BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk da shekaru sunja kuma ta tsufa, amma babu abinda ya hanashi ganeta, sunkuyar da kai yayi da alamar rashin gaskiya tare da cire hular kanshi ya fara firfita da hannun babbar rigarshi, Alhaji ne ya kalleta yace “Husseina, kin sanshi ne dama?”

Labaran dake cikin mota zaune fitowa yayi ya zo ya tsaya gabansu ya k’ura musu ido, ita ma duk’ar da kai tayi ta fashe da kuka, Labaran ne ya sake matsawa cikin tashin hankali yace “Hajia lafiya kike kuka? Meya faru?”

Fad’awa tayi jikin Labaran hakan ya sashi shafata yana daddab’ata alamar rarrashi, Hassana ce ta sake cewa “Husseina wai meke faruwa?”

Da k’yar malam Rabi’u ya d’ago cikin i’ina yace “Ee.h to..ina ga dai.. ko bata da lafiya ne?”

D’agowa tayi ta kalleshi tace “Banda lafiya? Me zai hana ka fad’a musu abinda ya faru.”

Alhaji ne yace “Wai me yake faruwa ne? Ku fad’a mana.”

Cikin tsananta kuka ta kalli Alhaji tace Ba komai, kawai mu tafi.”

Labaran daya kafe malam da ido shi dama har yanzu al’amarin mutumin na gindayar dashi yace “Hajia daga ganin mutumin nan yanayinki ya canza, dan Allah ki fad’a mana ko da wani abu mana ko hankalinmu zai kwanta.”

Juyawa malam Rabi’u yayi da nufin barin wurin sai Labaran yace “Hajia ko dai wannan shine…” Shiru yayi bai k’arasa ba dan da k’arfi malam Rabi’u ya juyo yana kallonshi, ita ma Husseina kallonshi tayi, sai Hassana ce tace “Shine me?”

Cike da ladabi yace “Hajia kwanan baya sanadiyar ganinshi yasa na miki tambaya akan mahaifina, jikina yana bani kamar akwai wani abu tsakanina da shi, kuma alak’ar zata iya zama mai k’arfin gaske, amma gudun b’acin ranki yasa bana iya aiwatar da komai.”

Duk shiru sukayi sai Husseina data share hawaye ta kalli Labaran tace “Tabbas shine, ba zan tab’a manta kamanninshi ba.”

Hassana da Alhaji ne suka ce “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.” Alhaji ne ya d’ora da “Ya ilahi, malam Rabi’u?”

Husseina shigewa tayi mota ba tare data kalli kowa ba, Hassana ma shiga tayi tana waigen malam, Labaran dake kallonshi rasa abinyi yayi, sai kawai ya juya shima ya shiga mota ya tayar, Alhaji ne yayi k’arfin halin matsawa kusa dashi yana kallon idonshi yace “…

*Alhamdulillah*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_34_

“Gaskiya banyi tsammanin haka ba, sam abun baiyi min dad’i ba, cikar kamalarka tasa ban tab’a maka wannan zaton ba, tashin hankalin daka jefamu cikinshi Allah kad’ai yasan iyakarsa, amma yanzu a matsayinmu na manya ba zamu ce da kai bamu yafe maka ba, domin kuwa bayyana da kuma tonuwar lamarin nan a yanzu bayan tarin shekarun da aka kwashe ya isa yasa mu fahimci akwai wani al’amari mai girma, kuma gashi a bayyane auren *Maryama* da Junaid yayi, sai mu musu fatan alkairi.”

Yana gama fad’a ya wuce shima inda colonel da kanshi ya bud’e mishi mota ya shiga suka wuce. Husseina na zuwa gida d’akinta ta wuce ta dinga kuka, sam bata so had’uwar ta da shi ba, amma gashi yau ta gani, haka farin cikinta ya koma bak’in ciki, haka shima Labaran, kana ganinshi zaka gane yana cikin damuwa, sai dai shi har zuciya yana so ya gana da mahaifinshi, *uba*, wanda ya rasa tsawon shekaru, bai tab’a d’ora idonshi akan ko da dangin ubanshi ba bare uban. Kamar yanda baya b’oyewa Soueiba komai yanzun ma bai b’oye mata ba, ita kanta abun ya d’an dameta sai dai bai hanata karb’an duk wani daya zo gidan dominta ba.

Tako kamar na gwiwa, d’aya bayan d’aya sai kace wata sarauniya, yayin da mai aikinta ke biye da ita a baya rik’e da jakarta, babbar riga ce jikinta mai kama da babbar rigar maza, d’aurin d’an kwalin ya hau kanta sosai, sai yalolon gyalen data d’ora a kafad’a d’aya da manyan waya har biyu a hannuwanta, zobuna da sark’a da yan kunnai duk gwal ne, dogayen takalma a k’afarta da suka dace da kalar kayan, da gani babu tambaya kasan mai yana aiki a wurin, jan nata har ya k’azamce ta yanda take d’aukar ido, ga kuma hodar data d’auka ta k’ara fito da ita, cike da k’asaita da jin kai da isa ta k’arasa tsakiyar filin da ake kad’in guitar. Yau a k’ofar gida ne ake kad’a guitar d’in sai tarin yan zaman biki da suka zagaye mawak’an suna kallon rawar da wasu maza keyi irin ta buzaye, bayan k’arar guitar haka wurin ya hargitse da shewa irin ta buzaye (ma Sajida nasan zaki fahimci irin shewar, ) wasu na karkad’a harshe abun birgewa ana rawa wacce tafi kama da tsalle tsalle, dan wani tsallen sai anyi k’asa sosai ake yin sama ana harba k’afafu (abun birgewa). Zuwan *Aissata* yayi daidai da zuwansu Ammar shi da abokanshi wanda suka zo d’aukar abincin da yasa Zeituna ta girka mishi, zai shiga gidan Sayyada yar Fatime da kuma wasu daga cikin yan mata suka taho wurinshi, nan suka tilasta mishi sai sun d’auki hoto dashi, sun d’auki hoton zai shiga sai kuma ya kalli wurin taron, nan ya hangi Aissata ta bud’e bakin jaka tana watsa kud’i kamar hauka, murmushin zaki gane kurenki yayi mata ya nufeta, nan ya kutsa filin taron ya sameta yana murmushi yace “Uwarmu sannu da k’ok’ari.”

Kallonshi tayi a sama tace “Cava.”

Kallon mai bisa ruwa ya mata yace “Uwa irin wannan lik’i haka, kice dai aljihun uban namu yayi kuka yau?”

A wani yamutse ta kalleshi tace “Qu’est ce que tu remarque (Me ka lura dashi)?”

Murmushi ya mata yace “Eh to, da yake ai a lokacin aurenku da tonton munje Niamey, kuma har gidanku muje kafin ma d’aurin auren, in baki manta ba ai har d’akin Ummynki na shiga na ci abinci.”

Kallonshi tayi da alamar rashin fahimtar zancenshi ko d’aya, hakan yasa tace “De quoi tu parles? (Akan me kake magana), je ne comprends rien (Ban gane komai ba).”

_Hyahyahya, bata gane komai ba, yana nufin ya ga gidanku ke d’in ba yar kowa bace bare ace zaki iya fantamawa da kud’in gidanku._

Murmushi ya mata ya k’urawa fuskarta ido yace “Amma uwarmu powder nan fa ta karb’i fuskarki, wallahi yanda kika san wata kyakyawar sarauniya.”

Dariya ya mata ya wuce cikin gidan, ganin babu isassar hanyar da zai wuce yasa shi tambayar *Farisa* k’anwar Jibril inda uwa Zeituna take, ita ta fad’a mishi suna gidan da za akai amare suna girki, da mamaki ya kalleta yace “Gidan da za akai amare? Wane gidan to? Bayan kowa da nashi gidan, Ina ne gidan?”

Nuna mishi gidan nan tayi tace “Yah Ammar gaya nan, yanzu ma ana kai kayansu ne ana gyaran d’aki.”

Jim yayi alamar tunani, murmushi ya saki yace “Duk yanda akayi wannan aikin Alhaji ne, dan shine kad’ai yake matuk’ar son ya ga iyalinshi a wuri d’aya, baya son ganin sunyi nesa da juna, shiyasa duk da kowa na da hali amma suke manne gida d’aya.” Kallon Farisa yayi yace “Je ki kira min ita.”

Galala ta kalleshi jin yace wai ta kira mishi ita, Zeituna fa yake nufi, wucewa tayi shi kuma ya fito dan ya jirata a waje, sai dai yana tunanin yanda zasuyi rayuwar aurensu a kusa da iyayensu, a gaskiya ya so ya bar gidan nan ko ya samu salama, amma kuma ba zai iya yi wa Alhaji musu ba, yana cikin tunanin nan Zeituna ta fito cikin shirinta sai dai duk ta had’a gumi saboda aikin da suke, girki ya tambayeta tace an ida dan haka yasa aka fito da manyan kuloli aka zuba musu, su Amar na zaune a k’ofar gida suma suna nasu casun, sai dai ko magana bata had’a shi da ko d’aya daga cikinsu ba, sai Junaid wanda tuni wasu daga cikin dangin Alhaji da kuma dangin Soueiba suka tafi d’aukar amaryarshi Goûré tare da abokanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected