BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Junaid na barin nan wajen masoyiyarshi ya nufa inda yasan zai iya ganinta, tun daga wajen masallacin ustaz Sani d’an jatau yake baza ido amma shiru harya k’arasa bakin *pacific*, wani lungu ya shiga da motar dan yasan suna zama nan ita da k’awar ta, amma rashin sa’a bai samu ganin ko d’aya daga ciki ba, kiran wayar k’awarta yayi dan Maryama bata d’aukan kiranshi tana ganin kamar yana takura mata, a lokacin sun fito daga cikin d’akinsu tana rufewa da d’an kwad’o kiran ya shigo, k’awar mai sunan *Iklima* ce ta kalleta tace “Mutuminki ne fa Mari, me zan ce mishi idan na d’auka?”

Masha Allah, tabbas Maryama mai kyau ce ta gidan gaba, ga ta doguwa sosai da d’an kumari, gashi fatarta jawur da ita duk da tana shafa mai amma kasan ita ma akwai asalin farinta, akan luma-luma kumatunta kuma wasu tsage ne suka k’awata fuskar har guda bibbiyu, a take tace “Kawai ki fad’a masa bama tare dake, kar ma ki fad’a masa na fita.”

Zata d’auka kiran ya tsinke kuma sai baiyi gaggawar maidowa ba, hanyar gidansu ya nufo wanda ke bayan masallacin daya bari a farko, yana sake kira kuma Iklima ta d’auka tace “Barka da dare.”

“Barka Hajia Iklima, ya kike?” Cikin sakin fuska ta amsa da “Lafiya lau, ya yau?”

Saida ya sauke ajiyar zuciya yace “Yau da dama, ina mutuniyar take? Nasan kema kinsan bata d’aukar kirana.”

Kallon Maryama tayi suna kan hanyar fitowa daga gida, kewayen wata mata Maryama ta lek’a ta same su zaune a d’an filin wurin suna kallon telbijin, matar ce ta kallesu tace “Mari fita zakiyi ne?”

“Eh maman *Husna*, ina *Huda* take ne?”

Da sauri wata yarinya da ba zata wuce shekaru biyar zuwa shida ba ta mik’e tsaye ta tunkarota, tana suwa ta rik’e hannunta tace “Mamma, yau ma fita zakiyi?”

Da murmushi ta shafa fuskarta tace “Fita zanyi Huda, amma yau ba zan jima ba zan dawo kinji.”

Marairaicewa tayi ta k’ara matse hannunta tace “Mamma kullum haka kike cewa ba zaki jima ba, me ya sa ba zakiyi zamanki a gida ba?”

Ba annuri a fuskarta tace “Saboda saina fita muke samu mu ci abinci.” Hannu tasa a jakarta ta fito da dala ashirin (ba zasu gaza naira ashirin ba), bata tayi tace “Gashi kije Aminu ki siyo madara kisha, idan kinji bacci kije lungunmu ki kwanta nayi shinfid’a.”

Juyawa tayi zata fita taji ta rik’e hannunta, tana juyowa yarinyar tace “Mamma meyasa ke saida dare kike nemo mana abinci? Ki dinga zuwa da rana mana tunda baki komai a wannan lokacin.”

A hankali ta zage hannunta daga na yarinyar ta sake juyawa, kamar saukar ruwan sama ta tsinci muryar Huda na cewa “Mamma kenan da gaske ke ‘yar iska ce?”

Tsayawa tayi amma bata iya juyowa ba saboda hawayen da take, Iklima na ganin haka ta fice ta barta, da sauri ta taka ta barta nan ta fita, amma saboda wayo da kuma k’uruciya sai yarinyar ta fito da gudu har k’ofar gida tana kuka cikin d’aga murya tace “Ashe dama ban da uba, ni shegiya ce, to ni dai bana son neman abincin naki hakanan, daga yau ba zan sake cin abincinki ba idan kin kawo, kije kawai karma ki…”

Marin da Maryama ta d’auke ta dashi yasa yarinyar fad’uwa k’asa, wani daga cikin masu zama a k’ofar gidan ne ya kama Huda ya d’auke ta yana rarrashi.

Iklima dake amsa wayar Junaid shi kuma a daidai lokacin ya k’araso k’ofar gidan, cikin rashin sani tace “Mari ai tun rana rabona da ita dana barota gida, izuwa yanzu kuma nasan ta yada zango a wani wurin.”

Daga inda yake ya hango fitowarta sai Maryama dake bayanta, daga cikin wayar yayi murmushi yace “…

*Allah ka mana kyakyawan k’arshe.*
18/05/2020 à 13:46 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

_Bismillahir rahamanir rahim_

_2_

Daga cikin wayar yayi murmushi yace “Karki damu ma naga hasken idaniyar tawa.”

Da sauri ta d’auke wayar daga kunne ta juya hagu bata ganshi, tana juyawa dama ta hangoshi yana fitowa daga motar, a hankali ta fara takawa wajen shi sai Maryama dake biye da ita a baya wacce bata san meke faruwa ba, saida taga Iklima ta tsaya wajenshi kad’ai ta fahimci mayenta ne ya sake dawowa, tsaki tayi ta tafi a harzuk’e zata wucesu kamar bata gansu ba ma, da sauri ya tare gabanta da gudu gudu, kallon juna sukayi kafin tace “Malam matsa min a hanya ko.”

Kai ya girgiza duk yayi kalar tausayi yace “Ba zan iya ba Maryama.”

Tab’e baki tayi tace “To saika zauna kayi gadin wurin ko, ai shi zaka iya na sani dan kamar kaine ka yankewa wahala cibiya lokacin da ta zo duniya.”

Murmushi yayi dan kalaman da suka fi wannan ma ya jisu a bakinta, zata rab’a ta wuceshi ya sake tare gabanta yace “Dan Allah Maryama ki saurare ni, wai me ya sa har yanzu idonki sun kasa gane miki masoyinki na gaskiya ne? Maryama me ya sa ba zaki yarda da soyayyar da nake miki ba?”

Da k’arfi tace “Saboda duk maza halinku d’aya ne, kana son samun soyayyata ne saboda kawai kana son jikina, kuma na fad’a maka ni yanzu a ruwa nake, karuwa ce ni, ba buk’atar saika yaudareni kafin ka samu jikina, 2000f cfa (jaka biyu) kad’ai ka bani zan iya kwana tare da kai, saboda ni k’aramar karuwa ce da aka cewa *je ki kya gani*, abinci kawai nake nema da zan ciyar da kaina da kuma ‘yata, tunda muma halitta ce ba zamu iya rayuwa babu abinci ba, amma kai ka tsaya sai wahalar da kanka kane kana b’ata min lokacin da rera min wani banzan wak’anka wai kana so na, mtssss.”

Tunda ta fara magana ya saki baki yana kallon nata k’aramin bakin, har k’asan zuciyarshi tana birgeshi, yana son kallon kyakyawar fuskarta mai d’auke da tsagu har hud’u, wanda kowane kunci ya samu bibbiyu, amma ta kasa fahimtarshi har yanzu, wani murmushi yayi mai kama da ciwo yace “Yanzu akan jaka biyu kad’ai Maryama kike wofantar da kanki ga mazan da basu san ciwon kansu ba? Maryama akan kud’in da ba zasu iya siya miki ko zanin atamfa ba kike kwanciya da duk d’a namijin daya miki magana? Maryama taya zaki illatar da kanki da gangan alhalin kinsan ba kya da kud’in warakar matsalarki ba?”

Hannayenshi yasa aljihu ya lalaba ya fito da duka kud’in dake cikin ak’alla sun ba jaka d’ari biyu baya ya janyo hannunta ya damk’a mata kud’in a hannu kamar zaiyi kuka yace “Karb’i wannan kiyi duk buk’atunki iya na yau kawai, ni kuma na miki alk’awari kowace safiya zan kawo miki adadin wannan kud’in dan biyan buk’atar ki kawai data ‘yarki, amma ki min alk’awarin babu ke babu sake kula wani namijin, ki bani tabbacin zaki kula min da kanki za kuma tsare min mutumcinki, dan Allah Maryama.”

A hankali ta raba hannunta da nashi ta sakar masa kud’in a hannunsa tana kallon cikin idonshi tace ” Bana buk’atar taimako daga wajen kowa, zanyi aiki da jikina wajen samo mana halak d’in da zamu ci, amma bana son kud’in ka, kad’an d’in da nake samu sunfi min masu yawan da zasu fito a hannun kowane d’a namiji.”

“D’a namiji! D’a namiji! Maryama kullum maganarki kenan d’a namiji, wai wace irin ta’sa namiji yayi miki haka da har kika mana kud’in goro haka? Ki fad’a min ni kuma zan tsaya tsayin daka wajen ganin na goge waccen bak’in fantin da waccen mutumin yayi mana, sannan ki bar tunanin halak kike ci ke da yarki, kud’i ne da kika samu ta hanyar sab’awa ubangiji.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected