BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ko a jikinshi ko nace a kwalar rigarshi, binsu yayi babu gardama ko musu ko nadama a tare dashi, sai dai abun ya wuce yanda yayi tunaninshi, dan kai tsaye babban gidan kaso suka wuce dashi, kuma ba’a b’ata lokaci tsayawa tambayarshi wani abu ba, jefashi kawai sukayi ciki suka rufe bayan sun raba shi da wayarshi.
Babu wanda hankalinsa bai tashin ba sanda labarin ya riski kowa, Hamna da Hajia ma kuka suka shiga yi, a tsaye lieutenant yaje dan jin abinda ke faruwa? Fad’a, ya daki wani har ya ji masa ciwo yana kwance, sannan ya zagi tenu (ma’aikanta masu kaki) shine abinda aka fad’a mishi, al’amarin bai mishi dad’i ba, ranshi ya b’ace ta yanda ya juya ya tafiyarshi ba tare da yace komai ba, tunaninshi shine akan me Ammar ba zai yarda ya girma ba? Da yaranka har shida amma kana abu kamar yau aka haifeka.
Gidan ma daya fad’a musu basu ji dad’i ba, amma su Hajia suka ce ya zasuyi daya wuce hak’uri su fito da shi, Hamna kuma da taji sai ta aza sabon kuka tana fad’in laifinta ne ai, da bata kula saurayin ba duk da haka bata faru ba, sannan da bata nuna mishi shi ba jiya da yanzu yana gida. Nan dai lieutenant da Labaran suka shiga k’ok’arin fito dashi tun kafin ma kowa yasan da al’amarin, amma abun ya wuce yanda suka tunaninshi, dan abu d’aya da aka fad’a musu shine sai an musu sulhu sun ce sun yafe, kafin nan saida suka d’auki nauyin maganin yaron.
*A gurguje*
*Abu* fa ya ci tura yaja daga, duk abinda aka ce suyi yi sukeyi amma shiru, saida aka kwana *shida* kad’ai aka zauna dan ayi sulhu, mahaifin yaron mai sunan *Ak’il* da yayanshi duk suna tare dashi, sai lieutenant da Labaran da kuma Ammar d’in. Nan aka ce ya bashi hak’uri sannan babu shi babu shiga harkarshi har abada, nan fa ya rantse ya maimaita cewa ba zai bashi hak’uri ba, in ma suna da abunyi suje suyi kar su b’ata lokacinsu, Labaran ya lallab’a ya bashi hak’uri a wuce wurin, durk’usawa wada ba gajiyawa bane, amma yace wannan wanda dai sai dai ya ida takeshi ya shige cikin k’asa.
Hakan yasa lieutenant ranshi b’acewa yace su barshi kawai, fita yayi ya bar Labaran yana ta tausarshi, amma abun haushi yaron nan da shegiyar kafiya yace ba fa zai bayar ba, babu yanda za ayi an dakar masa d’an uwa kuma ace ya bayar da hak’uri dan an raina shi, shi ma Labaran haka ya baro wurin rai babu dad’i, su kuma suka ce zasu nuna mishi taurin kai da iskanci, tuni kuga gane shi suka kafa mishi kahon zuk’a.
*Daga* lokacin nan kam abubuwa suka canza mishi, ya jigata ya kuma yarda daya fara wahala, amma dai bai yarda ya nuna uban kowa ya gane ba (wuya makarantar kare), abinci da aka kawo masa kullum na safe daban na rana daban na dare daban, amma suma ana kawo shi zasu juye a nasu kwanon su cinye, wanda ake girkawa anan wanda maza ne ke surfa masarar ayi tuwon suke bashi, sai randa sukayi niyya ne suke rage mishi su zuba a leda su jefa mishi, bai tab’a nuna musu komai ba yana kallonsu dai duk ya gane fuskokinsu zaiyi wanka ya canza kayan da aka kawo mishi, amma fa sauro da rashin lafiyayyar shinfid’a da kuma rashin kankana ma kad’ai sun addabe shi, suna tsangwamarsa a wurin da jefa mishi magana, wankin ban d’aki da shara duk babu abinda basa saka shi a wurin, amma duk sanda yake aikin cikin izza da jin kai yake yin shi, ko wayarshi basa bashi kamar yanda suke ba wasu dan suyi kira su maido, sun hana shi ganin kowa kai kace ya saci kud’in gwamnati ko kisan kai, shi kuma ya riga daya san laifinshi bai kai hukuncin da suke mishi ba, shiyasa ma ya zuba musu ido yana k’arewa duk wanda ya masa da kallo, jira yake su gama nasu kafin ya darza musu salon tashi didimar.
*Comment…*
*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:40 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_76_
*Sati biyu* kenan da rufe shi, colonel da gwamna babu mai labari, lieutenant nan ne ya tsawatar kar wanda ya fad’a musu, amma tsakanin mata da miji sai Allah, yau dai abun ya damu Hamna ta yanda take jin ba zata k’ara kwana ba tare da mijinta ba, kiran Gambo tayi tana kuka, yana jin muryarta cikin kukan nan yasa dreba ya tsayar da mota, yana kan hanyar shi ta zuwa aéroport zai bar k’asa ya dakata, cikin tashin hankali da kulawa yace “Hamna me ya faru? Lafiya kike kuka? Me akayi?”
Cikin matsanancin kuka tace “Abba sun rufe yah Ammar, kuma Abba ya hanaa fad’a maka, dan Allah Abba ka taimaka ka fito dashi, ba fa wani laifi ya aikata ba.”
Ajiyar zuciya ya sauke ya rintse ido yace “Me yayi aka rufe shi? Tun yaushe yake rufen ma?”
“Abba satin shi biyu?”
Da k’arfi cikin razani yace “Me? 2 semaine? Me yasa Hamna? Shin yaron nan baya da gata ne ko me?”
Cikin kuka tace “Abba ne ya hana a fad’a maka.”
Tsaki yayi tare da kashe wayar, kallon dreban yayi yace”Muje.”
Babban mai tsaron lafiyarsa dake kujerar gaba ya kalla yace “Gida zamu je yanzun, kayi magana da dreban jirgin, ni zan kira président muyi magana.”
Bai tsaya tambayarshi ba dan in dai kaji yace gida to gidan Hajia yake nufi. A d’an lokacin da bai taka kara ya karya ba suka iso, suna shigowa garin ya kira colonel da a lokacin yake wani k’auye a *mali* ya fad’a mishi tare da neman taimakonshi, wai Allah zo kaji fad’a wajen uban Ammar, yanda kasan Gambo ne mai laifin haka ya dinga kirta masifa ba k’akk’autawa, shi dai bai taya shi ba har ya gama yace yaje gida zai tura mishi da wasu daga cikin sojoji, yo su za’a nunawa kaki, a k’arshe ma cewa yayi kaf jami’an sun ci…har da shi ma bai cire kanshi ba da lieutenant d’in.
Da isar shi gidan ko ciki bai shiga ba suma suka k’araso, Hajia kawai ya gaishe da ita yace zai je ya dawo yanzu, daya fito shi kanshi saida gabanshi ya fad’i, to me Hussein ke nufi daya turo wannan motocin, mota har hud’u da sojawa a ciki, duk akan menene? Duk fitowa sukayi suka shiga sara mishi da girmamawa, kafin babban cikinsu ya sanar dashi colonel ne ya turosu su bashi tsaro inda zaije, godiya ya musu kafin suka d’auki hanya, kamar wanda zasu tafi yak’i, shi ga nashi motocin dake ta jiniya wi wi wi, duk inda suka wuce sai an bisu da kallo sai dai zaka san babba ne ya zo.
Sanda suka isa, a lokacin da suka shiga wurin da matsiyacin gudu, kafatanin sojojin dake ciki kowa neman bindigarshi yayi ya sake rik’eta da kyau, kowa ya gama zama a ankare dan tunaninsu gari ne babu lafiya, ko ana wani babban fad’a ko kuma wani garin ne ake yak’i aka zo neman taimakonsu, duk sun tsaya cikin shirin kota kwana na tafiya, suna kallo sojojin ke ta durkowa daga cikin motocin, sai dai motar da gwamna ke ciki suka ga garde cord d’in shi ya bud’e yana hakimce bayanshi, da mamaki suka bishi da kallo suka kam, basu san da zuwanshi dan ana d’aukarsu wani lokacin dan su kare lafiyarshi, sai kawai ganinshi sukayi anan, to me ya kawo shi? Tambayar da kowa ya jefi kanshi da ita kenan, yana gaba garde d’inshi na bayanshi da bindigarshi ya d’ora hannu kanta, sai soja biyu a gaban gwamnan wanda suna cikin masu tsaronshi, sai sauran jami’an a bayansu duk suka k’araso wajensu suka tsaya, suma dai gefe sukayi da bindigoginsu suka shiga sarawa duk wanda ke sama dasu, da hannu kawai ya musu alamar su shiga ciki, jiki duk a sab’ule suka rufa masa baya da tunanin ko lafiya? Kujera suka matso mishi da ita ya zauna, amma saiya tokare ya tsaya ya kalli k’aramin major d’in yace “Je veux voir mon fils, je peux?”