BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

A cikin shekaru *goma sha biyu* Zeeya bata sake haihuwa ba sai b’ari data dinga yi har sau biyar, hakan yasa tace ma Suley ta hak’ura da haihuwar kawai Allah ya raya mata ukun ma, tuni kuma lokacin ta juya akalar burin kowa izuwa nata burin, tun farko data nuna ga aikin da take su suyi basuyi mata musu ba, dan dama ita ce mala’ikan gidan mai horo, dan Abbansu babu ruwanshi tsakaninsu dashi wasa da dariya ne, amma ita babu wannan sai had’e fuska kamar sojiya, Hassan ya duk’ufa nashi karatun inda yana kammalawa kafin ya samu aiki tace ai dole yayi aure, har Suley yace mata da son samu ne a aurar dasu baki d’aya, amma gudun kar ya kawo mata zab’inshi wacce zata zo ta sauya mata ra’ayin yara daga yanda suke mata biyayya yasa ta k’i yarda, haka yaran suka nunawa mahaifinshi ya rabu da ita kawai zasu mata biyayya, kuma kullum dama idan ya so mata magana akan tsaurin da take musu su ke nuna babu komai, saiya zab’i yayi shiru dan kar yaran su fahimci akwai rashin jituwa tsakaninsu da har zai saka su dinga saka bakinsu a al’amarinsu, *Sa’ada* yar aminiyarta ce wacce ke Agadez ita ma, sanin babu ruwanta ita da yarinyar tana musu kallon kidahumai yasa ta nema mishi aurenta, duk ba’a b’ata lokaci ba akayi komai aka gama, kasancewar tana karatu yasa bayan auren aka nema mata gurbin karatu anan ta ci gaba, duk da babu soyayya tsakaninsu suna mutumta junansu da girmamawa, baifi wata d’aya da aurensu ba Allah ya bata cikin ‘ yan biyu, lokacin kuma Hussein ya dawo gida hutu shima aka fara maganar aure, sai dai tace bata ga yarinyar data dace da Hussein ba, tana buk’atar yarinya wacce bata da wayewa da zurfin ilimi ta yanda ba zata damu ko saka ma rayuwar d’an ta ido ba, sannan wacce bata da wani gata ta yanda ko ya daketa zai daki banza () dan ta sanshi da zuciya, yana da kwana biyar da zuwa ya tuk’a Hajia da kanshi ya kaita bikin ‘yar k’awarta a Zinder, to fa anan ta had’u da *Zeinabu* a cikin k’awayen amarya take, duk yanda ta so ta kasance haka take, bugu da k’ari iyayenta sun rasu tana hannun kakarta ne *Inna* wacce ta haifi Babanta, su ma dai ba’a d’auki lokaci ba aka fara shirye shirye, su suna ganin zasu shiga babban gida ne, dan wannan lokacin *Alhaji Suleymane Hassan Gaga* ya zama d’an kasuwa lamba d’aya wanda ya zama komai da ruwanka, kampanin buga ledoji, kampanin sarrafa pliwa da sukari, kampanin sarrafa duk wani abu daya shafi roba irinsu robobi, bokiti tabarma da takalma na roba, gidajen mai wanda lokacin basuyi yawa sosai ba, baya ga shaguna ba adadi, da kuma kampaninshi na buga atamfofin dake garin *Niamey* , ya dai zama kicima shima, dan haka suke cewa kakarsu ya yanke sak’a, *(kuna musu kallon biri suna muku kallon bishiyar hawa)*, lokacin da aka saka ne ya bawa Hussein damar yin tafiya kafin lokacin, duka wata biyu yayi sai suka zo Zinder za ayi *18 Décembre* anan, bayan an kammala ana ta shirye shiryen komawa Hajia tace dole ya kira Zeinabu yaje ya sameta su gaisa karya yarda ya bar garin nan basu ga juna ba, Hussein ya kira Zeinabu da yar wayarta yace ta zo su gaisa kafin ya wuce dan shi ko gidansu bai sani ba saita waya dama suke gaisawa, Inna da rawar k’afa ita ta tayata shiryawa aka fesa mata turaruka sannan ta tafi a taxi, haka taje compagnie wajenshi babu mai tunanin faruwar wani abu a cikinsu, turarukan data fesa yasa hankalin Hussein tashi, hakan ya ingizashi har yayi abinda bai tab’a yi ba, duk da yaga Zeinabu kuma bata wani birgeshi ba, amma hakan ya kawar da budurcinta a wannan ranar, duk da ta so bijire masa amma daya tuna mata shine zai aureta sai tayi shiru ita ma, a wannan tarraya ne aka samu cikin *Junaid*.

Ana gobe d’aurin aure Inna taga laulayin Zeinabu yayi yawa, tana dubata ta gane ciki ne da ita, ko da ta tambayeta wane shegen ne? Ta fad’a mata wanda zata aura saida ta sauke ajiyar zuciya, nan tasa ta kirashi a waya wai yazo, ba tare da shakku ba yace idan ya zo me zai mata? Inna dai da taga yaron fitananne ne ba zai zo ba sai kawai ta amshi wayar ta fad’a mishi komai tare da cewa ita zata sanar ma da iyayenshi, nan fa hankalinshi ya tashi dan ba zai ce k’arya bane, sulhu ya nema anan ne fa Inna tace zata rufa asiri amma dole ya biyata, nan tace tunda dama ba mataimaki gareta ba to ya d’auke mata abinci da sutura, ba musu ya amince da hakan inda washe gari aka d’aura aure sukayi gum da bakinsu.

Bayan aurensu da wata uku Sa’ada ta haihu kuma ‘yan biyu, *Ammar* da *Amar*, Hajia na d’ora ido a kansu Amar ne yafi shiga ranta, tana kallonshi kawai taji kamar yaranta ne take kallo lokacin data haihu, Ammar kuma daya cika asibitin da kuka sai take ta mishi sharri wanda mutane ke dariya ana ganin na kaka da jika ne, to fa da irin wannan hantarar ta gina rashin jituwa tsakaninta da Ammar, iyayensu ma da suka gane tafi k’aunar Amar sai suka fi mayar da hankalinsu kanshi, indai suna gabanta duk abinda Ammar zaiyi sai sun hantareshi da zaginshi dan jin dad’in ta, Amar kuma baya laifi a wajensu dan ko bata gidan babu mai dukanshi, dan tsaf zata gurza maka rashin mutumci ko uban daya haife shi ne, a wannan lokacin cikin Zeinabu na wata hud’u, Husseina ma sai tace Labaran yayi aure dan tunda yasan ta hanyar da aka haifeshi ya mayar da hankalinshi kan kasuwanci harya tsaya da kafarshi, da k’yar ya samu yarinya mai nutsuwa da hankali wato *Soueiba*, amma data amince tana son shi tsaf ya fad’a mata tarihinshi bayan ta mishi alk’awarin ba zata gujeshi ba, haka tace taji ta gani kuma daga shi har mahaifiyarshi babu mai laifi, girma da mutumcin Suley da ake gani a gari yasa iyayenta basu wani zurfafa bincike ba suka bashi aurenta, dan dayawa d’auka suke Husseina matar Suley ce saboda har wannan lokacin miji bai samu ba, suma anyi aure lafiya lau lokacin kuma aka haifi Junaid, kuma suna da wata tara da aure ta haihu, bayan watanni ma Soueiba ta haifi Jibril.

*Bayan shekaru biyar* Gambo data durmiyashi cikin siyasa ya samu nutsuwa, yana zuwa tace mishi ta mishi mata aure zaiyi, bai ja da maganar ba shima ya amince, *Hadiza*, ita ce yarinyar data zab’a mishi wacce anan unguwarsu take, sam Hadiza bata son shi dan tana da wanda take so, amma fin k’arfi da ganin matsayinshi yasa babu yanda ta iya, had’a kai ‘yan uku sukayi suka had’a k’arfi da k’arfe suka gwangwaza sabon gini na gani na fad’a a wannan zamani, a *ADS* suka buga wannan gini tun lokacin unguwar babu mutane dayawa sai wane da wane, haka akayi tsari mai kyau a lokacin aka d’aura auren Gambo, tare suka dawo gidan dukansu harda su Labaran da suke jin ba zasu iya rayuwa da su ba dan sun zama d’aya, Zeeya tayi farin ciki da hura hanci da k’afafa ganin gidan da yaranta suka gina, sai dai bata ji dad’in tarewarsu tare da su Husseina ba sai taga kamar sun zamar mata k’arfen k’afa.

*I ❤ u true fan’s*
10/06/2020 à 12:07 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected