BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallonta data mata yasa Raihan ganin ta sake shiga uku, da sauri ta mik’e tayi baya nesa da su cikin matsanancin kika tana fad’in “Iyayena dan Allah ku fahimce ni, wallahi ban aikata abinda kuke tunani, idan baku yarda ba zaku iya kaini duk likitar da kuke so a duba ni.”
A fusace Abbas yayi kanta ganin haka Sameera da sauri ta mik’e ta shiga tsakaninsu tace “Kayi hak’uri dan Allah ka nutsu, idan muka bi ta zuciya zamu iya kasheta, a k’arshe zamu iya yin nadama.”
Yatsa ya nuno mata ya bud’a baki zaiyi magana wayar shi tayi k’ara, juyawa yayi ya koma inda Sameera ta saki wayar ta taso ya duba, lambar Alhaji Khamis ne wanda suke mutumta juna, juyawa kawai yayi ya fita daga d’akin inda Sameera ta juyo kan Raihan ta wanketa da mari tace “Mamana abinda zaki saka min dashi kenan? Me na miki a rayuwa da kika zab’i hukuntani ta wannan hanyar?”
Dafe kunci tayi tana kuka zata durk’usa k’asa ta fizgota ta nufi toilet da ita, suna shiga ta mayar da k’ofar ta rufe ta kama Raihan da k’arfi ta zage mata dogon wandon had’e da pant d’in ta, kunya ce tasa Raihan ja baya tana rufe gabanta, wata harara Sameera ta wurga mata hakan yasa ta d’an kawar da kanta, ba zato ba tammani taji wani zafi ya ratsata da k’arfi sakamakon shigar da yatsa da Sameera tayi na kusa da manuniya, k’ara tayi lokaci d’aya kuma tayi shiru har wasu hawayen wahala sun zubo mata, fito da yatsan tayi ta kalleta sai kuma ta zauna dab’as a tsakiyar toilet d’in, ita gaba d’aya ma kanta ya kulle ta rasa taya zata iya fahimtar yarinyarta budurwa ce, ba zata iya kaita likita ba gaskiya saboda sanannun mutane ne su, hakan zai tab’a kima da kuma mutuncinsu, Raihan kuma d’aukar wandon tayi ta mayar ta sunkuya tace “Ammie, dan Allah ki daina kuka a kaina, Ammie zan sake samu wani mijin na aura, nayi miki alk’awari da idonki sai kin tabbatar da yarki bata watsar da tarbiyyarta da kika bata ba.”
A waje kuma yana fita Alhaji Khamis ya samu k’ofar masallacin ya tsaya, cikin nutsuwa Alhaji Khamis yace “Alhaji Abbas na fahimci duk abubuwan dake faruwa, idan zaka bani dama zan so na karb’awa babban d’ana *Baban gida* aurenta? Dan bai kamata a fasa d’aura auren nan ba.”
Kallonshi Abbas yayi sosai, hak’ik’a yasan Alhaji Khamis mutumin kirki ne mai sanin ya kamata da dattako, sai dai kuma baisan komai a game da d’an sa ba, duk lalacewar Raihan kuwa zai yarda yayi wannan gangancin? Ganin baice komai ba yasa Alhaji Khamis cewa “Nasan abune mai wahala, amma karka damu ka fad’a min abinda ke ranka, maganar aure tafi k’arfin wasa, Baban gidan bai tab’a aure ba, karatu ya saka a gaba, yanzu haka ma yana *Maroc* wurin karatu, amma shekara mai zuwa zai kammala ya dawo gida, sunan mahaifina ne da shi, wato takwaranka ne.”
Kallonshi Abbas yayi sai kawai yace “Ba damuwa Alhaji Khamis, ai hallaci ka mana, kasan yarana ka haifesu amma baka haifi halinsu ba.”
Take suka shiga masallacin yan mutanen da suka rage suka shaida d’aurin auren *Abbas Khamis Abbas* da kuma *Khadija (Raihan) Abbas Abdul rahaman* akan sadaki dubu d’ari biyu.
Suna fitowa daga masallaci ana taya juna murna suna tattauna yanda tariyar zata kasance, amma Abbas cewa yayi ai kawai tunda shi Khamis gobe ne zai tafi to kawai zai tafi tare da surukarshi, sannan a yau zai gama mata shirye shirye taje can ta samu mijinta, kuma duk yayi hakane dan ya kawar da ita daga gabanshi, dan ranshi b’acewa yake idan ya ganta kuma tana tuna mishi da abinda shi ma ya aikata, nan Alhaji Khamis ya kira gida ya sanar da iyalai, mahaifiyar Baban gida ta rasu sai kishiyoyi, hakan yasa babu wacce tayi murna da jin haka, dan su abinda suka hango ba wai dalilin auren da gaggawa ba, a’a, tarin dukiyar da mahaifin yarinyar ke da shi, mutumin daya mallaki jirage na kanshi, compagnie da masana’antu ba adadi, sannan uwarta ma jinin sarauta ce, wannan bak’in cikin yasa suka kasa farin ciki, saidai sunyi abincin sadaka kamar yanda mai gidan yace, dan in basuyi ba rai zai b’ace kasancewarshi mutum jajirtattace a gidanshi.
Baban gida ma da yaji musu yayi wa mahaifin nashi, amma dayake yana da zafi saiya balbaleshi da bala’i yace idan ya turo mishi yarinyar ya yankata idan ya cika d’an halak ne shi, haka yaja baki yayi shiru shima yana jiran isowar yarinyar.
*Ma’aruf* da kanshi ne ya shigo musu da abun kari, babu abinda Ma’arufa tayi tunani dan dama kusan kullum shi ke siyowa, ko da baya da kud’i ita zata bayar ya siyo, yana kallonta har ta gama cin indomie ta d’auki lemun daya siyo mai sanyi ta fita dashi tana sha, fatan alkairi ya mata har da cewa tayi sauri ta dawo fa, tana kan hanyar zuwa ta kira Abbas a lokacin an d’aura auren yana wa su Ammie bayani, ganin lambarta yasa shi barin waje ya d’anyi nesa da su, Harira data fito d’auke da jus jus d’in da zata kaiwa bak’in dake gidan ta ganshi yana amsa waya, tsayawa tayi ta lab’e ta kasa kunne tana sauraren shi.
Abinda taji kawai shine “Naji, mu had’u a inda muka had’u jiya, amma ki sani wannan uta ce had’uwarmu ta k’arshe dake.”
Tana ganin ya nufi wajen ajiyar motoci ta d’an fito daga lab’ewarda tayi ta aje jus jus d’in ta rigashi fita, yana fitowa ya d’auki hanya ita ma cikin sa’a adaidaita ta fito daga kwana, shiga tayi tace su bi bayan motar…
22/06/2020 à 17:26 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_21_
“Dan ubanka meye haka? Wallahi idan ka sake dukanta saina rama mata tunda d’an iska ne kai, Ammar meye haka? Zalincin ne ya motsa maka? Wannan wane irin haukane da iskanci? Me yarinyar nan ta maka da zaka kamata da duka haka?”
Cikin d’aga murya kamar zai fasa gidan yace “Ummy inba raini da iskanci ba ni Amna zata rainawa hankali? Na d’auke na kaita shagon Ilu amma dan iskanci a gabana zata tsaya kula wani bayan kuma tasan nine mijinta, akan me zata min haka? Laifin me nayi? Tana so ta nuna ni ba cikakken namiji bane ko me? Waccen d’in da me ya fini? Kyau? Ilimi ko kud’i? Ko kuma lafiya da girman jiki taga ya fini?”
Cikin hassala Ummy tace “Mijinta? An d’aura maka auren da ita ne? Kai bari ma na tambayeka? Ka k’addara an d’aura muku auren, kenan haka zaka mata wannan dukan tana matsayin matar taka?”
Zaro ido yayi yace “To me zan mata? D’aki zan sakata na dinga rera mata wak’a ina mata rawa dan na kwantar mata da hankali?”
Kallonshi Ummy tayi tace “In kuwa hakane lallai ba namiji bane kai, ba zaka tab’a zama jarumin namiji a gurin mace mai hankalin da tasan ciwon kanta, tun ranar da aka ce Amna ce k’addarar aurenka ta fad’a mata na fara mata kukan tausayi, dan indai har akayi kuskuren had’a ta da kai to babu makawa yarinyar nan tana daf da ajalinta.”
Take yaji wasu hawaye na son taho mishi, mahaifiyarshi ce data haifeshi take fad’a masa haka? K’ok’ari yayi ya mayar da hawayen ya kalli Amna yace “Kina ji ko? A dalilinki ne take fad’a min haka, ni kuma nayi alk’awari saina tabbatar muku da namiji ne ni.”