BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
D’aga kafad’a yayi alamar ko oho sannan aka ci gaba da sha’ani, sai dai har aka tashi daga taron bai sake ganin Hamna ba, wanda hakan ba k’aramin dad’i ya masa ba, dan dama ganinta cikin shigar nan data fito da komai nata yana tayar masa da hankali, sai yaga duk idon kowa a kanta yake. Nan aka koma gida aka raka kowace amarya ta sake shiga d’akinta. Duk abinda aka saka ma rana dai k’ararre ne dama, sai gashi anyi an gama kowa ya kama gabanshi an bar amare da angaye da halinsu.
*12:00* da sallama Jibril ya shigo d’akin da ledoji a hannunshi, Jamila dake zaune tsakiyar gadon kasa amsawa tayi dan gabanta ne taji ya tsananta fad’uwa, har saida ya zauna kusanta bata motsa ba, ganin bata da niyyar magana yasa ya aje ledojin hannunshi ya yaye mayafin nata yana kallon fuskarta, ajiyar zuciya ya sauke ya d’anyi k’asa da kanshi sannan yace “Jamila.”
Saida ta had’e yawu yafi sau biyar kafin ta amsa k’asan mak’oshi da “Na’am.”
Murmushi yayi jin firgici a cikin muryarta yace “Muje muyi alwala ko.”
Jinjina kai kawai tayi alamar to sannan ta sauko a hankali ta fad’a ban d’aki, yana zaune yana jiranta har ta fito, saida ya k’urawa fuskarta ido ganin ta wanke kwalliyar dake fuskar, mik’ewa yayi shima ya shiga, ba jimawa ya fito ya samu ta shinfid’a sallaya, gaba ya tsaya ita kuma daga gefenshi a baya suka kabbara sallah.
A wajensu Junaid ma hakance ta kasance, bayan sun idar da sallah zai janyo ledojin shi yaga ta mik’e, da mamaki yace “Zauna mana, zo ki cika cikinki Hajia ta.”
Kallonshi tayi tace “Ina zuwa, zan canza kaya ne.”
A gabanshi, yana kallo ta zage rigarta ya rage sai bras a jikinta a k’arshe ma bras d’in cireta tayi ta saka ta bacci sannan ta janye siket d’in ta, yana kallo ta cire pant d’in ta ta saka na rigar baccin, juyowa tayi ta zo ta zauna kusa da shi cikin jijjiga jiki irin na yan duniya, nan suka fara cin kazar yana bata a baki ita ma tana bashi, tun basu ida ba wasan ya sauya ya kuma girmama suka haura kan gadon mulki.
Amar ma har har sukayi sallah suka ci abinci idonsu bai had’u ba, har zuciyarshi baya son Umaimah so na soyayya, amma babu yanda zaiyi duk da yana da halin da zai iya ce ma Hajia bai sonta kuma ta amince, amma yayi hakanne saboda yan uwanshi. Yanzun haka kayan bacci ne ya sanya a d’akin shi ya dawo d’akin, tsaye ya sameta ita ma tayi shirin baccinta, k’ala bai ce mata ba ya haye gado ya kwanta, tana ganin haka ta kashe wutar d’akin ta d’auko bargo a ledarshi ta cire ta shinfid’a k’asa, ta d’auko matashin kai zata koma ya tashi zaune yana kallonta, cike da halin ko in kula yace “Kinga dawo nan ki kwanta, meye na kwanciya a k’asan kuma bayan ga gado?”
Sam bata ji dad’in yanda ya mata magana ba, haka ta taso ta d’an zauna amma bata kwanta ba, shi ma daya kwanta baccin kasa d’aukar shi yayi yana kallonta, ganin haka ba zata gyara su ba yasa shi zura mata hannunshi alamar ta taho yace “Zo k’anwata.”
Kallonshi tayi ta kalli hannun, saida ta sunkuyar da kai sannan ta mik’a mishi hannun, jawota yayi ta matso kusa dashi ya rumgumota a jikinshi, d’aya hannun yasa yana shafa kumatunta a hankali, a haka haka kuma sai bacci yayi gaba da ita, a hankali ya gyara mata kwanciyarta ya ja mata lallausan bargon dake kan gadon sannan shima ya kwanta.
A b’angaren *babban yaya* kuma nashi salon daban yake dana kowa, domin kuwa yana shigo ya hangeta tsakiyar gado ta nad’e k’afafu, tsaye yayi ya aje ledojinshi k’asa yace “…
*Alhamdulillah*
_Idan naga ruwan comment zakuji wani insha Allah._
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_35_
“Amarya haka ake tarban miji?”
Wani fad’uwar gaba taji, amma sai tayi shiru bata d’ago ba, takowa yayi saida ya tsaya kanta ya janye mayafin fuskarta, tallabo hab’arta yayi ya saka idonta cikin nashi, murmushi ya mata yace “Ai na d’auka kuka ne kike? Dana tambayeki kuka me kike?”
Sunkuyar da kanta tayi tana k’ok’arin mayar da mayafin sai kuma yace “Kinga ta so ki gani.”
Hannayenta ya kamo ta sauko daga kan gadon suna fuskantar juna, tsaye k’ik’am ya mata yace “Taimaka min na cire wannan kayan, kinsan fa ban saba saka irin wannan kayan ba, kawai dai dan yana bikina ne ina so na fito a angona.”
Kasa kallonshi tayi sai kallon k’asa da take tana shafa wuyanta da tafin hannunta, ita fa wannan tijarar tashi ce tasa take shakkar aurenshi, ya zai ce ta taimaka mishi ya cire kaya? Ba ma zai barta ta mori amarcin ba wannan, kafeta yayi da ido yace “Ke dake fa nake.”
Da sauri ta kalleshi cikin tsoro ta zura hannu saman kanshi ta d’auke mishi hular, ajeta tayi kan gado ta kalleshi kamar zata fashe da kuka tana aika mishi da kallon dan Allah ka k’yale ni haka, hannu ya d’aga kamar zai mareta yana fad’in “Dallah ni kar ki min kuka, mage kawai.”
Ja baya tayi har ta fad’a kan gadon zaune tana binshi da kallo, cire babbar rigar yayi ya cilla mata ya rufe mata fuska, janye rigar tayi ta hangeshi ya shiga ban d’aki, k’amshin rigar daya daketa ne yasa ta k’ara mannata a hanci tana shak’a tana lumshe ido, tunaninta yanda zata iya wannan bahagon yayan nata take, wani k’asaitaccen murmushi ta saki saboda ganin sam bai b’ata nuna mata k’iyayya ba, tana cikin sakin murmushin nan ya fito ba tare data sani ba dan bai rufe k’ofar duka ba lokacin daya shiga, yana sauke ido a kanta yace “Jikanyar Hajia har na fara kasheki ne? To ai baki ga komai ba, sai ma anjima ko?”
Kamar wata marar gaskiya haka ta lallab’a ta aje mishi rigar bata yarda sun had’a ido ba, matsowa yayi ya kama hannunta ta mik’e tsaye ya turata gaba yace “Je kiyi alwala ki zo muyi sallah, tunda ke ma kina da tsarki yau kwana zamuyi muna ibada.”
Juyowa tayi ta kalleshi baki bud’e, ta fara tsoratada al’amarin nashi kam, wani dolon murmushi ya mata yace “Yi sauri mana, ko so kike saina fara nuna miki komai a fili.”
K’ara k’ank’ance k’aramin bakinta tayi ta juya kamar wacce k’wai ya fashe ma cikin ciki, kamar a mafarki sai ji tayi an mareta a mazaunai, juyowa tayi da k’arfi ta kalleshi, kashe mata ido yayi yana d’an cije leb’en k’asa, da sauri ta sake juyawa ta shige ban d’aki, had’e fuska yayi kamar ba shine ke dariyar nan ba ya juyo ya d’auki sallaya yana shinfid’awa yana fad’in “Kaji min yarinya, ku mata kun d’auka ku kad’ai kuka iya kwarkwasa ko, to ni ma da nayi niyya dana zama karawi.”
Duk da ta gama alwalar amma saita kasa fitowa tana tunanin abinda zata tarar, ganin shiru yasa shi sanyo kai cikin ban d’akin, had’a ido sukayi tana tsaye gaban madubi ta jinjina a bango, ba tare daya shiga ba ya zura hannunshi ya kamota suka fito, suna zuwa ta samu hijabi ta saka suka kabbara sallah, suna kammalawa daga nan ya juyo ya fuskanceta, hannunshi ya zura ya d’an janye hijabinta daga kanta ya dafa kan nata ya karanta mata addu’a “Allahumma ini as’alukha khairuha wa khairu ba jabaltaha alaihi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi.”