BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Cikin jinjina kai liman yace “Hakane.”
Imran ya kalla yace “Imran, kasan da maganar nan ko kuwa?”
Cikin ladabi yace “Na sani Baffa.”
Kallon mutanen dake d’akin yayi yace “A yammacin ranar da d’an uwana zai bar duniya sunyi magana da liman, bayan liman ya min bayani kuma na gamsu d’ari bisa d’ari, dan nasan ba zai fad’a min abinda ba haka ba, bayan liman kuma ya sake kiran *Falmata* ya sanar da ita an tsayar da maganar, hakan ya tabbatar min wannan shine burin d’an uwana na k’arshe, shiyasa na tara mu anan ina neman yardar kowa da had’in kai dan ina so na d’aura auren bayan sallah la’asar a yau d’in nan.”
Liman ne yace “Yallab’ai wannan ai ba wata matsala bace, nima a yanzu bana da wani buri daya wuce na ga anyi auren nan, da alama burin takawa kenan na k’arshe.”
Jinjina kai Abba yace ya kalli liman yace “Imran ka amince a d’aura auren nan yau?”
Cikin sanda kai k’asa yace “Bana da wata matsala Baffa, na so ace mahaifina yana raye zaiga wannan lokacin.”
Abba ne yace “To Alhamdulillah, tunda kun amince sai kowa yaje ya fara shirin data kamace shi kafin la’asar.”
Kamar saukar aradu sai kuwa matar waziri *Asabe* tace “Tab’dijam, lallai ma duniyar nan babu gaskiya, ace mutum lokacin da yana raye ba’a k’ago wannan labarin ba sai yanzu, humm.”
Kowa kallonta yayi, waziri kuma k’uri yayi da ido yana kallon yanayin Abba, dan yasan in ranshi ya b’ace ba fa da ita zaiyi ba da shi mijinta zaiyi, tabbas Abba yaji maganar har cikin ranshi, dan k’arshen raina masa hankali ne matar tayi, da ace ba mace bace ko kuma a cikin family take da saiya kasheta da mari, amma daya saci kallon ‘yar tashi yaga har ta fara hawa sai kawai a ranshi yace “Zan barki da wannan ita ce daidai ke, idan na tabbatar kin shiga hankalinki zai dakatar da tarzomar.”
Abbas kuma hankalinshi na kan tashi yar rigimar, wani kallo data wa Asabe ne yasa shi rik’e hannunta yana murza yatsunta, gyara zama Sameera tayi da kyau tana kallonta da wani irin yanayi kafin tace “Ke kuma malama waya saka bakinki a cikin maganar family? Ku fa kawai kun zo nan ne fa a matsayin wanda zasu zama shaidu a cikin al’amarin.”
Sake matsowa tayi gaban kujerar kamar zata fad’o k’asa tace “To wai ma me kike nufi da abinda kika fad’a? Kina nufin mahaifina da liman zasu zauna su k’irk’iri labarin k’arya ne a cikin mutanen da baku fi su kiraku da bayinsu ba? Ke yanzu inba rashin mutumci ba har zaki kalli wannan ki fad’a masa maganar nan, ko kinsan abinda kika fad’a zai iya jaza miki hukuncin kisa ta hanyar rataya?”
A kowane sakan ranta ne take ji yana k’ara b’acewa, dan ji take kamar fa matar ta kalli Abbanta ne tace mishi mak’aryaci, ga kuma Abbas dake ci gaba da matsar yatsunta alamar tayi shiru tayi hak’uri, kenan ma yasan da an b’ata mata rai, mik’ewa taje tayi da niyyar tace matar ta fita sai kawai Ammie tace “Kiyi hak’uri takwara, koma ki zauna.”
Ko kallon Ammie ba tayi ba sai hararan matar take amma dai ba tace komai ba, hannunta Abbas ya kama ya jawo dan ta zauna amma tayi k’yam ta cije, liman ne yace “Hajia Fati kiyi hak’uri ki zauna muyi magana.”
Hawaye ne taf a idonta ta nuna Asabe tace “Abba na fa take nufin mak’aryaci ne, Abban nawa.”
K’aramin tsaki Abbas yayi ya mik’e tsaye ya had’e fuska ya kalleta yace “Malama fita anan, taron yara ne a gurin nan da zaki tayar mana da hankali.”
Juyawa tayi ta kalleshi ido tsaye da nufin yi mishi tas, amma suna had’a ido saiya mata kallon da yasan dole ta shafa mishi lafiya, yau da gobe tasa Abbas karantar matarshi da kuma iya zama da ita, duk zuciyarta da masifarta tana shakkarshi, duk yanda bata barin takwana shi kam tana kwana har ma ta hantse bata rama ba, sai dai inya gaya mata abin ya mata zafi sosai to ta kanyi zazzab’i ko ciwon kai na tsananin bak’in ciki da takaici, wani lokacin kuma kan yara take hucewa duk abinda sukayi saita musu fad’a harta had’a da duka, yanzun ma tana ganin ba zata iya ramawa ba saita juya kan Asabe wacce ita ta jima da tsorata, tunkararta tayi da sauri da niyyar cakumota ta jefar a k’asa…
*Wato takwara har yanzu ba’a shiryu ba kenan a gane cewa an girma.*
05/06/2020 à 13:18 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_8_
Washe gari ma tunda asuba suka shirya dan tafiya sadakar uku, a tare aka fito dan tafiya, su Junaid a mota d’aya suke sai Ammar dake tashi motar shi kad’ai kamar maye, wasu motocin har sun fara fita sai kawai Ammar ya fito daga motar shi ya zo ya tsaya gaban k’ofar Junaid dake mazaunin matuk’i, kallonshi yayi ya sauke gilashi yana jiran yaji me zai ce mishi, shiru sukayi sai kallon kallo ake, hakan yasa Amar dake baya zaune yace mishi “Fita ka dawo nan, shi zai tuk’a.”
Murya k’asa k’asa Junaid ya fito yana fad’in “Iko sai mai shi.”
Yana komawa baya Ammar ya shiga ya figi motar suka fita daga gidan suma, sun d’auki titi ana tafiya cikin yan uwa, tafiya ake su dai ukun suna hira amma banda shi daya rufe kunnuwa da abin sauraro (écouteur), cikin mintocin da basu kai awa ba sai gasu gidan roumji, kwanar da zaka shiga ta tabbatar da kai cikin garin sauran motocin suka shiga, amma me sai Ammar yayi tazarce zuwa titin tare da k’ara gudu, kallon kallo aka fara sai dai kowa ya kasa magana, Amar ne yayi k’arfin halin cewa “Ammar ina ga fa ka b’ata hanya.”
Shiru yayi mishi sai ma k’ara birkaka giya da yayi, kallonshi Junaid yayi zaiyi magana Amar ya mishi alama daga nan kar yace komai ya kalleshi kawai, Jibril na ganin haka saiya tab’e baki ya k’ara gyara zama yace “Ai dai duk tsiyarshi ba siyar damu zaiyi ba ko? To fak’at.”
Amar ne yace “Amma da dad’i musan inda zamuje.”
Muryar Ammar suka tsinta yana fad’in “Budurwar taka tasan da zuwanka ne?”
Da mamaki Junaid ya juyo ya kalli yan uwa suma kallonshi suke, a hankali Ammar ya karkato kai zuwa ga kallon Junaid dan yasan dashi yake, kallonshi yayi shima yace “A’a bata sani ba, ita ai tana nan garin.”
“Bata sani ba kuma shine zaka je har ka nemi aurenta? Baka tsoron ta d’auka ita ce rayuwarka hakan yasa ta rainaka.”
Yanda yake maganar yasa Junaid ji kamar mahaifinshi colonel ne ke maganar, dan haka yayi shiru baice komai ba, tsaki Ammar d’in yayi yace “Ku tabbatar idan munje zamu dawo yau d’in nan, dan ba zan iya kwana wani gari ba haka kawai.”
Tsuru tsuru sukayi da ido suna kallon juna, Jibril ne ya fad’a da k’arfi “Wai kana so kace yanzu can muka nufa?”
Yana sharara gudu yace “Hakane.”
“Amma…” Kasa k’arasawa Jibril yayi sai Amar daya ce “Amma d’an uwa Hajia da su Abba ba zasu ji dad’i ba, kuma ya zamuyi doguwar tafiya irin wannan ba tare da mun sanar dasu ba?”
Ba tare daya kalleshi ba yace “To idan har yanzu nono ake baka na aje ka anan mana ka koma ka tsotsa.”