BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallon idonshi tayi wanda suka cicciko da hawaye tayi wani murmushi tace “Ba zaka tab’a iya goge wannan bak’in fantin ba, kamar yanda ba zaka iya dawo min da mahaifina dana rasa ba a dalilin wautar d’a namiji irinka, haka kuma ba zaka tab’a sawa mahaifiyata ta kalli idona ba bare harta min magana irin ta uwa da d’iya, dan haka dan Allah Junaid ka rabu dani nayi rayuwata, ka barni na k’arasa k’azamar rayuwa ta a haka ba tare daka tuna min da baya ba, ina farin ciki da hakan.”

Murmushi ya mata yace “Magana kawai kikayi akan baya, amma gashi har na iya hango triste (damuwa) d’in da kike ciki, Maryama tu es en colère (kina cikin hushi), kamar fansa ce kike son d’auka ko kuma dai hushi ne ke sakaki abinda kikeyi.”

Cikin k’ok’arin b’oye damuwarta tace “Laise moi en paix (ka bani lafiya).”

Wucewa tayi yabi bayanta da kallo, Iklima ce ta zo wucewa ta gabanshi ya bata kud’in nan yace “Dan Allah Iklima ki rik’e wannan kud’in kuyi wani anfanin dashi, sannan ki sanar da Maryama irin son da nake mata, wallahi ko misk’ala zarra bana da niyyar cutar da ita, aurenta nake so nayi, yau d’in nan har nayi magana da magabata na, kuma na samu amincewar kowa, ita kad’ai ta rage min na samu ta ta amincewar, na rok’e ki Iklima ki taimaka min na shawo kanta.”

Da mamaki ta kalleshi tace “Kana nufin ka sanar a gidanku zaka aure ta?”

Cike da tabbatarwa yace “Na sanar mana.”

“Kuma sun amince ka ce?”

“Sosai ma, wallahi da gaske nake Iklima.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Kuma ka fad’a musu irin matar da kake son aure?”

“Na fad’a musu Iklima, amma ban fad’a musu tana da ‘ya ba, abu mai mahimmanci su san wacece zan aura.”

Zata wuce yace “Kud’in fa?”

Juyowa tayi tace “Ka barshi kawai mun gode, idan na karb’a zamu samu matsala da Mari ne.”

Wucewa tayi shi kam yabi bayansu da addu’ar shiriya, cikin sanyin jiki kamar kullum ya shiga motarshi ya kamo hanyar gida dan babu abinda zai tsinta a wajen.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Su Hamna yan mata sune a falon sama tare da yara ta kunna wak’a a wayarta sai rawa take yaran na biyarta a baya, Amna na zaune tana kallonsu tana dariya, sai Umminsu Ammar da ita ma take kallonsu tana dariyar tare da mahaifiyar Junaid, a gefe ma k’anwar Junaid ce *Jamila* duk da ba ita ke bi mishi ba, amma ita ce daidai su ma’ana warin haihuwa, dan yayarta *Umaima* bata cika son hayaniya ba itama, tana da tsatsauran ra’ayi, ita d’in ce wacce suka zama k’awaye da ita suna ta kallonsu, wannan hayaniyar ce tasa Ammar daya dawo falon ya zauna yana danna wayarshi yayi tsaki yafi dubu, in dai yace yaje yanzu dan yayi musu magana Ummi za tace ai zai takura ma yaranta ne, kuma yana da tabbacin in yaje sai ranshi ya sake b’aci saboda *kankana* *(sunan daya sakawa Hamna kenan saboda soyayyarta da kankana*), su kam basu san tsiyar da yake ba sai rawarsu suke kwasa, wannan dum-dum d’in da wajen ke amsawa yasa yake jin kamar benen zai fad’o mishi a kai, wani wawan tsaki ya sake ja yace “Wannan yarinyar wallahi saina karya mata k’afa ta yanda gobe ba zata iya rawar ba ma, ayi yarinya kamar dujal ne ya haifeta, mtssss.”

Wasu lambobi ya danna saiga lambar Amna ta bayyana a wayar tashi, kira ya aika mata da shi ta d’auka cikr da nutsuwa da fad’uwar gaba dan ita har ga Allah tana tsoronshi, duk da akwai banbanci tsakanin Hamna da Amna mai yawa, domin kuwa Hamna na da tsoron k’ananun dabbobi irun su k’adangare, kyankyaso, tsaka dacdai sauransu, Amna kuma bata tsoron wannan halittu kamar yanda take tsoron Ammar, Hamna kuma bata da zuciya da sanin ciwon kai, dan duk maganar da zaka fad’a mata komai zafinta saira karkad’e tace ko a kwalar rigarta, shiyasa duk maganganun da Ammar ke fad’a mata bata jin zafi, sai dai kuma akwai yab’a magana ita ma, dan tsoron da Amna ke masa ita bata mishi, idan taga ta shiga hannunshi kad’ai take tsorata da razana, sab’anin Amna kuma da magana ke mata mugun zafi, tana da zuciya da hushi, a tak’aice ma dai ita masifaffiyar amma fa ga wanda ya tab’a ta, idan kuma ka ganta zaka d’auka ko hannu ka saka mata a baki ba zata ciza ba, amma idan tana fad’a ko tayi zuciya to babu kyau, cikin sanyin murya ta amsa da “Na’am yaya Ammar.”

Sai kace a gabanshi take saboda yanda ya wani sake had’e rai murya k’asan mak’oshi yace “Ki fad’awa yarinyar nan ta kashe mana kid’an nan, idan kuma na samesu a nan ran uban kowa saiya b’ace.”

Yana fad’a ya kashe kiran tare da ci gaba da abinda yake, Amna kuma kallon wayar tayi kafin ta kalli Hamna tace “To shakira ya isa haka ko tunda *boss* yace a kashe wak’ar nan, da alama kuna damunsa ne.”

Kallonta Hamna tayi masha Allah kam kyakyawa ne ajin farko, suna da diri da k’ira gwanin ban sha’awa, amma duk da haka Hamna tafi haske sosai da tsayi kad’an, tab’e baki tayi tace “Shine ya kiraki kenan?”

Da ido kawai ta mata alamar eh, ci gaba tayi da rawarta tace “Ki kira ki fad’a masa bai isa ya katse mana jin dad’in mu ba, dan haka yanzu muka fara.”

*Hajia Zeinabu* (mahaifiyar Junaid) ce tace “Um um fa Hamna, hanyar lafiya abita da shekara, tunda yace ku kashe to ku kashe, ko kuma ki jasu kuje d’akin ku sai kuyi acan.”

Wata kyakyawar mata mai k’aramin jiki ce fara kuma doguwa ce tace “Saboda yace baya so shikenan sai a daina? Me zai hana ya fita waje tunda namiji ne shi, amma yana cikin gida kamar wata garar kunya.”

Zeinabu ce tace “Da dai kin basu shawara su koma ciki zaifi ai.”

Hamna ce ta kalli yaran tace “Kai mu ci gaba da nishad’inmu, kunsan boss ba fara’a yake ba bare maganar nishad’i, shi ya sa yake kishi da duk wanda yake yinsu.”

Tana maganar ne tana amma sai taga yaran kowa yayi zaune tare da mak’alewa wuri d’aya, tab’e baki tayi tace “Sai kace mala’ika nr shi daga ya turo sak’o ta waya amma duk kun tsorata.”

Kallonta ne ya kai kan Amna data kafeta da ido, cikin dubara Amna ta d’ora hannunta a bakinta da yatsa d’aya take mata nuni da k’ofar shigowa falon, da k’yar ta fahimci abinda take nuna mata ta juya dan ganin ko meye, ai ko ido cikin ido suka kalli juna ita da Ammar wanda yake tsaye k’ik’am ya cije gefen labb’enshi na k’asa, ai da gudu Hamna ta koma bayan Ummi tana mata rad’a wai “Dan Allah Ummi ki bashi hak’uri mu samu ya bar gidan nan.”

Ummi da tunda ta ganshi ta had’e rai kamar dai shi kalloshi take sosai, ganin yanda take kallonshi yasan sai ranshi ya b’ace in yayi magana, dan k’aramin aiki ne a gurin Ummi ta zageshi a gabansu har ma tayi yunk’urin marin shi, dan haka yayi k’wafa ya juya ya bar d’akin, yaran na gabin haka suka daka tsalle da shewa wai ya tafi bai dake su ba.

Yana barin nan kai tsaye asibitinsu ya wuce mai sunan *Clinik Aminci*, (na canza mata suna saboda kar na saka na ainahin sunan familyn ya fito fili), yana zuwa ya fito daga mota ya tunkari shiga ciki, a babban falon da mutane ke zama ya samu duk gurin zaman an cikeshi, kuma yana da tabbacin wanda yake da rendez-vous (appointment) da su ne, wata irin sallama ce yayi wanda na farko kawai yaji shi sai wanda suka ga bakinshi ya motsa, dan ranshi b’acewa yake idan ya zo asibitin ma, a ganinshi da yanzu watak’ila yana filin daga suna bada wuta, amma an zaunar dashi yana tambayar lafiyar mutane (mutum baya sanin abinda yake, haka kuma baka sanin mahimmancin abinda ke hannunka saika rasa shi), malamar asibitin dake zaune akan babban teburi wacce ita ke kula da wanda zasu shiga da kuma fara duba lafiyarsu, kallonshi kawai tayi dan ko ta gaishe shi ma ba amsawa zaiyi ba, tsaye yayi gabanta ya sauke jajayen idonshi akanta yace “Zan shiga, su bi layi da kyau, a kuma dinga shiga da hanzari saboda gudun b’ata min lokaci.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected