BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar had’in baki saiya zamana babu wata tazara tsakanin zuwan nasu, kuma kowa b’angaren su yake nufa dan ya shirya babu mai tunanin aiki gobe tunda dama asabar ce, sa’a akayi Junaid zai shiga d’akin shi Amar kuma ya shigo falon, nan Amar ke tambayarshi “To wai yanzu hanya zamu d’auka kenan?”

Junaid ne yace “Yanzu ba wannan ba, mu fara saurin kimtsawa dai, daga nan sai mu san abinyi, dan kasan gidan nan akwai yan gaggawa dayawa, babu wanda zai jiramu idan…”

Fitowar Ammar cikin bak’in yadi shara-shara har ana ganin farar rigarshi yasa sukayi shiru suka kalle shi, kamar dai kullum fuska a tamke ya kalli Junaid yace “Su waye yan gaggawa a gidan nan?”

Juyawa Amar yayi ya nufi d’akin shi yana fad’in “Na gode Allah da yasa tambayar nan taka ce d’an uwa, fatan alkairi.”

Junaid kuma murmushi yayi yace “Ah haba dai soja, cewa nayi dayake gidan nan akwai…”

Da gudu ya shige d’akin shi ya rufo k’ofar daga ciki yake fad’in “Yan gaggawa na ce, kuma kaine farko, sai wannan kawun naka (mahaifinshi kenan) colonel yake ko me ma.”

K’anan Jibril ne ya shigo da sauri wanda yake da tare da mahaifinshi Labaran a kasuwa suna kasuwanci shi ma ya shigo dan shine na uku da Ammar ya turawa sak’on duk da suna gaba dashi nesa ba kusa ba, kallonshi Ammar yayi yace “Ka fad’a ma yaran nan ina jiranku waje nan da minti biyar, idan lokacin nan ya cika baku fito ba, to zan tafiya ta ne tunda kowa da motarshi ai, amma ka fad’a musu umarnin Abba ne yace mu tafi tare.”

Yana gama fad’a ya fice daga d’akin inda *Jamil* ya bi dak’unan daya nuna mishi da kallo, k’wank’wasa musu k’ofar yayi ya sanar da sak’on Ammar kafin shima ya shiga dan shiryawa.

*Minti hud’u* Amma ya fara doka wata uwar oda data firgita duk wanda ke cikin gidan, wad’anda suka san da su ake tuni suka gigice suka rasa ma abunyi, ba tare daya daina odar ba sai kuwa gasu da gudu suna rige rige, Jamil bawan Allah ko d’akin shi bai rufe ba ya taho da gudu da takalmi a hannu da k’yale alamar gogewa zaiyi ko yake cikin yi, bud’e k’ofofin motar sukayi suka zauna Junaid yace “Dan girman Allah odar ta isa haka, gamu nan fa mun shigo ko.”

Amar ne ya doka wani uban tsaki saboda sai lokacin ya kula da abin goge bakin (brush) daya taho dashi a aljihu, juyawa sukayi suka kalle shi ai sai Junaid ya kwashe da dariya, cikin jin haushi Amar dan ko turare bai fesa ba yace “Kai ban son k’ananan iskanci fa.”

Mayar da kallonshi yayi ga Ammar yace “Allah Ammar ba ka kyautawa, yanzu shirin ma ka barmu mu tafi a tsanake amma ba zaka iya ba, wane wace irin rayuwa ce, haba.”

Juyowa yayi ya kalleshi ya had’e girar sama da k’asa yace “Kar ka fad’a min maganar banza, yan daudu ne ku ko mata da zaku ce shirinku na buk’atar b’ata lokaci?”

Cikin jin zafi Amar yace “Yan daudun ne kamar kai ba, ai kai gashi nan ka shirya a tsanake babu wanda ya takuraka, sai mu daka raina, wallahi ba dan ance Abba ne yace mu tafi tare ba da babu tsiyar da zata sanya na tafi da kai, tunda ai motarka ba fin tawa motar tayi ba.”

Idon Ammar ne sukayi launin ja ya fito daga motar da k’arfi tare da zagayowa inda Amar yake a baya yana fad’in “Amar ni kake kira d’an daudu? Ni? Ni sa’anka da zaka kirani da d’an d…?”

Junaid ne yayi saurin rik’e Ammar d’in saboda bud’e murfin motar da yayi zai daki Amar da shima ke shirin fitowa, fitowa yayi a hassale shima yace “An kiraka d’an daudu, mu daka kamalta mu dasu bamu da zuciyar jin zafi ne ko me? Sai kai daka fi mu sanin ciwon kanka kenan, uban son girman tsiya, tsakani na da kai ko minti biyu babu, amma kullum kai ganinka ka girmeni da wata tazara mai tsayi.”

Junaid dake ta rik’on Ammar yana bashi hak’uri cikin b’acin rai ya sa gwiwar hannunshi ya buge shi a baki yana fad’in “Dallah sakeni malam, kana ji yaro yana fad’a min magana son ranshi.”

Junaid daya ji hanb’ara a baki baisan sanda ma ya sake shin ba, tuni jini ya gabce mishi harda hanci ma, sai kuwa Ammar ya cakumi wuyan Amar da hannu biyu ya shak’e shi sosai yana fad’in “Ni kake wa iskanci, ko sakan d’aya na baka ince dai ni na fara shan iskan duniyar? Shine zaka tsaya kana raina min wayo dan kawai kunga ina k’yale ku.”

‘Yan biyu a madadin had’in kai sai gashi Ammar da Amar suna dakuwa kamar yara k’anana, amma Amar yafi galabaita saboda har yanzu Ammar bai sake shi ba daga shak’ewar daya mi shi, duk da haka kuma sai kai yake buga mishi a nashi kan, a d’aya b’angaren kuma yasa gwiwar k’afar shi sai tokara mishi yake a ciki, shi kuma duk dukan da yake ma Ammar d’in ma ba ji yake ba, ai kuwa gani Ammar zaiyi kisan kai yasa Junaid dake jinyar kanshi da Jamil suka fara k’ok’arin b’anb’are shi, dan tuni fuskar Amar ta fara had’a jini daga baki da hanci, amma saboda bak’ar zuciya ta Ammar sai ya dinga kai musu haura suma, ana cikin haka Ummy da ta ga mutuwar Hajia Fatime a kafar sada zumunta na alahlin Gaga ta taho gida suka ji muryar ta tace “Junaid, Jamil, ku barshi ya kashe shi.”

Tana fad’a ta wuce b’angaren su ko kallonsu batayi ba, su Junaid kuma basu bar raba su ba saida Junaid ya tattara k’arfin shi ya fizgo Ammar daga jikin Amar yana fad’in “Dallah malam sake shi ko.”

Amar na jin ya samu numfashi ya durk’ushe a wurin yana mayar da numfashin wahala, Jamil ne ya taimaka mishi ya mik’e suka nufi b’angaren iyayen sai Junaid daya bi bayansu bayan ya k’arewa Ammar kallo wanda ya buga murfin mota da k’arfi ya juya ya koma b’angaren su, suna shiga ciki suka ci karo da Zeinabu da faranti a hannu, tana ganin Amar a yamutse tace “Jamil lafiya? Meya same shi haka? Allah yasa dai ba hatsari yayi ba.”

Kafin ya bata amsa Junaid ya shigo bakinshi har ya fara kumbura kuma har yanzu yana fitar da jini kad’an kad’an, da sauri ta saki farantin ta k’arasa ga Junaid tana fad’in “Kai wai lafiya? Meya sameku ne haka?”

Cike da k’aguwa Junaid ya d’an janye hannunta data tab’a shi yace “Umma ba komai, ba had’ari mukayi ba.”

A lokacin Jamil harya zaunar da Amar kan kujera ya nufi d’akin Ummy dan ta fito ta duba shi, Zeinabu ce ta kalli Junaid tace “In ba had’ari kukayi ba to me kukayi? Dubeku fa.”

Shima zama yayi a kujera ranshi a b’ace yana murza bakinshi, Soueba ba ta fito yayi daidai da fitowar Jamil dan Ummy tace babu inda zataje can su suka sani, Soueba ce ta kalli Jamil tace “Kai wai lafiya; meya faru ne haka? Meya samu Amar d’in.”

Cike da damuwa yace ” Mama ba komai, dan Allah kije ki samu Ummy ki fad’a mata Amar na zubar da jini ta zo ta duba shi, ni na mata magana amma ta k’i fitowa.”

Amar na jin haka ya mik’e ya nufi d’akin Ummy duk da jirin dake son kwasar sa, cikin fad’a da hushi Zeinabu tace “Wai duk uban da aka tambaya sai yace ba komai bayan ga komai d’in, to koma menene ya faru ba sai ku fad’a ba, idan har kunsan ba zaku fad’a ba meye na shigo mana d’in? Wato inda iyayenku ne maza suka k’ura muku ido da tuni kun sakar musu zance, amma dake mune marainanku da muke wasa da ku kowane na hancin uwa sai dai yace ba komai, to kuje da ku da ba komai d’in duk kun ci uwarku.”

Cikin b’acin rai Junaid yace “Dan Allah Umma meye haka? Mun fad’a miki ba komai ba shikenan maganar ta wuce ba, zaunawa zamuyi mu fad’a muku Amar da Ammar ne suka samu sab’ani har ta kaisu ga doke doke.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected