BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tab’e baki tayi tace “Ka ci k’aniyarka ko da kai da goron.”

*Masautar Basraba*

Sarki Imran Musayyib ne zaune akan sofa wacce tasha kwalliya mai d’aukar ido da birgewa, sanye yake cikin kaya na alfarma kuma na sarauta, sai dai babu nad’i a kanshi sai hula kawai, hatta takalmin k’afar shi irin na sarauta ne masu kwalliya daga sama kuma rufaffe, sai gefenshi liman ne tare waziri suna kallonshi da girmamawa yace ” Liman kunce zakuyi magana dani mai mahimmanci, shiyasa ma na ce mu zo nan ciki saimu tattauna.”

Duk da yana sarkinsu amma suna jin dad’in yanda yake girmamasu saboda shekarunsu da kuma dad’ewarsu a fada, dan tun mahaifin Sameera na kan mulki suke tare da su har mahaifinshi ya karb’a kuma shi yanzu gashi a kai, liman ne ya kalli waziri yace “Waziri sai kayi bayani ko.”

Kallonshi waziri yayi ya kuma kalli sarki yace “Ranka shi dad’e Allah yaja zamaninka, dama magana ce data shafeka ta kuma shafi cikin gida, to mun jima muna sonyin maganar amma duba da yanda zaka d’auki maganar yasa mukayi shiru, yanzun ma mu fara jin jita-jita ne a gari da kuma labari daya zo mana daga wasu masarautun na magaganu da ake ta yad’awa akan ka, shiyasa muka ga hakk’inmu ne mu sanar da kai abinda ke faruwa.”

Wata lallausar ajiyar zuciya yayi ya kallesu a tsanake cikin fitar da kowace kalma a bakinshi yace “Liman, waziri, kar kuji komai ku fad’i abinda ke ranku, ina kallonku ne kamar iyaye na, kuna da damar sakani nayi abu ko bana so.”

Cike da jin dad’i waziri yayi murmushin gefen labb’a ya k’ara gyara zama yace “Mai martaba dama magana ce akan aure, kamar yanda kasan dokar garin basraba ta bawa mace damar yin mulki in har tana da aure, to haka ma dokar basraba ta bawa sarki damar auren mace biyu, uku, hud’u, amma mata d’aya bata dace da sarkin wannan gari mai tarin albarka ba, yanzu haka tsegumin da al’uma keyi kenan da ma wasu masarautun ana cewa sarki ya karya doka ta hanyar zama da mace d’aya har na tsewon shekara goma sha biyar, shine muka ga ba zamuyi shiru ba al’umar gari su ci gaba da tsegumi akan masarautar nan ba tare da munyi yunk’urin dak’ile matsalar ba.”

Shiru yayi kansa k’asa yana tunani akan abinda suka fad’a, tabbas gaskiya ne shi kanshi yana tunanin k’ara aure ko da zuciyarshi na son *Ameera* ne kad’ai, amma kuma ganin matsalar mata da ba’a rabasu da kishi musamman yanda suke k’azanta shi idan ance sun had’u gidan sarauta ko wani babban gida, shi shaida ne akan irin kishin da matan mahaifinshi keyi da mahaifiyarsu, duk da sun gamsu shine magajin sarki amma kuma suna bak’in ciki da hakan, kawunansu shi da yan uwanshi ba a had’e yake ba saboda yan ubanci, to wannan ne yake mishi shamaki da tunanin k’ara aure sai yaji yafi so yayi ta zama da Ameerarsa kuma sarauniyarsa, yana cikin tunanin abun fad’a musu liman yace “Ranka shi dad’e ba abu bane na ujila da muke buk’atar jin amsa daga bakinka yanzu yanzu, zamu koma mu, lokacin daka yanke shawara ma ji.”

Waziri da sam maganar liman bata masa dad’i bane ya kalleshi, tsaki yayi a cikin zuciyarshi saboda takaici, shi fa burinshi yanzu bai wuce ace ‘yarsa ta shigo gidan sarauta ba a matsayin matar sarki, kuma yayi sa’a *uwar d’aki* (mahaifiyar Imran) har yanzu bata son Ameera saboda ganin basu dace ba, shiyasa ma ta k’arfafa masa gwiwa kan su tuntub’e shi da maganar k’ara aure, ita ko ta mishi magana zai shawarci *takawa* (har yanzu suna kiran tsohon sarki da wannan sunan), kuma takawa zai bashi zab’i ne yayi idan yana so idan baya so ya bari, uwa uba kuma ‘yar uwarshi Sameera kuma mai bashi shawara akan harkokin mulki dama na cikin gida, ita kanta zata zame musu matsala, dan hakane ya taho da liman dan su mishi magana saboda yana matuk’ar ganin girman liman saboda mutum ne da babu wanda yake shakka in banda ubangijinshi, zuwansu tare ne zaisa ya yarda da duk abinda suka fad’a ya kuma gamsu, muryar sarki ce ta dawo dashi daga duniyar tunani yana fad’in “Liman na yarda da bayaninku, amma duk da haka zanyi shawara, duk abinda na yanke zaku ji.”

Da girmamawa liman ya amsa da “Allah ya shige mana gaba, Allah ya k’ara maka lafiya da nisan kwana.”

Mik’ewa yayi yana fad’in “Mun barka lafiya ranka shi dad’e.”

Mik’ewa waziri yayi yana bin bayan liman da harara, shi da ya so ayi komai a k’are yau d’in nan, amma gashi ya mishi shamaki da matsayin dake tunkaro shi, suna fita ya mik’e ya d’auki babbar alkyabarshi ya saka ba tare daya d’ora hular ta ba, cikin tako d’aid’ai ya tunkari k’ofar fita, yana isa k’ofar fadawa biyu ne tsaye suka sunkuya suna masa kirari, wucewa yayi suka take masa baya, duk da dare ya fara yi amma har yanzu ana kai da kawowa gidan, iya hangenka iya girman gidan, a haka ya isa b’angaren tsohon sarki wanda yanzu baya komai sai zaman gida da bawa mutanen gidan karatu, dan har yanzu jikinshi babu kyau tun rashin lafiyar daya kwanta sakamakon rashin sanin inda d’an uwanshi da yarshi suke, kamar yanda baya buk’atar k’yale k’yalen duniya hakan yasa ko mai gadin shiga k’ofar shi babu, Imran kuma dama kai tsaye yake shiga wajen mahaifin nashi, dan haka yanzu ma suna kawowa ya dakatar da fadawa shi kuma ya k’wank’wasa k’ofa, yaye labulen yayi dan tunda yaga k’ofar bud’e yasan zai iya shiga kai tsaye, zaune ya hango Musayyib ya tank’washe k’afafun shi da wani babban littafi a gabanshi yana karatu, yana ganinshi ya rufe littafin yana sakin murmushi da fad’in “Imaran kai ne yanzu? Zo zauna nan.” Har Imran ya zauna shima yana murmushin, saida ya gama daidaita zama kamar yanda mahaifinshi yake kafin ya kalleshi yace “Ni ne Abba, Abba na karatu ake?”

Da murmushi ya amsa da “Kamar dai kullum.”

“Allah ya k’ara maka lafiya Abba na, Allah ya k’ara maka nisan kwana.”

Murmushi yayi sosai yace “Imaran, ko yanzu na mutu Alhamdulillah, na rabu da iyayena lafiya, nayi mulkin jama’a kuma na tabbatar ban bar hawaye a idon talakana ba sai wanda ubangiji bai bani ikon saninshi ba, ina zaune da ku lafiya, to ni kuwa me zan nema a wata doguwar rayuwar?”

Ba tare da murmushi ya bar fuskar Imran ba yace “Hakane Abba, ina fatan Allah yasa na kamalta mulki irin naka.”

Shi ma da murmushin yace “Kana kamaltawa Imran, labari na zuwa min na duk abinda ke faruwa, sai dai fatan a gama lafiya a kuma tabbata a haka.”

D’an kallonshi sarki yayi yace “Abba na magane ce dani a baki na, bansan ko kuna da lokacin da zan iya fad’a muku ba?”

“Imran ka d’auka lokacin nan nawa na kane, kai ba ma wannan ba kad’ai gaba d’aya lokacin daya rage min na sauran rayuwa ta.”

Murmushi ya sake fad’ad’awa dan ko ba komai yana jin dad’in zamanshi tare da mahaifinshi, duk wata kalma da zata fito daga bakinshi mai dad’i ce, uwa uba ya kirashi da sunan Imaran, dan inba gabanshi ya zo ba baya jin wannan sunan, daga ranka shi dad’e sai mai martaba sai Allah ja zamaninka da sauransu, hakan yasa yake jin dad’i idan ya tuna a duniya akwai wanda ke kiranshi da Imran sak, dan ko mahaifiyarshi bata kiran sunanshi musamman daga lokacin da aka d’ora shi mulki zuwa yanzu, wani lokacin yana ji kamar tana sakaya sunanshi ne saboda ta tusawa abokan zamanta takaici, wani lokaci kuma kamar harda alfahari. Gyara zama yayi ya fara masa bayanin abinda su waziri suka fad’a mishi tare da cewa yana neman shawararshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected