BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Cikin kuka tace “Mihari (na k’oshi).”
Kawu Mamu ne ya fara magana da hausa saidai a yanayin daya iya yace “Wane abinshi jaki bata? Ke ki shaurare ni ma da kyau kiji, wannan ishkanshin nata ya kusha karewa domin kuwa aure jan mata, janje kauyen *gwadojji* na shamo mata miji kafin ta ja min abun kunya, shannan na tsawon kwana uku ban lamunshe ki bata abincin gidan nan ba, ja ta shi ashan wajen yawon ishkanshin na ta.”
Dad’i Jumma taji hakan yasa ta juya zata koma bukkarta tace mishi ” Jamwala (saida safe).”
Tana shiga bukkar ba tare da damuwa ba ta cire hijabinta ta shinfid’a k’asa ko tabarma babu ta kwanta tana kallon yaran dake kan katifa duk da dai ba wata ta kirki bace, amma a wajenta da take kwana k’asa wannan d’in kamar gado ce na alfarma, tunanin iyayenta ta shiga yi wanda suka nuna mata gata da soyayya lokacin da suke raye, amma mutuwa ta d’auke su a lokaci d’aya sakamakon had’arin daya ritsa da su na mota, wani sabon kuka ta dasa ta ci ta k’oshi hata gode Allah kafin bacci yayi gaba da ita.
*Gaga’s falimy*
*10:30* na dare Amar dake zaune a falo suna kallo shi da duka ‘yan uwan wayarshi tayi k’ara, yana dubawa ya d’auka yana fad’in “Ummy baki kwanta ba har yanzu?”
Ammar dake zaune nesa da shi kamar zaiyi kwance yana latsa wayarshi ne ya kalleshi ta gefen ido, daga wajen Ummy ta amsa mishi da “Banyi bacci ba Amar, ka ci abinci ne?”
Amsawa yayi da “Ban ci ba Ummy, bana jin yunwa ne.”
“A’a ban yarda ba, maza ka shigo ka samu wani abu ko marar nauyi ne ka ci, kai baka tausayin kanka ne da halin da kake ciki? To ka zo yanzu ina jiranka.”
Kashe wayar tayi shi kuma ya mik’e a gajiye yana fad’in “Ummy sai kace wani yaron goye, ni ba yunwa nake ji ba.”
Junaid ne yace “To ina laifin Ummy, kulawa fa akace yabawa, ta damu da kai ne shiyasa.”
Wani dogon tsaki Ammar yaja ya mik’e a hassale ya shige d’akin shi ya mayar da k’ofar ya rufe, da kallo suka bishi sai dai babu wanda ya damu bare yayi tunanin abinda yasa yayi hakan, fita Amar yayi a farfajiya ya had’u da Jibril ya dawo a matuk’ar gajiye, gaisawa sukayi kafin shi ya wuce babban falo shi kuma nasu falon.
Ammar na shiga cilli yayi da wayarshi kan gado ya fad’a ban d’aki, ba jimawa ya fito ya watsa ruwa ya kashe wutar d’akin ya kwanta daga shi sai gajeran wando, kifa kanshi yayi tsakiyar pilow yana k’ok’arin ya cire damuwar nan a ranshi, baya so abun ya dinga damunshi amma ya zaiyi mutum ne shi mai zuciya da jini, jin baccin na neman gagararshi yasa ya mik’e ya b’allo maganin bacci, a k’a’ida damuwarshi bata kai yasha guda d’aya ba, rabi ya kamata yasha, amma saboda haushi yasa yasha guda d’aya sannan ya kwanta, ai kuwa baifi minti sha biyar ba kwana ya d’auke shi marar dad’i sai dai mai k’arfi.
*Washe gari*
Kamar ibada yau ma hakane a wurin Zeituna, tana yin sallah asuba ta shiga d’ebo ruwa a panpo, layin data tarar yasa har gari yayi haske kafin ta samu ta turo kurar ruwan mai d’aukar jarka (bidon) takwas, da kanta ta dinga saukewa tana shigar da su tana juyewa a randa da tuluna da manyan bokitai, saida ta gama cas sannan tayi wanke wanke, data wanke ne ta samu ta d’ora d’umamen tuwon masara wanda miyar kukar taji daddawa, kafin yayi zafi ta gama sharar tsakar gidan, tana idawa ta zubawa duk wanda tasan tana zuba ma ta kai musu, tana dawowa babbar buta ta d’auka ta fara d’iban ruwa dan tayi wanka, amma Jumma na gani ta fito tace “Me ja kiyi da wannan ruwan?”
Cikin marairaicewa tace “Inna wanka nake so nayi , kinga fa yau kwana hud’u kenan baki barni nayi wanka ba, har Hajia ta fara min magana akan k’azantar jiki na.”
Fizge butar tayi ta juye mata ruwan a jikinta tace “Ba ja kiyi ba, na ce ba zakiyi wankan ba marar mutunci kawai, ki wuce ki tafi hakanan in kuna son zuwa kafin nasa kawunki ya dakatar dake.”
Cikin muryar kuka tace “Dan Allah Inna to ki bari na ci abinci saina tafi.”
Da k’arfi tace “Abinci? Har abincinki ma kika fitar? To kiji da kyau jiya kawunki yace kar na sake baki abinci har na kwana uku, dan haka ki wuce ma karki wahalar da kanki.”
Takawa ta fara yi cikin fitar da hawaye tana matse hijabinta wanda dattinshi yasa take sanyashi a birkice, yanzu gashi ruwan data zuba mata yasa duk wani tsohon datti da wari ya taso, ita kanta sai take jin k’yank’yamin kanta, tana zuwa ta ja kurar ruwan dake k’ofar gidan ta nufi wajen aikinta da ita, saboda tafiyar dake akwai dama yasa ta fad’awa mai kurar zata dinga kawo mishi in zata je wurin aiki, tana tafiya tana share k’walla harta isa ta aje kurar ta wuce.
*Babban gida*
Tunda asuba da sukayi sallah basu kwanta ba, yaran dama duk matasa ne suna iya shirya kansu, dan haka kowa yayi shirin zuwa islamiyya, iyayen ma shirywa sukayi sai Hamna, Amna da Jamila da kuma Umaima, zuwa k’arfe bakwai suka gama kintsawa tare da cika cikinsu, nan fa aka fito dan tafiya gayya guda, masha Allah mota shida sukayi idan aka had’a data tsaron colonel suka cika takwas, a hakan ma wai dan Amar da Ammar da su Junaid sunce sai bayan azahar zasu tafi, motar Jibril aka ce yan matan su shiga, Umaima ce ta shiga gaba tana ta wani basarwa kamar dai Hajia kakarta, Amna ce ta kama murfin mazaunin baya zata bud’e yace “Tsaya.”
Tsayawa tayi tana kallonshi shi kuma ya lek’o yace wa Umaima “Malama fita ki koma baya akwai mai wannan wurin.”
Cike da gadara tace “Wa fa?”
Had’e fuska yayi yace “Ban sani ba, ki fito na ce ko.”
Tsaki tayi ta fito saida ta bangaji Amna kafin ta shiga ta rufe tana kallo ta ga wa zai shiga gaba, kallon Amna yayi yace “Shiga nan.”
Yana fad’a ya shiga ya tayar hakan yasa Amna shiga ita ma ta rufe, sahu ya shiga da motar inda aka bud’e musu k’ofa suka fara fita, Umaima ce tace “Yanzu dan rainin hankali dama Amna ce zata shiga gaba kasa na fito daga nan? Lallai ma yah Jibril ba ka da mutumci wallahi.”
Juyowa yayi kai tsaye kuma ya kalli gabanshi yace “Qur’ani in ban sauke ki ba kice d’an iska ne ni, ke ni zaki kira marar mutumci, kaji min shegiya kai.”
*Fad’an na yau kuma tsakanin mace da namiji ne*
Nuna shi tayi da yatsa tace “Allah kar ka sake sheganta ni, inba haka zan maka tijara a wurin nan, kuma da kake cewa ka sauke ni, ka jima baka sauke nin ba, ko kai baka ga duk motocin dake gabanmu da bayanmu na gidansu ubana bane.”
Cikin tashin hankali yace “Na gode Allah da yasa akwai motar ubana a ciki, na kuma yi farin ciki daya zama ubana ba matalauci bane bare ace yana zaman kawai ne a gidan na ku, kuma Allah kika sake min magana sai na ci uwarki a cikin motar nan naga abinda zai faru.”
Hamna dake latsa wayarta cike da damuwa tace “Kai, wallahi wata rayuwar ma batayi ba, ku yanzu da girmanku zaku tsaya kuna wannan musayar yawun haka, a cikin maganganunku fa harda gori kuke son ku shigo da shi, yanzu idan ace iyayenmu suka ji kuna tunanin zasu ji dad’i ne?”
Umaima ce tace “Ke bana son iskanci, kar yau dan kun ganni na had’a kafad’a daku yasa kuyi tunanin raina ni, tom.”
Cikin jin hushi ta ture Jamila dake tsakiyarsu wanda hakan yasa har Hamna saida ta kaiwa glas d’in motar karo, ita ma cike da tsiwa ta bangazo Jamila har ita da ake cutawa tace ” A’a kai, ni kuma mena muku? Kunga kuyi fad’an ku amma kar ku saka dani.”