BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin zubo da hawaye ido rufe tsabar kunya tace “Ummy ban masa komai ba, kawai dai abinda na lura ya hora ni ne saboda sunansa da nake kira.”

Hannunta ta rik’e tana fad’in “Yi shiru to ya isa, kiyi hak’uri kinji, zai dawo gidan ya same ni ai.”

Magunguna ta fito wanda zata bata da allurar da zata mata da kuma ta d’inki, ko da Zeituna ta kawo mata soyayya k’wai had’e da dankalin turawa da tea had’in kauri ya ji madara, saida tsiya Ummy ta matsa mata ta ci sosai kafin aka shiga aiki, Zeituna uwar tausayi sai gashi ita ma kuka ita Hamna kuka, ba tace taji haushinshi ba kam, amma dai ta tausaya ma yarinyar irin wannan tashin hankali haka, ko ita data auri ubansa ai ko rabin wannan jigata ba tayi ba, maganin bacci Ummy ta bata tasha ba jimawa ya d’auketa cikin salama.

Ajiyar zuciya ta sauke mai k’arfi tare da girgiza kai, kallon Zeituna tayi dake share hawaye ta kece da dariya tace “Kinga aikin yaron naki ko? A hakane kuma baki son ganin laifinsa.”

Hanyar fita tayi tana fad’in “Muje to ki wanke fuska, tunda yau dai d’an naki yasaka ki zubar da hawaye.”

Cikin basarwa Zeituna tace “To aunty mutum da matarsa, sannan kinsan halin ‘yarki taurin kai ne da ita.”

“Duk taurin kanta sai kiyi duba da d’an mutum fa ya tsaga ya fito ta gabanta, amma a hakan ya mata wannan cin wulak’anci, me kike tsammani idan da budurwa ce? Da kenan gawarta ce muka wanke yanzu?”
Dariya dai Zeituna tayi dan gaskiya ta fita gaskiya yau kam.

Safiyar ta yau Jibril dake d’an alak’a dasu ne ya samu labarin rasuwar malam Rabi’u, Labaran ya fara fad’a ma maganar, cewa yayi zai je amma idan Hajiarshi ta amince, yasan kuma ba lallai ta amince ba shiyasa yaje da kanshi, ya jima yana bata hak’uri da bata baki kafin ta yarda su tafi, Labaran da Jibril da Jamil tare da Soueiba da Hajia suka tafi, Husseina ta so Hajia tayi zamanta amma tace to in mutuwa bata zamar mana wa’azi ba me kenan zai ladabtar damu? Haka suka je wajen gaisuwa daga nan kuma har suka je gidansu Mari ganin mamarta.

Jikinta yayi kyau yanzu fiye da da kam dan maganarta ma lafiya lau sai abunda ba’a rasa ba, sai Mari da suka samu tana kan sharholiyarta, ta k’ara mulmujewa tayi jiki sosai, da gani kuma kasan k’ugunta yanzun na magani ne, ta shiga shafe shafe tayi jawur kamar zabiya sai dabbara dabbara na musamman a hannayenta, ta k’ara huje a kunnenta barkatai abun har ya k’azamce.

Sanda suka je bata nan suna zaune ana ta gaisawa da hirar ya bayan rabuwa sai gata ta shigo tana waya, atamfa ce jikinta amma har gwara wasu kayan na kanti akan na jikinta, siket d’in yanda ya kamata kai kace bata iya tafiya, ya fito mata da bankamemen k’ugun nan kam har saiya baka tsoro, rigar kuwa duk rabin nonuwanta a waje suke sun matsu sunyi pam dasu, baya ma haka duk rabinshi waje yake dan haka ko bras ma bata saka ba, atach ne akanta babu kitso ta d’aure da ribom, kwalliya ce ta tashin hankali a fuskarta da gani kasan ko dai biki zata je ko kuma ta dawo ne, duk da ta ganesu sarai amma cike da wulak’anci ta wuce d’aki tana fad’in “Sannunku.”

Girgiza kai Jibril yayi ya d’an kalli Mamanta, daga kallon da yaga tabi ta dashi zai fassara maka abinda take ji game da hallayarta, sai yaji tausayinta ya kama shi sosai, da zata amince shi kam daya d’auketa sun tare a sabon gidanshi da zai koma, ko ba komai dai akwai alak’a tsakaninshi da ita. Ko da suka gama gaisuwa suka tashi dan komawa, sallama sukayi sosai suka fita, a soron gidan suka ji ance “Jibril.”

Kusan a tare suka juya dukansu, Mari suka gani da d’aurin k’irji na towel kalar pink, dukansu fita sukayi suka barsu, d’auke kanshi yayi daga gare ta, cikin wata shegiyar murya tace “Huda nace ko zaka kawo min ita idan an musu hutu ta zauna tare dani?”

Ba tare daya kalleta ba yace “Ba zai yiwu ba gaskiya, amma dai in aka sake sun zan turota tare da dreba ya kawota, zai kwana anan shima kwana biyu sai su koma tare.”

Da mamaki ta kalleshi tace “Ban gane ba? Kana nufin ko wata ba zaka bari ta min ba?”

Bai kalleta ba yace “Ba zai yiwu ba nace, sai anjima.”

Ya juya zai fita tace “In ka isa Allah ya tsine min, to me kake nufi dani? In haifi yarinyar a ciki na kace zaka min iko akan ta, Allah baka isa Jibril ko da k’arfi zan k’waci ‘yata.”

Juyowa yayi ya kalleta sama da k’asa yace “Ni ba sakarai bane Mari, da kin nutsu kin gyara halinki da Huda ta zauna tare da ke, amma a halin yanzu na kawo miki yarinyata mace mai shekara goma sha biyu a duniya, c’est très difficile Mari.”

Juyawa yayi ya fita me Mari zatayi sai kuwa ta fara nuna halin rashin kunya da fitsara, har k’ofar gidan ta fita da d’aurin k’irji ta shiga aika mishi munanan ashar, shege tsinanne bak’ar haihuwa ai duk shi ya lalata idan ya manta ta tuna masa, shine yanzu zai mata iko da d’iyarta to bai isa ba, su dai babu wanda ya kulata tuni sukayi nisa ma sai ita suka bari tana haukanta, sai dai yayi niyya ba zai ma kawo Huda ko da tayi kwana biyun bane, zai kira mahaifiyarta ya bata hak’uri tunda ita ma tana son ganin Huda, amma yasan inya kawota tana iya rik’eta hakan kuma zai haifar da tashin hankali, dan akan tarbiyar yarsa zai uya makata kotu ma ta rabata da ita har abada, dan yana mugun son yarinyar yana kuma bata kulawa, duk wani motsi nata a lure yake dashi da taimakon Jamila da yanzu take d’aukar yar kamar nata yaran, sai dai kawai k’addara da kuma yaran zamani da wani lokacin sai su fi iyayen da suka haifesu dubara ma, amma har yanzu yana addu’a Allah ya yafe masa abinda ya aikata a baya ya kuma shirya masa yaransa da sauran zuri’a.

Har azahar bai dawo gidan nan ba saida Ummy ta kirasa ta masa wankin babban bargo, dariya kawai yake mata yana cewa tayi hak’uri to taja wa yarta kunne ta dinga girmama shi, a k’arshe dai tace an k’i aja d’in ya jima bai kasheta ba, sai kusan k’arfe biyu da rabi ya shigo gidan da matuk’ar bacci a idonshi, kai tsaye d’akinta ya shiga ya sameta kan sallaya kwance dan zaman salla ma da k’yar take d’an azawa saboda d’inki hud’u Ummy ta mata, zaune yayi k’asa kusanta ya dafata yana fad’in “Ayyah beby sannu, ashe baki da lafiya? Kai amma wallahi banji dad’i.”

Ko kallonshi ba tayi ba bare ta amsa mishi, tallabota yayi ya tayar da ita zauna, da sauri ta rintse ido tace “Washh.”

Cikin dubara ta d’an zauna rabi da rabi yanda bata jin zafin sosai, shafa kumatunta yayi yace “Sannu kinji, me ya same ki ne haka? Waya tab’a min ke?”

Idonta cike da k’walla ta kalleshi, da Allah zai ara mata lokaci da cakumar wuyanshi zaatayi sai taji ya daina motsi, sai dai bata da wannan k’arfin a yanzu kam watak’ila ko a gaba, janye hannunshi tayi daga kan kumatunta ta tashi da k’yar ta nufi gado, wannan enveloppe da makullin ta d’auko ta cilla masa a jiki tace “Ka rik’e bana so.”

Mik’ewa yayi tsaye yana d’aukar kayan yace “Ban gane na rik’e ba? Naki ne fa.”

A k’ufule ta kalleshi tace “Shine nace bana so, ai kasan nafi k’arfinsu ko tunda ni ba ci ma zaune bace, sannan ubana ya d’auke min nauyin komai.”

Tab’e baki yayi ya aje mata kan gadon yace “Ni ma kuma idan nayi abu na bashi baya kenan har abada, ko ki rik’e ko ki jefa a kwandon shara ruwanki ne, ni ladar wahalarki ce na biyaki.”

Da wani mahaukacin mamaki ta bud’e baki tana kallonshi, ladar wahalarta? Me ya d’auketa to? Tana cikin tunanin taga ya fice a d’akin yana hamma, a hankali ta fita daga d’akin ta bishi d’akinshi daya shiga, ko da ya juyo ya kalleta yayi murmushi yace “Har kin fara nema na da kanki madame?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected