BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
A tsorace lieutenant yace “Me? Ni kuma?”
Wani kallon karka mayar da ni k’aramin mutum Alhaji ya mishi kafin ya kalli kawu Mamu dake shima yake kallon lieutenant yace “Karka damu, bai d’auka abinda zan fad’a ba kenan.”
Kawu Mamu kuma shi sam shekaru ko yayan mutumin ba shine a gabanshi indai har zai samu kud’i, to amma matsalar su aure ne ya kawosu bare yayi tsammanin samun kud’i dayawa daga garesu da suka zarce na Jano, dan haka kawai sai yace “A gaskiya Alhaji ba zai yiwu ba, domin kuwa Zeituna na mata miji, aure zan mata.”
Murmushi Alhaji yayi yana mishi kallon babu abinda ban sani ba yace “Na sani, amma a labarin dana samu mutumin da zaka had’a ta dashi ba mutumin kirki bane, shiyasa ma na gabatar da d’ana dan shine ya dace da ita, tana son shi, shi ma kuma yana sonta, sab’anin waccen had’in da zakayi babu soyayya a cikinshi.”
Kawu Mamu da wannan karan kwarjinin Alhaji ne ya hana shi kallon idonshi, zufa ya ji ta fara tsatsafo mishi saboda tsoro da fad’uwar da gabanshi keyi, ganin yayi shiru yasa Alhaji cewa “Karka damu, ka fad’a mana duk abinda waccen ya biya ni zan ninka maka shi, sannan ka tsaga wa Zeituna sadakinta, a take anan zan biyashi.”
Da k’arfi ya kalleshi yana d’an nazartarshi, wata zuciyar ce ta nuna mishi karya saki reshe ya kama ganye, inda wata zuciyar ke nuna mishi ai ba k’ananan mutane bane, dan haka kamar sub’utar baki sai kuwa yace “Da gaske zaku biya ko nawa ne?”
Lieutenant da yaji wata tambayar sakarci kallonshi yayi yace “A cikin mu nan akwai k’aramin yaro ne da za’a zauna ana maka karya? Ka fad’a kaga aiki da cikawa mana.”
Saida gaban kawu Mamu ya fad’i dan yanda ya mishi magana babu alamar arzik’i a ciki, Alhaji ya kalli yace “Shin zaku iya biyan waccen mutumin kud’in shi jaka d’ai-d’aya har jaka d’ari biyu?”
Alhaji ne ya kalli lieutenant wanda ya d’auka ko shi zai biya kud’in, hannu yasa aljihu da niyyar fito da kud’in daya d’auko saboda baisan ina zasu zo ba Alhaji ya dakatar da shi ta hanyar fito da kud’i daga aljihunshi ya aje gaban kawu Mamu yana fad’in “Wannan jaka d’ari biyar ne, ka biya mutumin kud’in shi da duk wani abu da kasan ya wa yarinyar ko kuma kai, saura sadakinta?”
Kawu Mamu jikinshi ne ya fara rawa hannayenshi na kakkarwa wajen d’aukar kud’in, mamaki yake ace masu kud’i basu d’auki kud’i a bakin komai ba, wai har riga rigan fito da kud’in suke ma, kenan kowanensu ya bawa jaka d’ari biyar baya? Ya d’auki kud’in yana ta zanzarin ya saka aljihu yaji Alhaji yace “Ka yanka mata sadaki mu biya.”
Kallonshi yayi duk ya rud’e yace “Alhaji ko nawa ma ku kawo, ai ku manyan mutane ne, Zeituna ta zama taku halak malak.”
Murmushi Alhaji yayi yace “Ka fad’a min sadakinta kawai na biya, domin kuwa akwai sharud’an da nake son gindaya maka bayan hakan daga yanzu har zuwa lokacin da amarya zata zama k’ark’sashin ikon d’ana.”
Da sauri lieutenant ya kalle shi, wai da gaske Alhaji yake aure zai mishi? To shi kuma meyasa duk yaran gidan nan sai shi Alhaji ya zab’a? Me zaiyi da wani aure yanzu? Auren kuma ma da budurwa wacce bata wuce sa’ar ‘ya’yan dana rik’e a hannu na ba (Hamna, Amna)? Meyasa Alhaji zaiyi haka ba tare da shawara ta ba? Auren farko na mahaifiya, aure na biyu kuma na mahaifi, d’an kawar da kallonshi yayi a zuciyarshi ya furta “Ya Allah.”
Kawu Mamu ne yace “Alhaji zaka iya biyan sadakin Zeituna?”
Kallonshi yayi yace “Saurara kaji, idan ka zana sadakinta ba wai yana nufin kai zakayi komai ba, mijinta nan da kanshi ne zai mata kayan d’aki da lefe da duk wani abunda ake wa kowace ‘ya ‘yar gata, dan haka sadakinta da zaka fad’a yanzu inhar zaka bi kamar yanda addini ya tsara ne, to fa zaka bawa yarinya kayanta ta mora kamar yanda ita ce da zaman auren ba kai ba, idan kuma zakayi yanda muka saba ne a al’adance, to shine zaka cinye ba tare da yarinyar ta gani ba, amma duk da haka karka manta wani abu, Zeituna zata shiga gidan da million dubu ma tafi k’arfin ta bare tsirarun kud’in sadakinta.”
A wannan karan kam yanda yaga shi kanshi Alhaji yayi magana sai al’amarin ya fara bashi tsoro, dan haka cikin rawar baki yace “Kawai ku bada jaka d’ari ma.”
Wani murmushi Alhaji yayi na takaicin abinda kawu Mamu ya fad’a, dan shi ya zo ne ya nuna mishi gaba da gabanta, ya so ya yanko kud’in da shi a ganinshi ya fad’i k’arshen kud’i shi kuma saiya ninka mishi, ba dan komai ba sai dan yasan darajar ‘yar da kuma bin dokokin da zai gindaya masa, hannu yasa aljihu duka rigarshi ya fito da kud’i da suka fi na d’azu, aje mishi yayi gabanshi yace “Ka rik’e wannan sadakin Zeituna nena biya lakadan ba ajalan ba, ka saka mana ranar da zaka d’aura aure mu zo mu d’auki surukata, tsinke bana buk’ata daga gareka.”
Kawu Mamu fashewa yayi da kuka yana kallon kud’in yace “Alhaji, yanzu wannan kud’in nawa haka? Wannan ai ba zan iya irgasu ba, kona fara ba zan gama ba sai na kai shekara guda.”
Murmushi Alhaji yayi yace “Million d’aya da rabi ne, a hakan ma dan ka fad’i kad’an ne, na so na biya sadakin da zai zautar da kai ko ka shiga hankalinka, ka gane cewa ‘ya’ya da Allah yake bamu ba dan mu wulak’antar da rayuwarsu bane musamman akan kud’i.”
Sam kawu Mamu hankalinshi bai kai ga tunanin abinda Alhaji ya fad’a masa ba, Alhaji ne yace “Yaushe ka saka ranar d’aurin auren?”
Lieutenant ne ya mishi kallon mahaifina ka ceceni mana, kamar zaka gurgunta rayuwata ne fa, Alhaji kuma bai kula shi ba sai kawu da yace “Kawai ku zab’i ranar data muku sai a d’aura auren.”
Alhaji kuma dake son gaggawar d’auke Zeituna daga hannunshi ne yace “Idan na ce maka ranar juma’ar nan ban takura ka ba?”
Kallonshi kawu Mamu yayi ya d’an fara lissafi kafin yace “Nan da kwana uku kenan?”
Kai ya jinjina mishi dan haka yace “Ai kawai babu wata damuwa, babu takura ko kad’an, gobe ma da kaina zanje duk rugagenmu na sanar da sauran dangi dan su zo a shafa da su.”
Alhaji ne yace “Abu biyu zuwa uku nake son fad’a maka, daga yanzu har zuwa lokacin da Zeituna zata bar gidan nan ban yarda ta sake zuwa aiki ba, sannan daga yanzu bana so aiki ko na gidanka ne tayi komai k’ank’antar shi, sannan kada ta zama cikin takura ko matsi har lokacin da za’a d’aura auren nan, idan ka kiyaye wannan sai mu zauna lafiya da kai, ina fatan ka fahimta?”
Mik’ewa Alhaji yayi lieutenant ma haka suka nufi mota kawu Mamu na fad’in ai za’a kiyaye, da haka suka shiga mota suka sake d’aukar hanyar komawa gida, sai lokacin ne Alhaji ya kalli lieutenant yace “Babba, nasan kana cike da mamakin abinda na aikata ko, kuma kana son sanin dalilin da yasa na aikata hakan, yarinyar nan tana cikin wani hali a gidan kawun nan nata, sam ba mutumin kirki bane tunda har zai iya karb’ar kud’i a hannun wani mutum ba dan ya aureta ba sai dan ya dinga lalata da ita ta duburarta, uk’ubar da suke saka yarinyar ma kad’ai bai isa ba shine harda neman ruguza rayuwarta, dalilin haka ta fara tunanin barin garin nan ko zata ji dad’i a ranta, domin kuwa ta kamu da son wani da bai ma san tana yi ba, ni kuma ina jin haka shiyasa nayi gaggawar d’aukar mataki tun kafin ta shiga uwa duniya.”
Jinjina kai lieutenant yayi yace “Kayi daidai Abba, amma maimakon ka had’a ta dani ai da wanda take so d’in ka had’a ta da shi, zata fi farin ciki a hakan amma bani ba, Abba na mata tsufa dayawa, ina da matata da yarana, bana da tunani ko niyyar k’ara aure, yarinyar! Abba a duba k’uruciyarta, kada a tauye ta saboda bata da gata.”