BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shi kanshi tunda tace wai na bar maka gidanka tasa yaji kamar ta soka mishi mashi, kai shi fa wallahi tallahi idan ta sake maganar zata rabu dashi saiya zaro harshenta ya datsashi biyu, ta yanda gobe ba zata sake fad’in haka ba, yo inba ta raina shi ba kan wata yar iska da bata san ma akan me ake magana ba zata fad’a masa hakanen, da marinshi tayi duk da yafi mishi sauk’i kan tahowarta, yanzun haka ya zo ne da niyyar indai zata koma tare dashi to zai durk’usa har gabanta ma ya bata hak’uri, abune da bai tab’a jin ko tsammanin zai ji shi akan wata hallita ba, zuciyarshi ma saida yaji wani zazzab’i ya kamata.

Da sauri ya matso kusan Ummy da nufin tambayarta ina take? Rik’e hannayenta yayi zaiyi magana Hamna ta fito da towel d’in Ummy d’aure da kuma d’an k’arami ta d’aure kanta dashi, tana ganin ta juya zata koma da wani saurin bala’i yasha gabanta, kallonshi tayi fuskarta a had’e shi ma kuma haka.

Saida ya furzar da iska ya saisaita numfashin shi dake jin kamar zai bar gangar jikinshi kafin yace “…

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:39 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_74_

“Uban waye yace ki fasa min waya?”

Wani kallon mamaki ta mishi, wayar shi ma yake magana akai? Sake had’e fuska tayi tace “An fasa d’in, me zakayi?”

Rik’e k’ugu yayi yace “Biya na zakiyi ko kuma jikinki ya fad’a miki.”

Tab’e baki tayi ta rab’ashi zata wuce ya sake tare ta yace “Sai fa kin biya ni yarinya.”

A hassale tace “Kai kasan ni ba matsiyaciya bace, amma ba zan biyaka ba dan kaji dad’in kiran wasu yan iska kana hira dasu.”

Da wani mamaki a fuskarshi yace “Iyeee Hamna, ni ne d’an iskan ko yan matan?”

Sama da k’asa ta harare shi ta juyo ta tsaya gaban gadon Ummy, bayanta ya tsaya yace “Allah sai kin biya ni kud’in wayata, na yafe miki sauran ma ki ban d’ari biyu, sauran babanki zai cika min.”

Juyowa tayi tace “Saboda shine ya fasa wayar? To ko ni dana fasa ba zan biya ba.”

Gashinta dake jik’e da ruwa ya fizgo da k’arfi ya matso da ita kusanshi, k’ara ta saki sanda ya rik’e gashin nata, rik’e hannunshi tayi tana kallon fuskarshi da ido jawur tana shirin yin kuka tace “Sake ni Ammar.”

Jinjiga kan yayi yace “Waye Ammar d’in?”

Da k’arfinta tace “Kai, kai ne Ammar, Ammar Ammar Ammar! Na fad’a sunanka ne ai.”

Sakin gashinta yayi ya jawo k’ugunta ya had’e da na shi yana mata wani kallo mai ma’anoni yace “Naji zan yafe miki kud’in, amma sai munje b’angarenmu.”

Hannu biyu tasa ta ture shi tace “Da wa? Ni? Har abada Ammar, wallahi sai ka…”

Leb’enta na k’asa yayi saurin cab’owa da yatsunshi biyu cikin tsananin tashin hankali yace “Karki yarda bakinki ya sake fad’in ba zaki koma gida na ba, tawa ce ke har abada, kin gane?”

Idonshi ta kalla tana sako da hawaye masu zafi tana fad’in “In dai har kana kula irinsu Amie, to ba gidanka ba kad’ai har da tsanarka saina koyawa kaina, zan tsaneka Ammar tsana ta har abada.”

Da sauri ya saketa yana sunkuyar da kanshi, hannu d’aya yasa yana murza fuskarshi yana sauke huci mai zafin gaske, kallonta yayi kallo na basira yace “Babu komai tsakani na da ita Hamna, yau na had’u da ita kuma a yau na bata lambata, amma sam ba abinda kike tunani bane.”

Da k’arfi ta tureshi baya tana fad’in “To miye inba haka ba? Akan me zaka bata lambarka? Me take da shi a jiki dani bana da shi?”

Da sauri ya rik’e hannayenta yace “Babu Hamna, bata da komai da yake birge ni ma, ke kad’ai ce ke birge ni a yanzu, bayan ke wallahi babu kowa a gabana.”

“Amm..” Da sauri Ummy dake tsaye ta zuba tagumi tana kallonsu, kanta har ya fara ciwo saboda cacar bakin nan (ni ma yanzu haka nawa kan ciwo yake Ummy, tunanin yaranki kad’ai nasa gabana ya fad’i), mamakin yanda suka manta da ita a d’akin suke ta maganarsu ma take, wani na fad’a wani ke d’auka shi ma ya fad’a, ita sun hanata damar fad’an wani abu ma, nuna musu k’asan gadon tayi tace “Ku zauna.”

Kallon Hamna yayi saida ta zauna k’asan tana rufe kafad’unta da k’aramin towel d’in kafin shi ma ya zauna yana ta kallon fuskarta, kan gadon Ummy ta zauna ta kalle shi a nutse tace “Me ya had’aka da k’awarta har ka bata lambarka?”

Zunbur ya sake gyara zama kamar mai zaman tahiya yana fad’in “Ummy yarinyar nan bata da hankali karki saurare ta, na kai uwa Zeituna wajen bikin Jumare, na dawo shine na ganta na tsaya muka gaisa…”

Duk abinda ya faru ya fad’awa Ummy kafin ya kalli Hamna yace “Shine dan ubanta ta fasa min wayata sabuwa, Allah sai kin biyani ko kuma na siyar da motarki.”

Nuna shi tayi da yatsa tace “Kar sake zagar min uba malam, ya isheka haka fa.”

Dafe k’irji yayi da hannu ya zaro ido yace “Lah na shiga uku, Hamna ni kike nunawa da yatsa? Mijinki ne ni fa.”

Hararanshi tayi tace “Ka sake zagina ma sai kaji tafi a fuskarka Allah.”

Ummy ya kalla yace “Shikenan Ummy ‘yarki wuta zata shiga.”

Cikin juya baki tace “Sai ka kaini ai tunda kai ke da wutar.”

Kallonshi Ummy tayi, wai fa so yake ta koma a hakan har ya fara jigata shi, amma dai nuna tsananin damuwar da kuma lallab’ata shine baisan ya zaiyi ba, har da zagi yake had’awa, to a hakan zata koma ko me yake nufi? Had’e fuska tayi ita ma tace “Taje ta fasa wayar, to bari kaji ba ita ba ko ni naga ubanka na waya da wata Allah bayan na fasa wayar ma saina fasa mishi kai, ai kai ta maka mai sauk’i ma, malam fitar min a d’aki.”

Galala ya kalli Ummy, me take nufi? Ganin baiyi niyar mik’ewa ba yasa Ummy kallon Hamna tace “Yar albarka tashi canza kayanki, zanje da kaina na d’auko miki kayanki adadin da kike buk’ata.”

Wata dariya ya shek’e da ita yana mik’ewa tsaye yace “Eh lallai Ummy ba zaki iya zama alk’aliya ba, kuma da nasan wariyar da zaki min kenan da ban kai uwata wajen bikin nan ba har sai an gama wannan yak’in.”

Mik’ewa tayi ita ma ta ja rigarshi tana fad’in “Muje waje a barta ta huta, saina bata maganin ciwon kai tasha saboda damuwar nan daka saka mata.”

Juyowa yayi ya kalleta yace “Ke yanzu zaki iya zama babu ni a kusa dake? Kinfa san abinda nake baki kina ci cikin dare.”

Ita kanta Hamna saida ta dara tace “Bana so, ka ci kayanka kai kad’ai.”

Tsaye yayi ya rik’e k’ugu yace “Ummy kin kassara min zuciyata wallahi, zan fita yanzu amma ba zan sake dawowa nemanta ba, amma Ummy ki tabbatar kin ware mata gadonta, dan zan dinga kawo mata ziyara.”

Kallonshi tayi tace “To bismillah kaga yanda zanyi da kai.”

Saida ya kai k’ofa ya juyo ya kalleta yace “An dake ni kuma an hanani kuma, ke dai baki da imani wallahi ko kad’an.”

Ummy ce tace “Zama da kai ne yasa ta rasa nata ita ma.”

Ko da ya shigo da dare da sabuwar waya ya saka layikan nashi a ciki, yana zaune yana duba sak’onnin dake shigo mishi ta WhatsApp yaga bak’uwar lamba ta turo mishi hotuna, shiga yayi dan ganin wanene, tashin hankali sanda ya bud’a hotunan, Amie ta turo mishi hotunan ta tsirara, wanda ke da kayan ma kamar ba’a saka ba na d’aukar hankali ne, da sauri ya lik’e idonshi yana fad’in “Ya salam.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected