BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Tafiya yayi kamar zai bar gari duk inda ya gani sai yaga kamar za’a kama shi, kuma har wannan lokacin yana tunanin anya kuwa abinda zakayi daidai ne? Da k’yar ya isa wata doguwar hanya da babu mutane sosai, nan kawai zuciyarshi ta yanke mishi ya ajeta bakin titi ko ta samu taimako a mata sutura daga wasu bayin Allah, haka kuwa yayi saida ya tabbatar babu kowa ya fito da ita ya aje tare da jakarta da d’an kwalinta kafin ya juya ya bar wurin zuciyarshi cunkushe jikinshi na rawa na rashin saboda da tsintar kai cikin gagarumin tashin hankali, daga nan gida ya nufa da tunani iri iri.
*Basraba*
Gidan sarauta gaba d’aya ya hargitse da hidima na walima da aka shirya, sosai aka ci aka sha kafin yamma tayi aka fara shirin tarban amare kamar yanda uwar d’aki ta buk’ata, yamma tayi rana tayi sanyi gidan ya k’ara yamutsewa ta ko ina saboda bak’i da suka fara shigowa da amaren, nan hadimai da bayi suka fara kai da kawowa suna nuna musu masaukinsu, haka aka dinga shiga da amaren suna gaishe da uwar d’aki da kuma sauran matan da kuma uwar gidansu gimbiya Ameera kafin aka wuce dasu nasu masaukin.
*A gurguje*
Da dare bayan jakadu sun shirya Jawahir wacce ita ta fara isowa gidan kafin Safiyya, hakan kuma na nufin ita ce gaba da Safiyya yau ita ke da sarki, sarki ma da kanshi ya tarasu su ukun ya nuna musu mahimmanci da darajar uwar gidanshi, sannan ya nuna musu yana son zaman lafiya da kuma had’a kansu, yana gamawa ya sallami kowace ya koma bed d’in shi.
Uwar d’aki da kanta ta turo jakadiyarta ta taimakawa sauran bayin aka shirya Jawahir cikin shiga ta alfarma kafin ta kamota har falon sarki tayi wa sarki magana sannan ta koma, izinin shiga ya mata bed d’in, cikin nutsuwa da jin kunya ta shiga kanta k’asa, kan gado ya nuna mata ta zauna shima ya zauna kusanta yana kallonta, ba laifi kam kyakyawa ce ga kuma kunya, saidai akwai k’ananan shekaru gareta da gani, ganin ta k’i d’agowa ta kalleshi yasa ya kalli hannayenta da suka sha lalle, sake kallonta yayi yace “Jawahir.”
Har zata d’ago kanta kuma saita tuna yana daf da ita dan haka ta k’i d’agowa ta amsa da “Na’a.”
Murmushi yayi dan ta birgeshi data kasa kallonshi hakan yasa ya mik’e ya kama hannunta yace “Muje muyi alwala muyi sallah.”
Mik’ewa tayi tabi bayanshi har toilet, saida ta d’aga ido ta kalli toilet d’in ganin ban d’aki kamar d’akin kwanan wani, tare sukayi alwala suka fito sukayi sallah, bayan sun kammala ne ya mata tambayoyi kan addininta musamman yanda zatayi wankan tsarki da kuma yanda take sallahrta, abun mamaki shine amsa wasu tambayoyin da tayi ba daidai ba, bai wani nuna mata k’yama ko wani abu ba sai kawai ya bar abun a ranshi da d’aura niyyar d’ora mata a hankali harta fahimta, a nutse ya kalleta yace “Kina buk’atar wani abu ne da zaki ci?”
Kai ta girgiza alamar a’a, mik’ewa yayi tana kallo yayi shirin baccinshi tana zaune, ba zato ba tsammani taji ya kamo hannunta ya zaunar akan gadon ya koma ya kashe hasken d’akin sannan ya dawo, kwantar da ita yayi kamar wata beby ya kwanta gefenta, a hankali cikin nutsuwa da dabara ya samu ya lallab’a ta har ta zama cikakkiyar mace a wannan daren.
Kamar yanda mahaifanta suka rad’a mata tun kafin auren hakane ta kasance, a lokacin daya shiga ban d’aki dan tsarkake jikinshi cike da k’arfin halin duk da bata iya wa haka ta mik’e ta ta saka kayanta tayi sauri ta yaye wannan zanin gadon ta tura k’ark’ashin gado sannan ta zauna bakin gadon, yana fitowa ya kalleta da mamaki ya k’araso yana fad’in “Jawahir, ya zaki takura kanki haka? Kije kiyi wanka kinji.”
Cike da dagiya ta murmusa kanta k’asa tace “Ba komai, dama zan canza zanin ne kuma bansan a ina zan samu ba, shiyasa…”
Maganar ta tace ta sark’e haka kawai dan haka ya kamata ya nufi toilet da ita yana fad’in “Ki barshi kawai, ni zan canza wani da kaina, yanzu ki samu ki kula da kanki kinji ko.”
Yana fitowa ya fara k’ok’arin canza zanin, yana da niyyar idan ta fito ya tambayeta ina waccen zanin? Dan kar azo ta fita da shi sai kowa ya ga meya faru tunda akwai k’uruciya a tare da ita, amma jimawar da tayi tana kula da kanta da kuma kunyar fitowa yasa har bacci ya fara ridarshi saboda akwai gajiya a tare dashi, tana fitowa kuma jawota kawai yayi suka kwanta yana rumgume da ita a k’irjin shi kamar yar tsana.
*Abuja*
Cikin tsanani rud’u ya shigo gidan ya kuma zarce bed d’in shi, kile k’ofar yayi inda ya cire kayanshi ya shiga wanka, haka ya zauna ruwa na sauka a kanshi yana kuka kamar yaro k’arami, sam wunin ranar bai ma san ya akayi shi ba bare kuma yasan yanda ya gudanar da nashi, sanda Sameera ta ankara da motarshi taje d’akin dan suyi magana amma bai bud’e mata ba, haushi ne yasa ta baro k’ofar da niyyar ba zata sake komawa ba sai in ya fito dan kanshi, sam kamar ba gidan da aka d’aura aure ba, a haka har dare yayi yan mutanen da kenan ma suka watse, da dare kusan kowa ya kwanta amma banda Sameera dake tare da Raihan ana ta gyaran jiki, haka ma Abbas da abun duniya ya isheshi yake tunanin halin daya samu kanshi cikin d’an lokaci, sai kuma Harira data samu lambar Abbas d’in wurin Abdul raheem tana kwance kan k’aramin gadonta zata kira shi.
Yana kwance yana kallon sama kiran Harira ya doki kunnuwanshi, har ga Allah saida gabanshi ya fad’i kuma ya zabura ya tashi zaune, dan yanzu fa ya zama marar gaskiya ne kowane kira d’aukar shi yake wata matsalar ce, k’ara shiga damuwa yayi ganin bak’uwar lamba, amma wannan karan sai yayi saurin d’auka saboda maganin matsalar bai tsaya b’ata lokaci ba, shine ya fara cewa “Wake magana?”
Harira na jin muryarshi saida gabanta ita ma ya fad’i kafin ta daure tace “Harira ce.”
Da d’an k’arfi yace “What! Harira kuma? Wacece hakanan kuma?”
Murmushi tayi tace “Harira dai yar k’auye mai aiki gidanka, na kira ne muyi magana idan kana da lokaci?”
“Bana da to.” Ya fad’a a harzuk’e, dariya tayi dan tasan maganar yayi ne cikin jin haushi sannan tace “Dama wayar siyarwa ce gareni mai matuk’ar tsada wacce nake ganin da kai kad’ai zata dace, amma tunda kace baka da lokaci shikenan, saida safe, amma karka manta da abinda masu iya magana ke fad’a, *ko a k’ark’ashin k’asa ka shiga ka aikata abu to ka sani akwai ranar da zai fito*, bare kuma kai da a bayyane kayi komai naka ma, ka sani yanzu bana ganinka da wani sauran mutumci, tun ranar da nayi mugun gani, yallab’ai Abbas da karuwa a cikin gidanshi ba kunya ba tsoron Allah, tirr.”
D’orawa tayi da “Ban tab’a tunanin zaka iya aikata zina ba, amma sai gashi naga ka aikata har kisan kai ma, hakan fa na nuna rashin imaninka yayi yawa.”
Abbas da rigarshi tayi sharkaf da gumi yaji kanshi ya fara juyawa jikinshi ya fara kyarma ba tsayawa komai yace “Ke kuma nawa kike so?”
Wata dariyar jin dad’i tayi tace “Da idona naga duka ta’asar da kayi, a yanzu haka kuma ina rik’e da wayar yarinyar daka kashe mai d’auke da vidéon caskalenku, ni ba kud’i nake so sab’anin hankalinka ne, idan har kayi abinda nake so ni kuma zan rufa maka asiri har abada.”
“Ki fad’a min kawai me kike so da gaggawa? Sannan ki min alk’awarin zaki bani wayar nan idan har nayi abinda kike so.”
Saida ta gyara kwanciyarta kafin tace “Ina so ka aure ni, da ka amince ni kuma zan baka wayar tare da duka idanu na da sukaga abinda kayi.”