BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri ya dawo d’akin yana fad’in “Fito kai tsaye kice d’an wuta ne ni mana.”

Hannayenta ta d’aga tana tare shi dan ba zata iya gudun ba tana fad’in “Ni fa tambayarka ne nayi a jikinka kake ji ko a jikin wani.”

Juyawa yayi zai fita yana fad’in “Kinyi sa’a yau nake aurar da ‘ya wallahi, da sai na miki cikin yan uku.”

K’eyarshi ta ma gwalo tana fad’in “To inba d’an wutar ba wannan jirin daka d’iba dani kamar wacce ta hau jirgin sama.”

Tafiya suke a hanya tana d’aura d’an kwali, cike da nishad’i yake biyar wak’ar wani film wai ita *madubin dubawa* wacce Ali Nuhu da Rahama Hassan sukayi play roll d’in, yana biya kamar abun gaske, amma daga jin baitin da jarumar ta fad’a ya kalli Hamna yace “Kinji wai ta sauke farashi, yo shi ba dan ma ana so a bada maza ba wane farashi ne har mace zata kallemu tace ta sauke, ke baki ga inda muke tsada ba ma ku ne ke biyanmu sadakin.”

Shiru ta masa tana d’aura kallabinta kafin ya sake cewa “Kuma fa ita ba wata kyakyawa ba banda dai Allah ya taimake ta tana da manyan kaya.”

Kallonshi tayi ta harareshi sama da k’asa tayi k’wafa, kallonta yayi yace “Me ye na hararata ke kuma?”

Saida ta gyara d’an kwalin tace “Inba gulma ba da sa ido har ka mata kallon k’waf ka gane manyan kaya ne da ita ko?”

“To makaho ne ni?” Ya fad’a yana kallonta, a hassale ta kalleshi tace “Ba mahako bane, amma idan na cire maka su zaka dawo makahon.”

Wani kallo ya mata yace “Wai ke mayya ce?”

“Eh.” Ta fad’a tana kumbura, tab’e baki yayi yace “Wai ma me ye farashin da take magana akai?”

Kallonshi tayi tace “Ka tambaye ta mana.”

Tab’e baki yayi yace “Wai haushi kike ji saboda naga ita ma k’atuwa ce kamar ke? To naje na ce a dafani a cinye.”

Wani kallo ta masa bata sake cewa komai ba har suka isa.

Yau fa akayi ta kam a wajen d’aurin aure, bayan an d’aura ya shigo da ango har cikin gidan, har d’akin Ummy inda amarya take ya zaunar dasu, hud’uba ya musu sosai mai ratsa jiki, saida ya gama kamar abun arzik’i sai kuma ya kalli Huda yace “Kina ji na? Duk sanda ya guma miki laifi ki zo ki same ni, sai kin fad’i yanda kike so na miki dashi, in na dafa miki shi da fatar jikinshi ne, ko kuma sai an cire fatar a dafa sai kin zab’a.”

Ango dai murmushi ya saki inda ya kalleshi shima yace “Kai ma kuma idan ta b’ata maka, ka zo ka same ni zan fad’a maka yanda zakayi da ita.”

Kud’in hannunshi ya mik’a ma Huda yace “Karb’i nan sadakin ki ne.”

Cikin lullub’inta na dara tace “Abba ka rik’e kawai, ni babu abinda zanyi dashi.”

Kallonsu Ummy dasu Zeinabu yayi yana dariya yace “Kunji wai Abba, yanzu nan fa ya ce na aurar, kai Allah nagode maka, yanzu nan da yan shekaru kad’an Amnata ma zan aurar da ita.”

Kallon Huda yayi ya kamo hannunta ya damk’a mata kud’in yana fad’in “Wannan sadakinki ne, kamar yanda mijinki ne kad’ai ke da wani muhimmin hurumi akan ki yanzun, haka wannan kud’in ma ke ya dace ki rik’e abinki, lada ce ta wani muhimmin abu da zaki rasa a jikinki.”

Sautin kukanta ta k’ara hakan yasa shi dafa kanta yana fad’in “Kar kiyi kuka mana, ni ma saiki saka ni kuka.”

_(Allah ya bar mana kai kakanmu Tahir, ka iya wakilci)_

Saida ya kai k’ofa zai fita ya kalli Zeituna yace “Uwa wai me yasa amare ke kuka ne? Wani abu suke tsoro ko kuma fargaba ne?”

Da kunya ta shiga rarraba ido ta kalli Ummy tace “Aunty ce zata fad’a maka.”

Da sauri ta bar wajen Ummy na fad’in “Ke dawo ke zaki iya da kayanki, ai ba ni ya tambaya ba.”

Murmushi ya saki yana kallonta yace “Ummy na ma gane, to amma naga ai daga baya kuma idan kuka saba kun ma fimu zak’ewa.”

Da k’arfi ta dafe k’irji tace “Mu kuma?”

Cikin i’ina yace “A’a ina nufin su, su matan.”

Ficewa yayi ta bishi da kallo, ko data hange shi tsaye kan Hamna dake shirya yaransu da suka kwana anan tace “Allah fidda *A’i* daga rogo.”

*Badak’ala na ban kwana insha Allah*

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:40 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_79_

Ana ta cashewa a wajen bikin Hamna na zaune k’ofar gida tare da wata k’anwar Soueiba, ta baza mata hajar kayan mata tana dubawa inda Ameera ke kusanta tsaye, Ummy ce zata shiga cikin gidan ta kalli Ameera tace “Wai ke yaushe zaki girma ne? Kina nan k’ugunta ba zaki je cikin yara kuyi wasa ba.”

D’agowa Hamna tayi ta k’ara mannata a jikinta tana fad’in “Ummy ki barta dan Allah, ni kaina bana so tana min nisa ai, mace ce dole ina buk’atar tafi sabawa dani fiye da kowa.”

Tab’e baki Ummy tayi tace “Amma kuma bata sakewa cikin yara taya za tayi wayo da fasaha?”

Turo baki Hamna tayi tana kallon Ummy har ta wuce, kallon Ameera tayi ta manna mata sumba a kumatu tana fad’in “Ai kina da wayo ko?”

Kallonta tayi tana mak’ala hannayenta a wuyan Hamna tana dariya da fad’in “Ummy, in fad’a miki wani abu?”

Kallonta tayi tace “Fad’a min mana yer uwata.”

Saida ta kalli k’anwar Soueiba dake ta mik’owa Hamna magani tana karb’a tana dubawa, cikin kunne ta rad’a mata magana, bud’e baki tayi da dariya a fuskarta ta kalleta tace “Da gaske? Haka yace miki?”

Cikin jin kunya ta rufe fuskarta da kallabin Hamna, jinjina kai tayi tana fad’in “Ina ga fa za ayi yar gida ce ko?”

Dariya suka saka gaba d’aya, tana cikin dubawa ta ga motar Ammar ta paka, da sauri ta shiga tattara kayan tana fad’in “Taimaka b’oye kayan nan kar mutumin nan ya sauke min kwadon tsiya a wurin nan.”

A tsorace matar ta shiha tattarewa tana fad’in “Baya so kina aiki dasu?”

Saida ta gyara zamanta tana kallon motar tace “Ba haka bane, bana so ya sani ne kawai zai min tsiya wallahi.”

Suna kallo ya fito ya canza kaya bana safe bane jikinshi, a hankali Ameera ta tarbeshi inda ya kamo hannunta suka k’araso, yana zuwa ya dangwari kan Hamna yana fad’in “Kankana me kike fad’a ma ‘yarki naga kuna ta dariya?”

Matar na kallonshi tana musu dariya sai Hamna data dafe kanta tace “Yaushe?”

Kallonta yayi yace “Ke ni ba makaho bane ina gani, me kike fad’a mata?”

Turo baki tayi tace “To wai banda ikon da zanyi magana da “yata ne? Sirri mukeyi mana kai ma kaje ka kama naka yaran mana.”

Tab’e baki yayi yace “Ke dai kika sani, yanzu tashi shiga cikin gida.”

Da sauri ta mik’e tana fad’in “To yallab’ai.” Kallon mai maganin tayi ta k’yabta mata ido ta shiga ciki tare da Ameera, a baya ya bisu yana fad’in “Yau ma ana bikin ba zaku rabu ba? Wai ke wace jaraba ce kika koyawa yarinyar?”

Gum tayi da baki dan ta fahimci me yake nufi, tayi magana ne ya fara tayar mata da hankali cikin mutane, rik’o mayafinta yayi hakan yasa ta juyowa tana kallonshi, kallonta yayi yace “Yunwa nake ji.”

Wani kallo ta masa tace “To ya zan maka kenan?”

Shima wani kallon ya mata yace “Ya rage naki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected