BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin rashin karsashi yace “Mu kan mu abun ya bamu mamaki, dan abune da bai cika faruwa ba gaskiya…”

Katseshi yayi da cewa “Me ye abunyi yanzu?”

Cikin girgiza kai yace “A gaskiya yanayin jikinta ma ba zai bayar da damar da za’a fara mata dialyse ba, dan kaga tana jin jiki sosai kuma kowane dialyse zatayi perdre d’in 10 kg, dan haka ina ga mu…”

Da k’arfi ya mik’e tsaye yana fad’in “Dan haka ayi me? A barta ta mutu kenan? Haka kake so ka ce?”

Girgiza kai yayi yace “Non docteur, amm…”

Cikin daka masa tsawa yace “Kaga fad’a min mafita kawai, ina so ka fad’a min abinda zanyi matata ta samu lafiya, bana son ganinta a halin da take cikin nan.”

Shi dai yana so su rabu lafiya dashi sai kawai ya rubuta masa magaunguna yace ya siyo, da gudu ya fita kamar wanda yasha giya dan har yanzu kanshi mugun sara masa yake.

*Kwanansu* biyu a asibiti, abubuwa sun k’ara dagulewa, tun safiyar yau da Ammar ya shigo d’akin ta fara masa nasiha ya rage zuciya ya dinga hak’uri ya kula da yara waye waye, sai kawai zuciyarsa ta karye ya fita daga d’akin, Allah ya sani har zuciyarshi yana son Amna kuma yana son zama da ita, amma baisan wacce k’addara ce ke shirin raba shi da ita ba, baisan ilimin dake cikin rashin lafiyarta ba, tunda ya fita ya zauna cikin masallacin asibitin bai sake tashi daga nan ba, yanda ya ga safiya a cikin shi haka ya riski rana da dare.

Al’amarin bai sake tashin hankalin kowa ba saida ta nemi a kawo mata yaranta, daga kwance haka take shafar kawunansu tana musu murmushi, Ameera da tafi kowanensu shak’uwa da ita ce ta kwanta kan jikinta tana kuka, Ameer ne ya jayeta daga jikinta yana fad’in “Ke baki gani bata da lafiya.”

Fizge hannunta tayi ta sake kwantawa kan jikinta, Ummy dake tsaye kusansu ne ta kalli Hamna dake tsaye ita ta kawosu tana hawaye, hannun Ameera ta kama cikin muryar kuka tace “Beby na zo mu je ko? Zaki sha ice cream?”

Mak’ale kafad’a tayi tace “Um um.”

Saida ta share hawayenta ta sake kamota tace “Muje kinji har da madara zan siya miki.”

Duk da bata saki jikinta ba haka ta bi Hamna zasu fita, cikin muryar da bata fito sosai ba Amna tacej “Yer uwa.”

Juyowa tayi tana kallonta ta tako a hankali ta zo ta tsaya, hannu ta mik’a mata ita ma ta zuro mata na ta hannun ta rik’e gam, murmushi ta saki mai kyawun gaske tace “Karki manta dani kinji, ki ci gaba da min addu’a, ke da yah Ammar zaku kula min da yarana, nasan da haka ban da matsala, karki rabu dasu duk wuya, yah Ammar zai shiga damuwar rashi na, ki…kkk…kw…”

Ganin ta kasa fad’ar kalmar kuma ita kuka ya ci k’arfinta yasa ta fizge hannunta da k’arfi ta tashi a guje ta fita, bata tsaya ba saida ta kai k’ofar asibitin ta durk’ushe nan tana kuka da iya k’arfinta.

Ko da ta fita Amna ta kalli inda Hajia take ta mata alamar ta zo, matsowa Hajia tayi tana kuka ta rik’e hannunta tace “Amna dan Allah kiyi ta addu’a, insha Allahu zaki tashi kinji.”

Sakin hannun Hajia tayi ta kalli inda Hadiza ke tsaye wacce ta zo da taji jikin ya k’i kyau, ita ma alamar ta zo ta mata ta rik’e hannunta, magana take yi amma bata jin komai, a hankali ta durk’usa ta kai kunnenta kusan bakinta, cikin sanyin muryar da bata fita tace “Mama, ki yafe min, ki yafe min, Abba ma ya yafe min, yah Ammar, ki kira min yah Ammar na rok’i gafararshi, dan Allah ki ce masa ya zo ina son ganinshi, Mama, Mama, Mama, sau uku na kira sunanki ko? Dan Allah ki ce Hamna ta zauna tare da yah Ammar da kuma yara na, zata iya kula dasu kamar yanda nake yi, dan Allah Mama, kinji, kinji ko.”

D’agowa tayi tace “Na ji Amna, kiyi ta kalmar shahada a bakinki, bari na kira miki Ammar d’in.”

Tashi tayi da sauri ta fita, amma tana fitowa ita ma ta tsaya cikin wani d’aki da babu kowa ta shiga rera kuka, ta d’auki kusan minti ashirin tana kuka kafin ta fita ta same shi zaune ya had’a kai da gwiwa, da sauri tace “Ammar, ka zo dan Allah Amna tana son ganinka.”

Tasowa yayi daga cikin masallacin ya matso kusanta cikin layi na galabaita yace “Mama dan Allah ku rabu da ita, zafin ciwo ne ke damunta kawai.”

“A’a Ammar, ka zo kawai tunda tace tana buk’atar ganinka.”

Cike da kasala yace “Shikenan muje.”

Juyawa tayi ya saka takalminsa ya bi bayanta, ji yake gabanshi na tsananta fad’uwa, ko da suka isa d’akin suka ji ana ta kalmar shahada da kabbara, babbar kalmar data daki zuciyarsa ita ce ta”Allah yasa anyi sa’ar tafiya.”

Suna shiga tare suka ganta ruf, da d’aya d’aya ya shiga kallon mutanen d’akin, yanayin kowa da furucin bakunansu ya tabbatar masa da abinda zuciyarsa ke raya masa, wani tartsatsi yaji daga kanshi har zuwa k’afarshi, kamar wani ne ya turashi sai ganinshi sukayi ya fad’i warwasss…

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_64_

Da sauri Ummy tayi kanshi ta durk’usa tana duba shi, mik’ewa tayi da sauri zata fita daga d’akin saiga Amar da Jibril sun shigo da sallama, da sauri ta kallesu tace “Yawwa ku kama shi dan Allah, ina zuwa.”

Fita tayi daga d’akins
su kuma suka tallabe shi suka fito dashi, a wani d’akin aka kwantar da shi Ummy duk ta rikice sai wasu likitocin ne suka diba shi suka saka masa ruwa.

*Allah mai girma*, jinjiga, girgiza, d’imuwa da zautuwa babu wanda baiyi ba, Amna dai ta tafi gidanta na gaskiya cikin sa’a, duk wanda ke d’akin a lokacin ya shida tayi kalmar shahada a matsayin kalmarta ta k’arshe a duniya, an ci kuka har an gode Allah kamar babu gobe, wasu suna son suyi dauriya amma da an kalli yaranta uwa uba Ameera sai a saka wani sabon kuka.

Hamna na zaune kan dakalin dake fuskantar cikin asibitin su Zeituna suka fito jiki a mace kowa na ta sharar hawaye, da mamaki ta taso ta tare su cikin dakusashiyar murya tace “Aunty kuma ta saka ku kuka ko? Ni bansan me yasa take haka ba, amma yanzu ya jikin nata?”

Kallon juna sukayi sai Hajia da tace “Jikin Amna yayi sauk’i Hamna.”

Murmushi tayi tace “Taji sauk’i kenan Hajia?”

Sake kallon juna sukayi suka mata shiru, kallon kowane take da alamar tambaya tace “Lafiya? Wani abu ya faru ne?”

Zeinabu ce tayi k’arfin halin cewa “Hamna ciwon Amna dai ya k’are daga yau.”

Kallonta take kamar irin bata gane komai a abinda take fad’a, suma duk ido suka tsura mata suga me zai faru, kusan minti d’aya tayi a haka kafin ta fara jinjina kanta, lokacin data motsa sassan jikinta ne kad’ai ta fahimci wasu sabbin hawaye masu zafi dake gangaro mata, nuna kanta tayi da yatsa kamar mai koyon magana tace “Am…na, ye..r uwata, me ya sameta?”

Hajia ce ta dafata cikin ban baki tace “Sai hak’uri Hamna, haka Allah ya so, addu’a zaki mata kinji.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected