na amince, ni kuma zan tabbatarwa da iyayena a budurwa naje gidan mijina.”
♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Tun daren jiya Ma’aruf daya fad’awa Meena aikinsu ya kammala ta dinga saka mishi wani tunani tana nuna mishi dukiyar nan fa kamata yayi ace tashi ce shi kad’ai, farko baisa abun akai ba dan ba zai iya cutar da yar uwarsa akan dukiya ba, amma da dare suna zaune d’aki shi da Ma’arufa ya kalleta yace “…
22/06/2020 à 17:26 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
_Kyautarku ce_
*Momyn Dady*
*Lubabatu Shehu Shayi*
*Umman Modee*
*Sis Chappa*
*Zeinab*
*Hafsat Yahaya Ali*
*Choukra*
*A~A~S~*
*Maman Abulkhairi*
*Voisine Ruky*
*Maman Tasleem*
*Aisha Gimba*
*Rafi’a*
*Wahabijubaina*
*Hafsat Uba*
*Soumayya mahaman kaka*
*Ummu Khairat*
*Maman Chapa’atu*
*Fasma*
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_20_
“Gaskiya nayi farin ciki sosai da kuka amsa kira na, dama kuma nace su turo iyayensu ne domin a samu fahimtar juna sosai, yanzu Alhamdulillah zamu iya tsayar da magana.”
Lieutenant ne yace “Hakane Alhaji, kuma dama ai mu ya kamata mu fara zuwa Allah bai nufa ba sai yaran, amma yanzu mun zo muji da kanmu daga bakinku.”
Wani hukuncin ubanjigi sosai Labaran ke kallon tsohon saboda zamansu iri d’aya ne irin zaman rak’uman nan, kawai kamar had’in baki sai suka sa hannu suka d’an tura hularsu baya suka shafi goshi, tsam colonel yayi da ido ya kallesu ganin sunyi abun a tare kamar sun tsarashi dama, shi kanshi Labaran satar kallonshi yayi amma malam Rabi’u bai kula da hakan ba, nan suka ci gaba da tattaunawa suka tsayar da magana inda lieutenant ne yace “Idan har zaku lamunce mana zamu so ayi bikin nan da wata d’aya, da yake akwai sauran yan uwanshi da suma duk za’a aurar dasu nan da wata d’ayan, shiyasa muke so ayi lokaci d’aya a gama.”
Malam Rabi’u ne ya kalli yan uwan mahaifin Maryama da kuma yayan mahaifiyarta kafin yasa hannu ya maido da hularshi inda take wanda yayi daidai da Labaran ma ya dawo da tashi hular, cikin fara’a yace “Wannan ai ba wani abu bane, dama dalilin da yasa muka nemi ku zo kenan, dan haka ba wani abu kawai.”
Farin ciki sukayi inda lieutenant yace “To dama a shirye muka zo, dan haka.”
Colonel ya kalla da Labaran suka d’anyi k’usk’us kafin su kalli Junaid dake can gefensu, mik’ewa yayi ya fita jim kad’an saiga yara matasa suna shigo da akwatina masu kyau guda bakwai da kuma goro, nan suka tsayar da ranar daidai da sauran bikin tare da bayar da duk abinda ya dace, girkin da akayi dominsu aka fito musu da shi, har zasu fara ci sunawa juna bismillah muryar Labaran da malam a tare suka ce “A’a Alhamdulillah, ai ni bana cin naman tsintsaye.”
“A’a Alhamdulillah, ai ni bana cin naman tsintsaye.”
Wannan lokacin kallon juna sukayi a tare, murmushin da sukayi ne ya bayyanar da wani tabo dake fitowa a duka fuskokinsu a duk sanda sukayi dariya a gefen kumatunsu na dama, gaban Labaran ne yaji ya sake fad’uwa, amma banda malam da shi ko a jikinshi ma, haka dai suka gama cikin mutumta juna da girmamawa suka sake dawowa.
*Tun* daren jiya Alhaji ya d’aure wa Hajia yace fa babu fashi auren lieutenant, a k’arshe ma cewa yayi ta mishi lissafin abinda za’a buk’ata ya bayar, kamar wasa kuwa da safe haka ya sake sakata gaba saida tace kawai ya bada duk abinda yaga dama, aifa nan ya bata mamaki ta hanyar bata babbar enveloppe da kud’i har million uku ciki yace tayi idan ma basu isa ba tayi magana ya k’ara mata, sai ga Hajajju na kira a waya harda fita ita da drebanta wajen siyo kayan lefe da saurensu, amma ji take kamar ta mutu dan sam Zeituna bata mata ba, tana ganin bata dace da ajin d’an ta ba duk da yanzu d’an nata ya zama tsoho.
Da yamma Alhaji ya had’a kan yan uwa da abokan arzik’i suka kai akwati guda goma sha shida wanda kowace saida aka mata k’at da kaya a ciki gidansu Zeituna da goro salka biyu da kuma 1 million kud’in d’inkin kaya, kad’an ya rage Zeituna ta mutu tsabar bugawar da zuciyarta tayi, ita fa har yau a mafarki take ji da kuma ganin abun, ba zata tab’a yarda wai lieutenant ne zata aura ba, nan fa unguwa ta d’auki tsegumi k’asa k’asa anayi, wasu na fad’in ya siyar da ita saboda kud’i, wasu na fad’in kawai akwai surkullen da akayi har babban mutum kamar wannan ya kalli Zeituna yace yana sonta, to haka dai akayi aka gama Hajia ita ma kamar ta mutu.
*Ammar* na gama cin abinci ya kalli aunty yace “Aunty zan d’an fita, watak’ila ma na wuce ta wajen mutumin (mijinta) dan nasan akwai hira a bakinshi.”
Dariya tayi tace “Ai kam kamar ka sani, kasan shi baka raba shi da zance, amma kafin nan muyi hira mana.”
A tsanake ya kalleta ya sauke ajiyar zuciya, d’orawa tayi da “Ammar meke faruwa a gida? Tun shigowarka na hango damuwa tare da kai, sannan ga hannunka da bandeji, bugu da k’ari baka tab’a zuwan safe irin haka ba.”
Wata ajiyar zuciya ya sake saukewa amma baice komai ba, hakan yasa tayi murmushi tace “Hajia ce ko? Ammar ou dinga hak’uri da ita wata rana sai labari, ka duba ni ka gani mana, yanzu haka fa su Hamna sunfi shekara d’aya rabonsu da nan, kuma sun fad’a min suna son zuwa Hajia dai ce bata amince musu ba, amma kaga nayi hak’uri duk da cewar bayan rabuwata da mahaifinsu dana auri *Shu’aib* bamu samu haihuwa ba har yanzu, amma hakan baya damu na tunda ina tare da wanda zuciyata ke so, kaga dai ba cikin birni nake ba, sannan ba cikin daula ba kamar gidanku, amma wallahi hakan yafi min komai, kaima da wannan nake shawartarka da akayi hak’uri, idan ka samu wacce kake so sai kaga komai ya wuce.”
Cike da gamsuwa da bayaninta ya kalleta yace “Aunty wannan karan ma ba Hajia bace Alhaji ne, wai aunty jiya Alhaji yake cewa wai ya nemawa Abba auren yarinyar nan yar aiki, Zubaina take ko uwar wa ma? Kuma wai za’a d’aura auren ranar juma’a ta gobe, kiji fa?”