BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
K’arfin marin yasa shi duk’ar da kai gefe d’aya dafe da kunci, ya jima haka yana sauraron masifar da Ummy ke mishi, cikin hargagi da zautuwar tunani take fad’in “Baka da hankali ne? Wannan wace irin fitsara ce? A gidan uban wa ka koyo wannan tarbiyar? Anya Ammar kai d’ana ne kuwa? Ka sani fa a hanyar aure na same ka ba da zina ba.”
Hannun Hamna ta kama da niyyar barin wurin taji Hajia tace “…
*Saboda farin cikin isar da yarinyata lafiya d’akin mijinta.*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI_ (sai Allah)
*6* _JIHADI_
*7* _K’ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K’ADDARARMU_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura…)_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
*AHALI NA*
©
*TAURARIN NIGER..*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
✪{T . N}✪️
https://www.facebook.com/Taurarin-Niger-100155928500614/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_39_
Hajia ce tace “Malama meye na tunzura haka? So kike ki rufe bakinmu mu kasa fad’ar rashin kunyar d’an ki? To dawo da ita tafiya zasuyi.”
Juyowa sukayi suka tsaya sai rarraba ido suke alamar rashin gaskiya, a lokacin ne Hajia ta kalli Hamna da kyau, kallabi ne jikinta wanda bai rufe mata jiki ba, tabbas Hajia tasan ita da Amna ba ma’abota bras bane, dan gabansu a cike yake kuma pampam dashi, su Umaimah ne sarakan sawa kullum, amma ganin yau sun mata wata irin cikowa kamar mai ciki yasa ita kanta sai taji ba dan Ammar ba mutuminta bane data yarda da abinda ya fad’a, Ummy dake cike da razani da tsoro tuni ta ga kallon da Hajia ke mata, da sauri tace “Hajia kinsan shi da shirmen banza, bai san me yake fad’a ba wani lokacin, komai ya zo bakinshi saiya fad’a.”
Amna ce ta kalli Ummy ranta a matuk’ar b’ace na marin data wa mijinta, d’an k’aramin iska ta furzar irin na rashin jin dad’in nan kafin ta matsa kusa da Ammar da har yanzu ya k’asa d’agowa, a hankali ta kama hannunshi tana kallonshi, ganin bai kulata ba yasa ta kalli Hajia tace “Hajia dan Allah kiyi hak’uri ki barta anan, wallahi bata san tafiya ita ma.”
Wani kallo ta mata tace “Ita ta fad’a miki bata so? Ko kin ari bakinta ne kin ci mata albassa?”
Kallon Hamna tayi tace “Na sani bata so, kuma gata nan ku tambayeta.”
Mahaifinsu ne yace “To ko bata so ba dole ta hak’ura ta so ba tunda Hajia tace a tafi da ita.”
Hajia ce ta kalli Hamna tace “Ke kika fad’a mata ba kya son tafiyar?”
Kallon Hajia tayi ta kalli Amna da ita ma ta kafeta da ido, kallon kiyi hak’uri ta mata sannan ta kalli Ummy dake kusa da ita, a k’wayar idon Ummy ta hangi abinda ta kasa fahimta, shin tana son tafiyarta ne ko kuma a’a, rashin sanin amsa yasa ta kalli Hajia ta sunkuyar da kai tace “Ni ban fad’a mata ba, ina so na tafi tare da Abba.”
Kallon mamaki da takaici Amna ta mata, me yasa za tayi haka? Cikin jin haushi tace “Amma ai ni nasan ba kya son tafiyar, kuma idan kin manta na tuna miki, kina shirye shiryen tafiyarki koyon kwalliya ne.”
Idan har ba bak’ar magana ta fad’a mata ba tasan ba zata rabu da ita cikin sauk’i ba, dan haka tace “Ni bana son koyon wata kwalliya, wajen mahaifina zan koma da zama.”
Murmushin rainin hankali Hajia ta bisu da shi tace “To kinji abinda ta fad’a da bakinta, dan haka ki barta ta tafi can, idan da rabo ma ta samu miji acan aure zan mata, sai dai kawai kije bikinta idan da hali.”
Da k’arfi ya kalleta, *miji*? kuma *aure*? acan d’in? Hummm! Juyawa yayi da sauri ya nufi hanyar barin d’akin, da sauri Amna ba tabi bayanshi dan bata ga abinda zata zauna tayi ba, kai tsaye b’angarensu suka koma.
Kallonta Hajia tayi tace “Ki d’auko kayanki ki zo ku wuce.”
Juyawa tayi ta koma sama, ba b’ata lokaci ta d’auko ta sauko k’asa, tana zuwa Gombo ya mik’e yana wa mutanen wajen sallama, tafiya sula fara yi suna barin falon, anan Ummy ta samu damar fad’awa Hamna cewa “Karki damu Hamna, ki tafi dasu yanzu, tunda Hajia ta yanke hukuncin nan babu mai hanawa, amma ina so duk abinda kike ji a jikinki karki bari kowa ya sani, ki kira ki fad’a min zansan abun yi, kafin lokaci mai tsayi kuma nasan ta hak’ura tasa a dawo dake.”
Jinjina kai kawai tayi suka fita, a farfajiya daidai k’ofar fita suka samu an saita hancin motocin, anan suka samu Aissata tsaye tana amsa waya da harshen zarma, saida ta gama wayar kafin ta kallesu cike da izza da d’aga kai sama tace “Sai anjima.”
Zeituna da Zeinabu ne suka amsa da “Sai anjima, Allah ya kiyaye hanya.”
Mai aikin data taho da ita ce ta bud’e mata k’ofa zata shiga, tsayawa tayi ganin Hamna na shirin shiga motar gabansu ansa jakarta a but d’in motar, da mamaki tace “A’a! Me wannan kuma take yi ne haka? Ina zata je ne?”
Mai aikin ce ta girgiza tace alamar bata sani ba ita ma, Gambo ne ya tsaya daga shirin shiga motar yana kallonta yace “Tare zamu tafi da ita.”
Yamutsa fuska tayi tace “Ban gane tare zamu tafi ba? Tare muka zo da ita ne?”
“Umarnin Hajia ne, dole haka za ayi madame.” Cewar Zeinabu, rai a b’ace ta juya ta kalli Gambo, kallon kiyi hak’uri mana har muje gidan ya mata, saida ta matse baki alamar akwai magana kafin ta shiga motar, tasan kawai dan Hajia ta muzguna mata ne ta had’a su tafiya da Hamna, amma inba haka ba meye na sawa a tafi da ita, yaran da ko da k’uruciya basu tafi ba bare yanzu da girmansu, suna kallo suka ja motoci suka fita daga gidan anata jiniya, basu zame ko ina ba sai filin jirgi, daga nan kuma suka d’aga zuwa Niamey.
D’akinshi ya shiga ya rufe zauna kan gado, tunanin abinda ya faru yake yi, yaji zafi sosai, ba wai marin data masa bane ya b’ata masa rai, marinshi da tayi a gaban wacce zai iya kira da matarshi, ta d’aga hannu ta dalla mishi mari, jin bugun zuciyarshi ya fara canzawa yasa shi mik’ewa da sauri ya fito daga d’akin yana fad’in “Ina! Ba zan tab’a bari damuwarku ta sa min ciwon zuciya ba, idan na mutu ma ba ciwo zakuji ba.”
Falon ya dawo ya nufi wajen fridge ya bud’a ya d’auki ruwa, saida yasha sosai sannan ya dawo ya zauna kan kujera, tv ya kunna yana kallo sai kuma ya tuna da Amna, tunda ya nufi d’akinshi ita ma tabi bayanshi, amma kallon daya mata yasa ta shiga d’akin ta ita ma. Mik’ewa yayi ya shig d’akin, kwance take kan gado tayi ruf da ciki, k’arasawa yayi ya zauna kusa da ita yana ci gaba da kallonta, sai dai yafi mayar da hankalinshi kan hannunta na hagu wanda ta mik’ar dashi, ta kifa hannun ta mik’e yatsunta wanda ke rufe da jan lalle, amma yatsanta manuniya sai bubbugashi take akan katifar da sauri sauri kamar tana bubbugashi akan tebur, shafa hannun nata yayi hakan yasa ta tashi zaune tana kallonshi, sunkuyar da kanta tayi sanda taji wasu hawaye sun taho mata, da alamar damuwa ya kalleta yace “Kuka ne kike? To me akayi kuma yanzu? Amna bana son kuka fa ko da na yaro ne.”
Abinda ya fad’a ne yasa ta rushewa da kuka ta d’ora kanta akan kafad’arshi, cikin kuka take fad’in “Yah Ammar bana jin dad’i, zuciyata kamar zata fashe, yer uwata yau tayi nesa dani, sannan Ummy ta mare mijina a gabana, banji dad’i ba ko kad’an, kawai dan babu yanda zanyi ne.”