BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yanda ya fad’a da k’arfi yasa ta rintse ido, kallon Hajia yayi yace “Hajia, ki fad’a mata ko ta kwantar da hankalinta ta nuna wa yaro ubansa, ki fad’a mata abun kamar a jininmu yake.”
Wani murmushin rainin hankali Hajia tayi ta kalli Ummy tace “Hakane Sa’ada, ki fad’a masa in dai har kinsan d’ansa, karki ji komai a game dani, kamar yanda ya fad’a ne a kowane d’aki akwai yaro irin Shureim, sannan ni kaina da kike gani fa sanda nake budurwa na tab’a yin cikin nan, ni na ma fisu laifi saboda zubarwa nayi, su kuma basu zubar ba sun haifi abinsu, to kika sani ko fantin dana shafawa kaina ne har yanzu yake biyar zuri’ata.”
K’ara saita muryarta tayi ta dafa hannun Ummy tana kallon fuskarta tace “Sa’ada, ba zan manta sanda aka kawoki gidan nan ba, ni shaida ce Hassan ya same ki a tsarkake, haka ma Hadiza ina d’aya daga cikin wanda suka taimaka mata a daren farkonta, wannan duk ya isa ya zama hujjar da yaranku zasu k’auracewa zina, amma inda gizo ke sak’ar shine ni, ni d’in ne duk ni na gurb’ata muku iyali, ki dubi Alhaji bawan Allah wanda bai san hawa ba bare sauka, shi ya kamata ace yafi kowa damuwa, amma shi ma ido ya saka min yayi hak’uri dani har saida mai rabawa ta raba.”
Numfasawa tayi tana ci gaba da kallonta tace “Sa’ada, ki dubi girman Allah ki fad’a masa gaskiya, Shureim d’an waye a cikin Ammar da Hassan?”
Kutumar bala’i! Shine abinda Ummy ta fad’a a ranta, Hajia! Ciki? Lallai ma, idan ta fahimci inda zancen ya dosa duk ita ce ma silar komai, lallai su Hajia manya, k’warin gwiwa ta samu daga jin kalaman Hajia, sai kawai taji bari ta fad’a da alama ta samu sauk’i.
Ba tare data kallesu ba ta fara goge k’walla cikin muryar data sha kuka tace “Gaskiya ne, Hamna ce ta haife shi bani ba.”
Hajia ce tace “Amma Sa’ada taya kika iya shirya lamarin nan ba tare da mijinki ma ya sani ba?”
Tsaf Ummy ta fad’a musu duk yanda akayi har haihuwarta, d’orawa tayi da “Wallahi a lokacin na tsorata ne sosai na rasa yanda zanyi, tunanin hukuncin da zaku d’auka akan shi ke da mahaifinshi ya k’ara tunzari muka ci gaba da b’oye, amma dan Allah kuyi hak’uri ku yafe min, ya lalata rayuwar yarinya ni kuma na taimaka masa, a idon doka da mutane duk mun aikata laifi.”
Cikin kuka sosai tace “Na sani da ace wani daga waje na ya ci zarafinta, wallahi sai inda k’arfina ya k’are wajen bi mata hakk’inta, da nayi anfani da mahukuntan dake gidan nan da kud’i da muk’amin mahaifinta wajen ganin na kai ko d’an uban waye k’asa, amma daya zama d’ana ne saina kasa yin komai na lullub’eta tare da laifin ina ta hura mata wuta, banda fargaba idan aurenta ya tashi, na yarda da kaina da gyaran dana koya iyaye da kakanni, dole zata banbanta tsakaninta da budurwa, shiyasa kullum fatana Allah ya fito mata da miji tayi aure.”
Kallonta duka suke sai kuma ya juya ya kalli Shureim dake tsaye gaban madubin Hajia yana kallon kwalaben turaren da suka d’auki hankalinshi saboda kyawunsu, kamo hannayenta yayi ya rumgume cikin muryar alhini yace “Yanzu Ummy wannan dalilin ne yasa kike ta nesanta ni dashi dama? Shiyasa ba kya so kiga muna kusantar juna sai kin raba mu?”
Kallonshi tayi tace “Kayi hak’uri Ammar, nasan yanda soyayyar jini d’aya take, duk yanda zan nisanta ku a cikin dubu zaku iya gane junanku, kawai dai ina nesanta ku ne bana son kuyi saurin gane junanku.”
Sakin yaron yayi ya rumgumeta kamar zaiyi kuka yana fad’in “A da tunani na shine baki sona, idan kina hantarata da zagi na sai naga kamar baki damu dani bane, amma yau na gane babu wanda kike so sama dani Ummy, duk wannan kasadar saboda ni ne kika d’auketa, nagode Ummy, dan Allah ki yafe min komai dana mike.”
K’ulli ta sakar mishi a baya tana fad’in “Shashashan banza, taya wai zaka ce bana son ka bayan a cikina na haife ka.”
D’ago kai yayi yace “Hauka na ne ke nuna min haka Ummy.”
Rank’washin shi tayi a kai tana murmushi tace “Kai fa na daban ne yarona, tashin hankalin da ka so min yanzu shine nayi gudu tun tuni yasa ban fad’a maka ba, nasan in ka sani zaka shelanta ne kowa yaji.”
Dariya yayi yana sosa inda ta rank’washeshi yace “Kamar kin sani kuwa Ummy.”
Wani kallo ta masa tace “Au! Kamar ma na sani ne? Wa ya fini saninka a duniyar nan.”
Hajia dake dariya tana kallonsu ne tace “To ku bani hankalinku nan.”
Juyawa sukayi suka kalleta cikin nutsuwa, saida ta kallesu tace “Maganar nan ba zata tsaya iya nan ba, dole akwai wad’anda zamu fad’a ma su san halin da ake ciki.”
Kallon juna sukayi suka sake kallon a tare da mamaki Ummy tace “Hajia su wa kenan?”
Cikin kallon basira tace “Hassan, dole ya sani ko da bama so, da kuma Husseina wacce yanzu ni kaina nake girmamata, ita kwatankwacin Alhaji ce da baya nan a gidan nan, dan haka ita ma zata sani, sai kuma Amna amma bansan ku me zakuyi tunani a game da ita ba?”
Tashin hankalin Ummy da ma Hajia ce kuma gashi ta tsallake cikin sauk’i, dan haka yanzu ita bata damu ba duk wanda ma zai ji ya ji a shirye take, cikin ladabi tace “To Hajia ke me kike gani?”
Saida ta gyara zama tace “A gani na ni dai a fad’a mata, ba dan komai ba sai dan halin rayuwa.”
Da sauri Ammar yace “A’a Hajia, kar a fad’a mata gaskiya ina jin tsoro.”
A tare suka kalleshi da mamaki, Ummy ce tace “Tsoro? Ammar kai d’in? Lallai.”
Hajia ce tayi murmushi tace “Ashe dai har abun ya zo inji me tsoron wanka, Ammar kai ne baka so a fad’i gaskiya, har kake cewa kana jin tsoro, tsoron ma matar aurenka.”
Kallonta yayi yace “Hajia ko yanzu wallahi a shirye nake dana fad’awa duk duniya waye Shureim, ita dai ce kawai bana son ta sani.”
“Saboda me to?” Cewar Ummy tana kallonshi.
Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Saboda tana d’aya daga cikin mata ukun dake kassara tunani na, tana d’aya daga cikin wanda tunanin al’amarinsu ma kad’ai yake firgita min nutsuwa ta, tana d’aya daga cikin sanyin idanu na, d’aya ce daga cikin ukun da bana son ganin tashin hankalinsu.”
Kallon Ummy yayi yace “Taya zan so nutsuwarta ta bar gangar jikinta kan abinda na aikata, kwanciyar hankali na ce ita, taya zan so taji abinda nake da tabbacin zai gusar da hankalinta, idan kuma haka ta faru ni wa zai nemo min nawa hankalin, mallakina ce kuma babban rabon dana gada a gidan duniyar nan, idan zan misaltata da gona to bansan adadin girman ekar dake cikinta ba, daga ni har yarana ita ce duniyar mu.”
Ummy da taji hawaye sun cika idonta ne tace “Bansan ya zata ji idan aka fad’a mata ba?”
Murmushi yayi yace “Ummy kunsan a ina naji kuwa?”
Girgiza kai tayi tana kallonshi har ya d’ora da “Ita ce ta fad’a min.”
Hajia ce tayi saurin cewa “Ita wa?”
“Amna mana.” Ya fad’a yana kallonta, zaro ido duka sukayi sai kuma Ummy tace “Amna? To ita a ina taji? Amma kuma banji tashin hankali ba?”
Murmushi ya sake yi yace “Ummy yarinyar nan tayi a rayuwa wallahi, ita ta fad’a min da kanta, amma abun tsoratarwa ta d’auki abun kamar tatsuniya, abun ma dariya yake bata sabodaa ganinta abu ne da ba zai tab’a faruwa ba, sannan tana da yarda akai na da kuma yar uwarta d’ari bisa d’ari.”
Da mamaki tace “Amma a ina Amna taji maganar nan?”
Ammar ne yace “A wurin Amie k’awarsu.”
Da wani mamakin tace “Amie kuma? A ina Amie taji to? Babu fa wanda yasan da maganar nan.”