BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri cikin jin dad’i Amna ta kalleta tace “Dan Allah yer uwa tashi kije.”

Juyawa yayi zai fita Hamna tace “An k’i a je d’in, Allah Amna ki fita idona, kai kuma wallahi ka da ka sake tanka min k’ibata, idon sha’awarta kake kasa matarka tayi maka can ka cinyeta idan kana so, maye kawai.”

Yanda ta k’arashe da murgud’a baki da harara yasa shi kallonta yace “Ai aljannata idan tayi k’iba saita hanani fita gaba d’aya, a yanzun ya muka k’are tana neman kasheni bare ta k’ara auki.”

Wani haushi ne taji na neman kasheta, to wai akan me yake mata wannan rashin mutumcin? Ina ruwanta dashi ma da zai rik’a b’ata mata rai?
Cikin shagwab’a Amna ta kalleshi tace “Duniyata, ya isa haka mana ka tafiyarka saika dawo.”

Kallon Hamna yayi yace “Kin ci albarkacinta, yanzu tashi muje na fad’a miki abinda nayi niyyar fad’awa masoyiyata.”

Cike da tsiwa tace “Ba zanje malam ka d’aukeni in ana dole.”

Bushewa yayi da dariya yace “Na d’aukeki? A gaskiya yanzu ban shirya ganin likitan k’ashi ba, gashi kuma yanzu rob ya k’ara tsada a kowane shago, dan haka ba zan iya ba amma wallahi sai kin je.”

“To na gani idan akai zaka d’auke ni.”

Nufowa yayi wajenta da sauri ta mik’e tsaye tana ja baya tace “Ammar bana son iskanci fa, Allah ka addabeni, wai kai baka da abunyi ne daya wuce ka bini a guje?”

Kallonta Amna tayi ta kalleshi tace “Dan Allah yah Ammar ku fita farfajiya, ni dai kaga ba iya tashi zanyi ba bana so ku fad’o min ku k’arasani.”

Kallon Hamna yayi yace “Ni ne Ammar kai tsaye ko kankana? Kuma ni ne baki san iskanci? To ki rubuta wannan kalaman ki aje saboda ki iya tuna dalilin da yasa na hukuntaki yayin da na miki rugu-rugu.”

Hanya ya kama zai fita ya kalleta yace “Ke dai kinfi kowa sanin kalar nawa horon, tarihi nake kafawa mutum idan har na tashi zuwar masa.”

Gabanta taji ya shiga fad’uwa dakan uku uku da sauri, ai kuwa ta sani dan ya kafa mata wannan tarihin, to miye abunyi? Hak’uri! Na bashi hak’uri kawai tunda na ga jarababbe ne na k’arshe kuma kaifi d’aya, bugu da k’ari kuma bugu d’aya yake yi sak’onsa ya isa inda ya aika shi, kallon Amna tayi tace “Ina zuwa.”

Da gudu ta fita ta nufi wajen ajiya motoci, tana hangoshi ta tsaya tafiya d’aya bayan d’aya, har ya shiga ya tayar ya hangeta saiya bud’e ya zuro k’afa d’aya yana kallonta har ta k’araso, murmushin gefen labb’a yayi yace “Kin zo bayar da hak’uri ne? Munafuka kinji tsoro kenan?”

Had’e fuska tayi ta harareshi tace “Allah ya sawak’e na baka hak’uri, kawai na zo fad’a maka…”

Shiru tayi ta rasa abinda zata fad’a sai shi yace “Me kika zo fad’a min?”

“Na zo karb’an sak’on ne.” Ta fad’a da sauri, wani murmushin ya sake yi ya kalleta da kyau yace “Kankana, wannan kayan da kika ce sun min nisa ki sani daga yau su ma *mallakina ne*, ka da ki kuskura ki jawa wani tsautsayi ko k’arar kwana ta hanyar k’ok’arin mallaka masa mallaki na, in kuma ba haka ba to ki sani har ke sai nayi kasonki (prison).”

Yana gama fad’a ya rufe murfin motar da k’arfi yayi baya baya ya daidaita ya fita a gidan, fitsari ne ko kuma ruwan haihuwa? Bata san ainihin meye ke son zubo mata ba tsabar kad’awar da cikinta yayi, to me yake nufi? Zai ajiyeta ne a haka yayi ta kallonta yana tsokanarta yana binta da gudu? Ko kuma karuwarsa yake da niyyar mayar da ita? Wannan al’amari yafi k’arfin tunaninta, amma zata k’aryatashi ta nuna masa ita ke da kanta bashi ba, zata nuna masa abinda ya faru ma ya k’wata ne da k’arfi ba da son ran ta ba ya karb’a, yanzu kuma zata bawa wanda ya dace ne, amma ba zata zauna ba kamar yanda yake mata wannan fatan, dan kuwa fatan zama ne yake mata.

*Da dare* yana kan hanyarshi ta dawowa gida tsautsayi da ba’a saka masa rana ya afka mishi, mai mashin da wata mota ne suka kwatse sai kawai suka bigi tashi motar daga k’ofar da yake zaune, Allah ya kiyayeshi bai ji wani ciwo ba sai buguwa da k’afarta tayi, bayan jami’ai sun zo sunyi dube dubensu da aune aune aka tafi asibiti, ya so tafiyarshi gida amma lura da wani jami’i yayi yana d’an taka k’afarshi da k’yar yasa suka matsa mishi suka tafi, kafin a duba shi k’afar tayi sumtum bata takuwa, saida ya kalli mai motar d’aya wanda duk ciki shine baida gaskiya yace “Kai dai Allah ya saka min wallahi.”

D’aya daga cikin jami’an ne yayi dariya sai mai motar dake zazzare ido yace “Ayi hak’uri yallab’ai, tsautsayi ne.”

“Na gidan uban wa? Karka wani d’orawa tsautsayi kaji, ganganci ne da hauka.”

Duk yayi maganar ne yana danna wayarshi, Jibril ya kira dan a lokacin yasan shine ke da k’arancin abunyi, yana d’aukar wayar ya kara a kunne yace “Ka zo *Clinik katsina* ka same ni.”

Jibril ne yace “Katsina kuma? Me kake…” Bai barshi ya fad’a ba kawai ya datse kiran, juya akalar motarshi kawai yayi ya d’auki hanyar, bai d’auki lokaci ba ya isa can, tun a k’ofar asibitin ya ga motarshi, hankalinshi ne ya tashi ganin yanda murfin dake b’angaren mazaunin yayi, yana cikin kallo da mamaki yana shiga asibitin wayarshi ta sake k’ara, d’auka yayi inda mahaifinshi yace ya zo gida ya same shi, a cewar Jibril “To Abba ina zuwa, yanzu haka ma ina asibiti ne Ammar ya kirani.”

“Asibiti kuma? Wace asibitin ta su?”

Cikin rashin tabbas yace “A’a Abba, ina ga fa hatsari yayi, dan ga motarshi can a waje ta bugu sosai daga wajen zaman matuk’i, amma dai bari na shiga ciki na gani.”

Cikin tashin hankali shima yace “Subhanallah, Ammar d’in?”

“Abba ina zuwa.” Ya fad’a yana kashe wayar ganin Ammar da yayi zaune jami’ai biyu tsaye a kansu, yana zuwa yace “Subahanallah, Ammar hatsari kayi?”

Mik’a masa hannunshi yayi yace “Ba surutu nake so, muje kawai ka kaini wajen duniyata, baiwar Allah yau saura kad’an wannan hamagon ya kashe mata ni.”

Wani galala mutumin ya kalleshi, shima kallonshi yayi yace “Eh na fad’a, kayi hak’uri in zakayi in kuma ba zakayi ba ka mutu, ba zan iya b’oyewa bane har na tafi da magana a bakina kuma wacce ta shafeka.”

Kallon jami’an yayi yace “Sai anjimanku.”

Kamashi Jibril yayi sun fara tafiya kuma ya fizge hannunshi yace “Kai sakar min hannu bana so, dama dan jami’an su gane ya bigeni ne sosai ko sun ci tararshi dayawa, d’an banza ya ban haushi wallahi.”

Jibril kam kecewa yayi da dariya yace “Sharri kamar mace.”

Hararanshi yayi yace “Idan ba mace ce bani ai na mata ne, mace ta haifeni, mace ta haifi uba na da uwata, mace ce mahutata kuma insha Allahu a yaran da zan haifa akwai mace, to meya rage min kuma?”

Jinjina kai yayi yace “Na ga ranar da bakinka zai rufe.”

Ba tare daya kalleshi ba yace “Sai ranar da k’asa ta rufe min ido.” Da suka fita saida ya jira makanikenshi ya zo ya d’auki motarshi sannan suka d’auki hanyar gida.

Labaran na jin Jibril ya katse kiran saiya kira lieutenant, shima yana d’auka abinda ya fad’a masa kenan, cikin tashin hankali ya kira Ummy dan yaji ko tana asibiti, cikin rashin fahimtar tambayarshi tace “A’a, lafiya meya faru? Ko jikin Hajia ne?”

Cikin tashin hankali yace “A’a ba Hajia bace, wai Ammar ne yayi hatsari, Jibril yaje ya duba asibiti.”

Ummy dake tattara kayanta tana sawa cikin jaka zata tafi gida tana jin haka ta saki jakar tace “Me? Ammar? To ya yake dan Allah? Yaji ciwo ne?”

Lieutenant ne yace “Ban sani ba nima.”

Cikin d’aga murya tace “To ka kira ka tambaya mana kaji, ya zaka ce min baka sani ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected