BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Shi kanshi Amar saida ya murmusa kafin yace “Kafi kowa sanin dole zamusha fad’a wurin Hajia, haka ma Abba da Ummy.”
Wata yar iskar dariya Ammar yayi ta gefen baki yace “Kuma kowa anan yasan waye za’a yiwa fad’an ba, ni ne, dan haka ban tsoron duk abinda zasu fad’a, na saba da jin hayaniyarsu a kai na dama.”
Junaid da shi dai ya ma rasa farin ciki zaiyi zasuje neman auren masoyiyarshi? Ko kuma yaji ba dad’i saboda bala’in da zasu tarar a gida? Dan ya sani dole sai Hajia ta d’auki mataki a kansu musamman taji me suka tafi yi, hakan yasa ya kallesu yace “Amma dan Allah yan uwa mu bar tafiyar nan ta zama sirri, dan in Hajia taji ranmu zai b’ace, ni kuma bana so saboda ni wani abun ya faru daku marar dad’i.”
Da wani kallo Ammar ya kalleshi yace “Sai me? Ta yanke duk hukuncin da zata yanke, ina da tabbas ba zata yanke mana hukuncin da zai cutar da mu ba saboda muna tare da shalelenta.”
Ajiyar zuciya Amar ya sauke danya fahimci kamar abun na d’an damun Ammar d’in, wayarshi ya d’auka ya sake danna wa’azin da yake sauraro yana fad’in “Allah ne ya taimaki tsohuwar nan ba’a siyar da bindiga haka kawai, da tuni hankalin kowa ya kwanta a gidan nan idan na wurga mata alburushi a tsakiyar zuciya.”
Junaid ne ya kalleshi yace “Kakar taka zaka kashe Ammar?”
Saida ya harareshi yace “Kakarku dai.”
Amar ne cikin dariya yace “Ko ba komai fa ta haifi ubanka.”
Nan ma juyowa yayi ya kalleshi yace “Ubanka dai ta haifa.”
Tintsirewa sukayi da dariya, kallon Junaid yayi yace “Ina fatan dai kasan inda zamu je? Ba sai munje ba ka samu gillisuwa a tsakiyar garin da ba na ubanninmu ba.”
Zaro ido Junaid yayi yace “Wallahi da gaskiyarka, ni duk cikin labarin da Iklima ta bani bata fad’a min sunan unguwarsu ba, amma bari na kirata saina tambaya.”
Jibril ne daga baya yace “Yayi dai zakin soyayya, Allah dai ya kai damo ga harawa.”
Juyowa Junaid yayi yana cikin neman lambar Iklima yace “Ai ko bai ci ba kai kasan zaiyi b’anna.”
Danna ok yayi ya d’ora a kunne, ba jimawa sosai ta d’auka suka gaisa kamar yanda suka saba, tambayarta yayi sunan unguwar tace gaskiya bata sani ba, amma ya bari ta kira Mari ta tambayeta, har zai kashe wayar tayi saurin cewa “Dakata.”
D’orawa tayi da “Da jima wata rana mun tab’a had’uwa da wani mutum a kasuwa babba, sun gaisa dashi sosai har take tambayarshi ya mamanta take, sai naji yace mata jikinta da sauk’i sosai, tabbas koma meye sunan unguwarsu babu nisa tsakaninsu da gidan bus d’in *Sonef*, dan tace min a unguwarsu yake aiki a gidan bus d’in.”
Godiya ya mata sosai kafin suyi sallama ya fad’awa yan uwan nashi yanda sukayi, shiru motar ta d’auka kowa da waya yana aikin latsawa, inda Jibril ya shiga tunanin inda zaiga yarinyar nan, gashi ko wani ba zai iya tambaya ita ba tunda babu wanda ya ganshi tare da ita, gashi tun jiya da akayi maganar garinsu yaji ya k’agu ya zo garin, yana matuk’ar son ganinta da idonshi, tayi aure? Ko kuma dai ta kasa samun jarumin namijin da zai iya zama da ita? Ko kuma dai… rasa ma abun tunanin yayi sai kawai yayi d’an k’aramin tsaki ya ci gaba da latsa wayarshi, haka suka dinga rarakar hanya ba ji ba gani ba tsayawa komai, dama bus ce idan ta zo *zinder* take tsayawa, amma su basu da dalilin tsayawa dan haka sukayi tazarce, daga zinder zuwa nan sai gasu a awa d’aya wanda yayi daidai da agogonsu k’arfe *11:20*, hakan na nufin sun ci awa hud’u a hanya, Jibril ne ya nuna musu inda gidan motar yake a sanin daya ma wurin, cikin sa’a suka iso sai Junaid dake tambayar gidan malam Muhammad wanda ya rasu shekara bakwai zuwa shida da suka wuce, mutum na farko ne yace bai sani ba, amma mace ta biyu koda ya tambaya tace “Eh na sani, ko ba Baban Maryama ba wacce tayi ciki? Ai yanzu basa waccen gidan mamanta na tare da kakarta ne.”
Daga cikin mota Ammar yace “Eh ita, ni ne nai mata cikin, na zo karb’an abinda ta haifa ne, ko zaki nuna mana gidan.”
K’uri ta masa da ido tana kallo, wannan wane marar kunya ne? Ganin kallon ya k’i k’arewa yasa shi bud’e murfin mota ya fito tare da d’ora duka gwiwoyin hannayeshi saman motar yace “Ya dai? Ko na tsaya da kyau ne ta yanda zaki ga ko na isa nayi wa mace ciki? Dube ni fa.”
Ya fad’a yana zagayowa inda suke tsaye tare da Junaid dake ta dariya, _(yan uwa haka fa jarumin yake, yana da sako zance ta yanda dangi ke ganinshi kamar faranci ne ke damunshi na d’an fari ko kuma rashin wayo, ni kuma nace a’a, haka wasu mutanen suke da sako zance ko wane iri ne)_, da sauri matar nan ta matsa tace “Da kun shiga kwanar nan kuka tambaya za’a nuna muku.”
Da sauri ta wuce ta bar wurin tana mamakin kalaman mutumin, tana gusawa kuma ta fara fad’a ai wanda yayi wa Maryama ciki ne ya zo amsar ‘yarshi, a k’aramin gari kuma da baya da maraba da k’auye sai gashi mata wasu har fitowa suke suna lek’e.
Suna shiga kwanar suka tambaya aka nuna musu, yaron daya nuna musu suka ce ya shiga ciki ya fad’a anyi bak’i, jim kad’an yaron ya fito tare da wata tsohuwa a bayanshi, masha Allah ta tsufa sai dai k’aramin jiki dake gareta amma doguwa ce sosai, Junaid dake kallonta ji yake kamar Mari yake kallo dan akwai kama a fuskarsu, d’aya bayan d’aya ta kallesu tana k’ara yafa gyalenta a kafad’a tana rufe rigarta munafata, cikin dattako tace “Ina kwananku yan samari.”
Junaid har k’asa ya duk’a yana fad’in “Ina kwana Hajia.”
Su Amar kuma daga tsaye suka gaisheta da girmamawa, amsawa tayi kafin ta kalli Ammar da hankalinshi ke kan waya tace “Gashi kuma ban shaida ku ba yara, daga ina haka? Naga kamar ba ‘yan garin nan ba.”
Junaid ne ya d’an kalli Amar hakan yasa Amar cewa “Hakane Hajia, ba garin nan muke ba, yanzu haka daga maradi muke, mun zo wajenku ne da muhimmiyar magana.”
Da mamaki a fuskarta tace “To! To ba damuwa, Allah yasa alkairi ke tafe da ku.”
Junaid ne yayi murmushi yace “Insha Allahu alkairi ne.”
“Shikenan, ina zuwa ko.” Ta fad’a tana juyawa ciki jiki a sanyaye, mamakinta me zai kawo zaratan samari haka har su hud’u gidan nan, iya tunaninta ta kasa gane me suka zo nema ko yi a wajensu, da haka ta samu d’iyar Baba zaune kan kujerar k’arfe tana tsiga musu yakuwa da zasuyi miyar taushe da ita wacce tun ranar data yanki jiki ta fad’i har yanzu tafiyarta sai jan k’afa d’aya take, maganarta ma ba duka kake fahimta ba, tsaye tayi gabanta cikin harshen barbarci tace ” Bak’i ne a wajen suka zo nan, sunce daga maradi suke, ni dai bana da kowa a can, dama daga Diffa suka ce, sai dai ko wajenki suka zo yan uwan mijinki ne, amma kuma basuyi kama da dangin Muhammad ba, dan gaskiya dukansu kyakyawa da su, wasu ma biyu a ciki kamar buzaye dan gashin kansu ma a murd’e yake, ko shakka babu kuma wannan ‘yan biyu ne, amma dai bari na shigo dasu sai muji meke tafe dasu ko?”
Saida ta gyad’a kai tare da d’aga harshenta sama ya manne a hak’oran ta na sama kamar yanda maganarta take yanzun tace “Tttoh.”
D’aki ta shiga ta fito da tabarma babba ta shinfid’a a bakin bishiyar magwaron dake akwai wanda baya ‘ya’ya, lek’awa tayi cikin dattako tace “Bismillah ku shigo.”
Shigowa sukayi suna doka uwar sallama, d’iyar baba ce ta amsa tana kallonsu ita ma d’aya bayan d’aya, izinin zama ta musu suka cire takalmi suka zauna, kaka ce ta wuce ta d’auko k’atuwar mazubin (tarmus) ruwa masu sanyi ta kawo musu, su uku ne suka sha amma Ammar yatsina fuska yayi alamar bai sha, kujera yar tsugunno kaka ta d’auko ta zauna kusa da d’iyar baba ta kallesu a tsanake tace “Yaran nan ina jinku, har yanzu na kasa tsayar da hankali na wuri d’aya saboda tunanin abinda kuke tafe da shi.”