BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
“Maganar fa na da mahimmanci.”
Shiru ya mata baice komai ba hakan kuma yasa ta tashi zaune tace “Uhum wato ba ma ka da lokacina ko, to gaskiya ban yarda ba tashi muyi maganar, dan idan nace sai gobe to wuri ya k’ure.”
Yanda take jijjigashi ne yasa ya bud’e ido ya sauka daga kan gadon ya nunata da yatsa yace ” Allah badan ina tsoron hushin Ammie ba dana tsula miki d’an karan duka a daren nan, wai Sameta yaushe ne zakiyi hankali ke? Har abada ace ba zaki bar mijinki ya huta ba kamar wata…”
Bai k’arasa ba ya juya ya bar d’akin, dan dama maganganun daya fad’a mata ya fad’a ne dan karta bishi d’akin shi saboda ya santa da zuciya, shiyasa ya tak’aita daga nan, yana shiga d’akin shi ya kwanta amma saiya kasa bacci, dan basa raba shinfid’a inba rigima sukayi ba ko sunyi fad’a, tunanin halin da take yanzu yakeyi kafin daga bisani ya fara tunanin Salma, tabbas ya saki Salma tun ma ranar daya gane da sihiri ya aureta, sai dai bai fad’a ma kowa ba inba Abba ba, amma da ana saki billion daya ma salma, da wannan tunanin bacci ya d’auke shi.
Sameera ma haushin maganganun daya fad’a mata ne suka sakata yin kwanciyarta tana huci, ta kuma san safiya nayi zai fara bata hak’uri yana cewa dan ta barshi yayi bacci ne ya fad’a mata hakanan, da haka ita ma bacci ya d’auke ta.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Tunda Harira ta koma gida ta samu Baaba mai wake ta fad’a mata ta samu aiki a gidan tsohon mai gidanta, bud’ar bakin Baaba cewa tayi “Karki raina min hankali mana Harira, wane irin aiki ne mutanen nan zasu baki bayan abinda ya faru? Kawai ki fad’i gaskiya idan karuwanci zaki fara, koda yake ma ba wannan ne karo na farko da zaki fara ba, amma ki sani wallahi ni babu ruwana duk abinda kika je kikayi can ke kika jiyo da matsalarki.”
Bata damu da abinda ta fad’a ba haka ta ci gaba da shirye shiryen tafiya, da dare kuma ta tara k’annan ta a d’akin su ta fad’a musu zatayi tafiya, Karime ce mai wayon cikinsu dan haka tafisu shiga damuwa, sosai Harira ta rarrasheta tare da nuna mata zata je yin aiki ne dan su dinga samun abinci suna ci suna k’oshi, sannan ta dinga biya musu kud’in makaranta akan lokaci, sannan ta cire dubu uku ta basu a kud’in da Sameera ta bata tace ta b’oye karta yarda Baaba ta gani, haka kuwa akayi haka suka kwana da tunanin wayewar garin gobe.
*Mu had’e a shafi na gaba insha Allah.*
29/05/2020 à 11:10 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*MASOYA NA*_
*Wannan kyautar taku ce*
_My Heenat_
_My BK_
_Aunty Aishan Umma_
_Mamienmu_
_Maman Annur (ma chérie)_
_Momyn Dady_
_My Hawwa_
_Sweet Hawwer_
_Sis Chappa_
_Mamar Hassan_
_Yar Baba (yar tsohuwa)_
_Rahila_
_Voisine Ruky_
_Auntynmu *Madame Dakoro*, jinjinar ban girma tare da fatan alkairi zuwa gareki, hak’ik’a samun masoyiya kamarki abun alfahari ne ga kowane mutum mai zuciya, alkairi yana da dad’i komai k’ank’antarshi, farin cikin da kika saka *habibiyata* yasa naga ya dace nima na mik’o godiyata zuwa gareki , domin kuwa duk wanda zai farantawa wani na kusa da kai, to hak’ik’a kai ya farantawa, da wannan nake miki addu’a Allah ya sama rayuwarki albarka, Allah ya jik’an mahaifa, Allah ya albarkaci rayuwar ‘ya’yanki, Allah ya k’ara yalwata miki, Allah ya k’ara dank’on soyayya tsakaninki da mijinki, Allah ya saka miki da gidan aljanna, wannan k’ok’ari da kike Allah ne kad’ai zai iya biyanki, fatan farin ciki *mdm Dakoro*._
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_4_
*Tunda safe* Abbas ya shirya saboda tafiyar data kama shi dolenshi zuwa k’asar *Belgium*, a wannan lokacin yasan Sameera na kitchen dan in har yana gari da kanta take had’a mishi abin break, dan haka ya kira da téléphone d’in dake kitchen d’in, tafi kusa da wayar dan haka Razeena na matsowa zata d’auka ta kalleta tace “Bari na duba.”
Tana d’orawa a kunne tace “Hello.”
Murmushi ya saki kamar tana gabanshi yace “Uwar gida sarautar mata, daga kanki an gama mulki na kowane fanni, matar Abbas kuma k’anwar Abbas sannan garkuwar Abbas, uwar ‘ya’yan Abbas kuma wacce ke mulki a zuciyar Abbas, farin cikin gidana, na ce ko zan iya ganinki a part d’ina yanzun nan?”
Duk da kalamanshi sun bala’in fasa kanta kuma taji dad’i sosai har zuciyarta, amma dayake daren jiya ya b’ata mata rai sai ta dake tace ” Why not? I’m coming.”
Saida ya sake kashe murya yace “Takawarki lafiya ‘yar sarki jikar sarki k’anwa ga sarki mai mulkin garin *Basraba*.”
Aje wayar kawai tayi kafin ta kalli Razeena tace “Ki kula da sauran aikin, ina zuwa yanzun.”
K’ofar falon tasa makullinta ta bud’e ta shiga, wani katafaren falo ne daya gaji da kyau da tsaruwa, duk da tayi mamakin ganinshi zaune akan kujera yana d’aura takalminshi k’afa ciki bak’ak’e sai shek’i suke da d’aukar ido amma saita sake had’e rai ta rumgume hannaye tana kallonshi, d’ago kai yayi ya kalleta har dariya na kusan kubce mishi, amma dariyar da zaiyi itama rigima ce zai b’allowa kanshi dan haka yayi shiru, har ya gama d’aure takalmin ya mik’e tsaye yana ci gaba da kallonta ya kuma d’auki jakarshi bak’a ya d’ora a kafad’a, tabbas yayi kyau ya kuma birgeta, dan gaba d’aya bak’ak’en suit d’in daya saka sun zabge mishi shekarunshi, gabanta ya tako ya tsaya yana kallonta yace “Are you stil angry with me?”
Kai ta d’aga mishi alamar Eh, dan haka ya kamo hannunta ya marairaice yace “Sorry mai sunan mama na, tafiya zanyi yanzu bana so na tafi kina hushi dani, please kiyi hak’uri ki manta kinji.”
Wani kallo ta masa ta zage hannayenta tace “Abban Raihan wai me ya sa yanzu kake min haka? Sam yanzu baka da lokaci na, jiya fa magana na ce zanyi da kai amma ka k’i ban dama, amma yanzu ka tsaya gabana kana fad’a min wai zakayi tafiya.”
K’asa yayi da kanshi yayi shiru saboda baida hujjar kare kanshi, ya sani shi kanshi yanzu ya zama buzy sosai, ba kuma komai ya janyo hakan ba sai gabatowar zab’e, duk da baya siyasa amma yana da ruwa da tsaki a harkar sosai ta yanda ya kan zama haka, kallonta yayi yace “Amma ai nace kiyi hak’uri ko.”
Cikin hassala tace “Amma ai hak’urin jiya ne ka bani, kuma ban hak’ura ba har sai ka fad’a min me ka so fad’a a k’arshen zancen ka.”
“Na fa riga da na sha maganin zama dake Meera, kin daina wahalar dani yanzu.” Shine abinda ya fad’a cikin ranshi, amma a fili saiya shagwab’e yace “Dan Allah ki yafe min, tafiya zanyi fa na fad’a miki, kinsan kuma ance tafiyar hali, ba lallai na dawo garekkkk…” Bata bari ya k’arasa ba ta rufe mishi baki da tafin hannu tace “Shiiii, please don’t say that, you know i love u, huh?”
K’asa tayi da kanta sharrr sai hawaye saboda duk lokacin da yayi maganar rabuwa ko mutuwa to ta kan tuna had’arin daya shiga a baya ne, rumgumeta yayi yana shafa bayanta yace “I love u too my Falmata.”