BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallonshi kawai tayi da ido, wanda ya kamata ya kira Appa shi ya kira da yaya, wanda ke mazaunin kakanshi kuma ya kira da Appa, wannan wace irin *BADAK’ALA* ce? Cikin tunani bata san ta fara tafiya ba saida taji ya rik’e hannunta yana fad’in “Aunty ina zaki je? Ina zuwa.”

Kallonshi tayi tace “To muje mu siyowa sabon bebynmu kaya ko.”

Da gudu ya rigata k’arasawa wajen motar, bud’ewa tayi ta shigar dashi sannan ta shiga, mai gadi na bud’e mata k’ofar anan ta ganshi tsaye tare da Abba da Labaran, sauke gilashin tayi tare “Abba barkanku.”

“Ina zaki je?” Ita ce tambayar daya jefo mata, cikin ladabi tace “Ummy ce ta aike ni na siyowa bébé kayan sanyi, amma yanzu mun dawo dan tace akwai hadari a gari.”

Cikin sakin fuska yace “Shikenan sai kin dawo.”

Kallon Shureim yayi yace “Hein ba magana?”

Ammar kawai ya kalla yace “Yaya na tafi.”

Murmushi ya masa yace “Saika dawo, ka kula da kanka.”

Wucewa tayi suka d’auki hanya, sun bar nan kenan Amie ta zo yin barka, gaishesu tayi suka amsa ta tambayi Ammar ya mai jiki da bébé, cikin amon muryar da yake nuna babu wasa ya amsa mata, ciki ta shiga kai tsaye b’angare Amna ta nufa, nan ta samu Ummy suka gaisa, saida suka gama gaisawa fa Amna sannan tace “Ummy ina Hamna take?”

Cikin sakin fuska tace “Hamna ko bata jima da fita ba, amma yanzu zata dawo nasan ba zata kai ko kasuwa ba.”

Hira suka fara tab’awa da Amna sai Ummy data bar musu falon, ba jimawa da fitar Ummy kuma Hamna ta dawo, Zeituna ta ci karo da ita saita fad’a mata yanzu Ummy ta shiga ciki, dan haka saita shiga kawai inda Shureim ke mata rigimar ta koma yawo dashi, kai tsaye d’akinta suka shiga ta same ta tana duba wasu kaya, kallonta tayi tace “Har kun dawo wai?”

“Wallahi Ummy, kinga kayan.” Ta fad’a tana mik’a mata ledar, bud’ewa tayi tana dubawa sai Shureim dake kamo hannunta da k’arfi yana fad’in “Ki bani ni, ki bani.”

Umly ce ta kalleshi tace “Wai me za’a baka?”

Dan kar Ummy ta dakeshi yasa Hamna sakar masa makullin, yana jin ta sake masa saiya fita a guje ta bishi da kallo, tana juyowa suka had’a da Ummy dake murmushi, cikin taushin murya tace “Ki k’ara hak’uri Hamna, insha Allahu komai ya kusa zuwa k’arshe, tunda a
mahaifin yaron nan ya canza al’amuran gidan nake son fad’a ma Hajia, matsalar d’aya ita ce ta yanda zan fara fad’a, amma nasan ko da na fad’a rai ba zai b’ace ba kamar zamanin baya.”

Cike da damuwa Hamna ta kalleta tace “Ummy ni kaina tsoro nake ji, wallahi kullum tunanin al’amarin gigita k’walwata yake, duk da yanzu dai abubuwa sun canza, amma muyi kallon abun ta b’angaren yer uwata da kuma Abba, Ummy ya zasu ji idan suka ji maganar nan, ya yer uwata zata kalleni taji wai Shureim d’ana ne, d’an nawa ma wanda na haifa tare da mijinta, duk da dai kafin aurensu ne amma abun akwai gigitarwa, sannan Abba da yake mishi kallon d’an shi shima ya zaiji Ummy?”

Jinjina kai Ummy tayi tace “Wallahi Hamna karki so ki tona raina kiji yanda a kowace rana nake bacci da fargaban nan, ni kaina nasan wannan abune mai matuk’ar d’aure ne, abune da ko da ya tab’a faruwa to ba dai a k’asar hausa ko kuma anan kusa ba, k’anwata Gaishata da bana b’oye ma komai, amma sai gashi wannan karan har alk’awarin fad’a mata da nayi bai cika ba, Hamna tun tana tambayata na fad’a mata har ta kai ta gaji ta daina, ni kaina bansan ta inda zan fara kawo k’arshen labarin nan da nine na fara shi ba tun farko.”

Cikin jimami tace “Kawai Ummy mu jira Amna ta samu lafiya a gama sabgar nan, kukan kura kawai zamuyi mu fad’a, in ya so ayita ta k’are kawai ko mun huta mu ma.”

Jinjina kai tayi tace “Allah ya shige mana gaba.”

Jin motsin zasu fito yasa *Amie* barin wurin da sauri wacce data mik’e zata tafi Zeituna ta fad’a mata ai Hamnar ta dawo tana wajen Ummy, tana zuwa yayi daidai da jin wannan babban sirri da ake ta b’oyo, da sauri ta koma b’angaren Amna ta zauna sai ga Hamna sun shigo, kallonsu take tana ta sak’a da warwara, sai dai ta girgiza kai kawai tayi murmushi, sai taji ma ta kasa tashi ta bar gidan, Amna da Hamna take kallo tana hasaso Ammar a idonta, lallai duk cikin lamarin Amna aka rainwa hankali, to miye abun b’oye mata ana zalintarta, kai ba zai yiwu ba wallahi, *gwara komai ya fito uban kowa yaji duk a k’one tare*, haka ta ci gaba da zama har k’arfe *09:00* dare yayi.

Mutanen d’akin sun rage daga Amna da Hamna sai Amie, sai kuma Husseina wacce suke kwana tare amma tana nesa dasu sai gyangyad’i take, Hamna ce ta tashi ita ma tace “Besty bari na fad’awa Ummy saina aje ki gida.”

“Ok besty.” Ta fad’a tana binta da kallon yar rainin hankali, saida ta ga fitarta ta gyara zama ta kalli Amna da kyau tace “Amna ke fa yanzu nan baki san komai ba ko?”

Kallonta tayi tace “Komai kamar me fa?”

Girgiza kai tayi tace “Allah sarki, gaskiya Amna ana cutarki a gidan nan, mijinki, yar uwarki da kuka fito ciki d’aya, da kuma Ummy, sun taru suna raina miki hankali.”

Duk mutanen da Amie ta ambata mutane ne da suka zama dunk’ulen rayuwarta, mutane ne masu matuk’ar mahimmanci a tattare da ita, dukansu zata iya sadaukar da rayuwarta akan su, dan haka a take taji wani haushinta da tsanarta sun dira a zuciyarta, sama da k’asa ta kalleta tace “Ni dai a sanin dana miki ban sanki da gulma da yarfe ba, bansan kuma yaushe kika koyesu ba?”

Murya k’asa k’asa tace “Amna wallahi maganar gaskiya nale fad’a miki, idan ma baki yarda ba to ki tambayesu kiji.”

A kausashe tace “Na tambaye su me Amie? Wai dama gulma kika zo ba dubiya ba? To tashi ki fita.”

Tab’e baki tayi ta mik’e tsaye ta kalleta tace “Dama ko a yan biyu akwai baud’add’e, ke kam ba zaki tab’a gane irin cutar da ake miki ba, amma idan mijin naki ya shigo ki tambayeshi waya
haifi Shureim? *Shi ko mahaifinshi*, inhar gaskiya zai fad’a zai ce miki shine, in kuma k’arya zai fad’a zai fad’a miki mahaifinshi ne.”

Juyawa tayi tana fad’in “Sai anjima.”

Zata fita Hamna ta shigo, juyawa tayi ita ma tace “Yawwa to yi sauri muje Hajia tace kar na jima.”

Cikin wata irin murya Amna tace “Dakata.”

Tsayawa sukayi suka juya suna kallonta, ba tare data tashi daga inda take ba ta kalli Hamna ido cikin ido babu yanayin wasa tace “Ki koma ciki babu inda zaki kaita.”

Da mamaki Hamna tace “Me yasa?”

“Saboda munafuka ce.” Ta fad’a kai tsaye, murmushi Hamna tayi a tunaninta jikin ne ya motsa tace “Kiyi hak’uri kinji yer uwa, ba jimawa zanyi ba yanzu zan dawo.”

Da k’arfi tace “Hamna babu inda zaki kaita, in kuma baki yarda ba to kuje ga hanyar nan.”

Kallon Amie Hamna tayi ta k’yabta mata ido alamar su mata wayo sai a zahiri da tace “Besty kawai ki tafi tunda yer uwata bata so ba zanje ba.”

Jinjina kai Amie tayi ta fita, Hamna na ganin haka ta kalli Amna tace “Akwai abinda kike so na miki ne ko ka naje na kwanta? Bacci nale ji sosai.”

Kallonta tayi tace “Kije ki kwanta saida safe.”

Juyawa tayi ta fita tana zuwa ta ja mota ta fita ta d’auki Amie, hak’uri ta bata kan abinda ya faru tace ba komai. Tana fita Amna ta bita da kallo, murmushi tayi tace “Ko yaushe Amie ta haukace kuma? Su yanzu nan mutane kallon mai hankali suke mata? Lallai ma Allah ya bata lafiya.”

Daga nan zaune ta saki wannan maganar kamar anyi rubutu a saman ruwa, jikinta ya bata Hamna ta tafi ta kai Amie gida ne, k’wafa tayi tace “Haba, kuje d’in mu gani.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected