BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Rugugugu! Sautin da gabanshi ya bayar kenan sanda ta ambacin sunan kankana, nisa dashi da tayi da kuma samun Amna sunyi tasiri sosai wajen mantar dashi ita, amma kuma bai kamata ace ya manta da ita ko dan abinda ya aikata mata, to amma ya zaiyi? Dole ya manta da ita tunda dai babu komai tsakaninsu, ciki ne dama yake zargin tana da kuma da akwai ciki da yanzu ya bayyana kowa yaji, dan baya tunanin Ummy zata iya yin abinda tayi yanzun, jin ta sake saka hannunshi a baki tana tsutsa yasa shi dawowa hayyacinshi, murmushin yak’e ya mata yace “To bari nayi wanka sai mu tafi tare.”

D’agata yayi daga jikinshi ya nufi hanyar d’akin kwananshi, tsayawa yayi ya juyo yace “Amma ke da baki shan kankana?”

“Haka kawai nake sonta yanzu.” D’akin ya nufa yana fad’in “Kinyi waya da kankanar asalin?”

Cikin d’aga murya tace “Eh, tana lafiya.”

Bayan isha’i suka fita, haka kawai suka dinga yawo suna zaga gari, sun jima sosai kafin ya mata siyayyar kayan ciye ciye suka dawo gida, tana fitowa daga cikin mota ta d’an matse cikinta tace “Wash.”

Kallonta yayi sanda yake fitowa yace ” Ya dai?”

Duk da abune da take wayan ji amma hakan baisa ta iya fad’a masa ba sai kawai tace “Ba komai, cikina ne ya d’an juya.”

Tsaye yayi har ta zagayo wurinshi ya kama hannunta yace “Ki kula fa Amna, karki ja min asara ki sani sabon aiki.”

Dariya kawai tayi suka nufi b’angarensu, saida ya tabbatar ta nutsu harta kwanta sannan ya zo ya ga Abba suka tattauna kafin daga bisani sukayi sallama.

*Washe gari* da safe kusan duk familyn ne a falon kowa da wanda ya zo ya gaisar, Ammar ma suna kusa da Zeituna zaune shi da Amna, da k’yar Junaid ya matsa mata ta zo gaishe da mutanen ba dan ta so ba, shiyasa ma ko da ta shigo ko sallama ba tayi ba, tana kallo yana gaishe da kowa amma banda ita, ganin hakan yasa Ammar k’ura mata ido, ko shi dai ai yana gaishe da kowa da girmamawa, amma tsabar rashin kunya ita ba sallama kuma ba gaishe da mutane, ba fa zai d’auka ba, wannan iskancin ba za’a yi shi dashi ba. Junaid na juyowa inda yake dan su gaisa ya kula da kallon da yake mata, cikin dubara ya d’an ja gyalenta suka koma gefe, juyawa tayi zata fita Junaid ya bita da kallo, Ammar daya kula da kowa na wurin ya bita da kallo amma babu mai k’arfin halin da zaiyi magana yasa shi kallon Junaid yace “Matarka raina mutane ne tayi?”

Ido a tsaitsaye ya kalleshi fatanshi kawai su rabu lafiya, ita kuma juyowa tayi tana mishi wanni kallo tace “Kamar ya?”

Saida ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yace “Naga kamar kinfi k’arfin ki gaishe da mutane, me kike ji dashi to?”

Cike da rainin tace “Ina da wani abu d’aya a rayuwata, duk ta yanda aka zo min haka nake zuwa nima, an nuna min ba’a k’aunata a gidan nan, shiyasa nima ban nuna ina k’aunar kowa ba.”

Idonta ya kalla yace “Amma ai kinsan girmama mutum ko? Sannan nan ba gidanki bane ko na mijinki, dolenki ki girmama duk wanda kika gani a ciki inhar kina da mutumci.”

Murmushi ta masa ta rumgume hannaye a k’irji tace ” Idan kuma bana da mutumcin fa?”

Mik’ewar da yayi tsaye yana d’an nad’e hannun rigarshi yasa Zeituna mik’ewa tana kallonshi tace “Dan Allah rabu da ita kaji, bata gajiya da rigima da kowa.”

Kallon Zeituna yayi yace “Um um uwa barni, ina so ne na fad’a mata da yaren da zata fahimta, duk rigimar da take muku ai dan bata samu daidai da ita bane, ni ba ita zan tsawatar ma ba mijin nata zan dallawa mari a gabanta ta gani, hakan zaisa ta shiga taitayinta.”

Kallon Junaid yayi rai a b’ace yace “Yo ba dan ma ya d’auki mutane ‘yan iska ba har wacece wannan yarinyar da zata zauna tana mana fitsara, yaushe ta shigo gidan naka har ta fara baka kulawar da kake ganin ta isa ta taka iyayenka kuma ta zauna lafiya, to in kai ka zama fanko wallahi ni akan iyayena babu yar iskar data nemi ta raina min su kuma na kalleta, dan ubanta kuma ta jaraba ta gani idan ban fizgo hanjin yarinya ba ta baki, to miye a cikin ido banda ruwa.”

“Da kyau Ammar, nagode, ka tabka rashin mutumcinka yau Hajia Zeeya’atu na bayanka, tunda shi gindinta ya mishi shamaki da zuciya.”

Kowa saida ya kalli Hajia da tayi maganar nan, Amna sagale ta kalle ta wacce ta tsargu da abinda ya fad’a take jin kamar da ita yake tunda dai ita ce matarshi, Ammar kuma a ranshi yace “Tunda rashin mutumci ne kenan kin d’aure min gindi? To na fasa.”

Maryama ce tace “To sai me? Ka mari mijina a gabana ka gani, wallahi da nima saina tsinke matarka da mari kuma a gabanka naga me zai faru.”

Juyawa yayi ya kalli Amna dake zaune ya tintsire da dariya ya nuna Amna yace “Ke wannan? Jar bala’i! Wallahi kuwa da kinja yau kowa ya kwana da yunwa, ke ki bar bala’i yayi kwana kinji, bana fad’a da mace ni sai maza mazan ma wanda suka k’osa, idan kuma kika cikani sai dai nasa ‘yar aljannata ta d’aukar min ke ta cilla a garu.”

Cikin taushin murya Amar yace “Dan Allah d’an uwa ka rabu da ita.”

Kallon Maryama yayi ita ma yace “Gaskiya baki kyauta ba, banyi tsammanin haka daga gareki ba.”

Zaune Ammar yayi yana kallon Amar yana fad’in “To dama me kake tsammani? Baka ga kakan nan nata ba mai masifar fad’a kamar Hajiar gidanmu.”

Amar da suke kallon juna ne ya mishi alama da ido cewa Hajiar fa na kallonka, duk da ya fahimci me yake nufi sai kawai ya gyara zamanshi ya ci uwar fuska kamar bashi ba, Husseina kad’ai ta iya fito da dariyarta amma sauran duk sun gimtse ta su, Hajia da kamar ta fashe ce tace “Shiyasa ba ma tab’a zama lafiya ni da kai, ba dai nice mai masifar fad’a ba? Zaka gani, akwai ranar da zaka nemi kaji ma fad’an nawa amma na maka nisa.”

Kallonta yayi fuska a had’e yace “Haba Hajiata, raha ce fa kawai, ke kinsan dani dake bata b’acewa, fad’an ki ai ni jinshi nake kamar kukan tsintsaye matuk’ar dad’i a kunne.”

Maryama dai basu ma san lokacin data fita ba tare da Junaid, yau ma fad’a sukayi sosai saboda yaji zafin abinda Ammar ya mishi, kuma yasan gaskiya ya fad’a mishi shiyasa ma bai biye mishi ba, amma fa daya mare shi da sai dai cikinsu d’aya ya kashe wani, yanzun ma k’ara fad’a mishi tayi dan sam zaman gidan nan nashi ya fice mata a rai, bata damu ta bar gidan ba tunda kowa na gidan baida mutumci a cewarta.

*Misalin 09:00* na safe Tanti Hadiza ta zo gidan, babban falon ta fara shiga cike da fargaban kalaman da zata ji daga Hajia, a lokacin tana d’akin Alhaji dan haka ta samu tarba mai kyau daga su Zeinabu da Soueiba da kuma Zeituna da bata tab’a ganinta ba ido da ido sai yau, a falon suke suna ta hira ta yaushe rabo inda suka cika mata gabanta da abun sha da ci, fitowar Hajia yasa duk wannan farin cikin ya b’ace kowa ta kama jikinta, duk da ta gane wacece amma bata wani kulata ba ta kalli Zeituna tace “Zaman me kuke anan? Ina ce aiki kuke a madafa.”

“Eh Hajia.” Ta fad’a tana mik’ewa ta nufi madafar, su Zeinabu ma mik’ewa sukayi inda Hadiza ke mamaki da maganar zuci cewa “Har yanzu bata canza ashe, yaushe matar nan zata daina bautar da matan ‘ya’yanta? Allah ya kyauta.”

Daga tsaye take k’are mata kallo sama da k’asa, murmushin gefen labb’a ta mata ta kawar da kai daga kallonta tana danna wayar hannunta tace “Wani ko a cikin kaskon mai ka saka shi haka zaka ciro shi a tsiyace, ank’i d’ana ba, amma sanyin ac da abincin gidanshi kad’ai ya isa ya gyara maka jiki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected