BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallonshi tayi tana dariyar jin dad’i tace “Ka zama *Abbana* daga yau?”
Gyad’a mata kai yayi yana murmushi, d’orawa tayi da “Kuma duk kana da kud’in siyan wannan abubuwan?”
Cike da tabbatarwa yace mata “Sosai ma, kuma ko da bana da saboda kiyi farin ciki ki wuce gori a idon jama’a ai ko bashi ne zan ci dan na siya miki.”
Cike da yarinta tace “Abba saniya nake so babba, kuma nafi son kalar ja tafi kyau mai manyan k’aho.”
Cikin dariya yace “Angama gimbiyar Abbanta.”
Wani dad’i ne ya kashe Huda daya sata fad’awa k’irjin shi ta kwanta luf tana k’ara goge hawaye, wata ajiyar zuciya ya sauke mai k’arfi, a hankali ya lumshe idonshi ya fata shafa kanta wanda yasha sabon kitso ya fito tsaf da shi sai walk’iyar mai yake, hakan daya faru kuma saiya zama kamar antsaga zuciyarshi an dasa mishi soyayyar yarinyar, take yaji k’aunarta na gauraya da jinin jikinshi, ba tare daya bud’a ido ba ya sumbaci kanta, cikin tausashiyar murya taji yace “Huda ki yafe min, nayi gaggawa a waccen ranar, duk laifi na na komai daya faru, mahaifiyarki ba da laifi ko d’aya.”
Ita dai da yau take jinta a k’irjin Abbanta yana shafata bacci ne ma ke sonyi gaba da ita, hakan ne yasa bata damu da me ya fad’a ba kawai ta sake yin shiru, ci gaba yayi da shafar kanta har yaji shirunta yayi yawa, yana lek’a fuskarta yaga ashe bacci harya d’auke ta, hak’ik’a mahaifiyarta ce tayi, daga kallon fuskarta kuma abubuwa dayawa ne suka ziyarci tunaninshi, ya zakayi da *Junaid, iyayenka ma, da ita kanta Maryama, sannan iyayenta ma da suka ganka*? Amma kallon fuskar Huda da yake sai yaji ya bashi k’arfin gwiwar tunkarar kowane irin bala’i da masifa, ‘yace dai gata ta zo zo duniya, tasha wahala kafin bayyanarshi ya kuma dan da ita, amma daga yanzu daya sani har zuwa lokacin da kowa zai fahimce shi ba zai bari tayi kuka ba, shafa kanta yayi ya sake sumbatarta yace “Wannan *alk’awari* na ne gareki.”
Ba tare daya d’auke ta daga kan cinyarshi ba ya tayar da motar a haka ya tuk’a suka isa wata alimentation, tsayawa yayi ba tare daya fito ba kawai ya sauke gilashin motar yace babbar leda yake so a had’a mishi ta kayan da suka san zasu birge yaro, saida ya siyo suka juyo dawowa inda suka bar Junaid, shi kad’ai ya samu zaune bakin dakali Maryama ta shiga dan kimtsawa, Junaid ne ya kirata a waya ta sake fitowa, fitowa Jibril yayi da Huda a hannu ya matsa daf da Maryama zai bata ita, murya k’asa k’asa tace “Baccin farin ciki ne take na ganin mahaifinta? Ko kuma baccin wahala ne?”
Da sauri ya sauke idonshi cikin nata idon da alamar tambayar me take nufi? A lokacin da zata amsheta ne tace “To ai naga kai idan har aka shiga mota d’aya da kai sai kayi b’arin ingantacciyar madarar da tana shiga mahaifa dole a tashi mutum da ita.”
Kallon wannan wace irin magana ce haka? Ya mata kafin shima yace “Huda, ‘Yata ce?”
Murmushi ta masa tace ” ‘Yar ka ce mana, a waccen ranar aka sameta, dalilin haka kuma na shiga karuwanci.”
K’asa ya kalla tare da saisaita murya yace “Ya fad’a min kuna shirin tafiya, amma dan Allah kafin ku tafi ki jira naje na dawo.”
Cikin makirci ta amsa mishi da “Karka damu zan jiraka, domin kuwa akwai matsalolin daya kamata mu warwaresu.”
Gabanshi ne ya fad’i ita kuma ta kalli Junaid dake waya da wanda yake so ya had’a shi da dreba tace “Zan shiga ciki na k’arasa shiryawa.”
Da kai kawai ya mata alama ta wuce ciki suma suka shiga mota suka d’auki hanya, gida Jibril yace ya aje shi, yana sauke shi kam d’akin shi ya shiga ya fito ya shiga motarshi shima, bai zame ko ina ba sai *Soura* mayanka.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Yana zuwa cikin takon rashin mutumci ya shiga hotel d’in, zuwanshi yayi daidai da Hamna na sakawa wani saurayi a cikin abokan ango lambarta a wayarshi, k’are mata kallo yayi, har zuciyarshi fa shi ya zo ne da niyyar ci mata uwar raina musu hankalin da tayi a gida, amma yana ganinta cikin ankon shagalin duka yan matan riga da siket ne jikinsu na less, amma yanda suka fitowa da da Hamna komai na jikinta saida yaji zuciyarshi ta buga, abinka ga mai yar k’iba k’irjin nan an fito dashi ya tsaya tsam-tsam, ga faffad’an k’ugun nan ya fito da kyau, d’aurin d’an kwalin dake kanta iya rabin kan kawai ya tsaya, inda manyan kitsonta na gashin doki (atach) ya kwanta a bayanta har yana kusan kaiwa a k’ugun, wani tafarfasa yaji zuciyarshi nayi, gani yake kaf mazan wurin surarta kawai suke kallo suna yabawa, jinjina kai yayi irin yana nufin zaki ci ubankin nan kafin yace ” Wato ni zata rainawa wayo?”
Daidai Hamna ta mik’awa saurayin wayarshi cike da jan aji zai karb’a idonta ya sauka kan boss, fad’uwar da gabanta yayi da d’aukar rawar da jikinta shima yayi yasa ta mantawa harta saki wayar bada gangan ba, saida taji fad’uwar wayar kuma tayi sauri ta kalli wayar ta rufe baki da hannu, zata sunkuya ta d’auka kuma Ammar na daf da kawowa, d’an girgiza kanta tayi a ranta tace “Wallahi wannan kallon rashin mutumci ne yake min, ba zan zauna ya kunyata ni ba cikin mutane.”
Ai saita mik’e ta kalli saurayin tace “Kayi hak’uri dan Allah.”
Fittt, ta kutsa cikin taron tana neman mafaka duk da saurayin na fad’in “Ba komai.”
Tsaye yayi gaban saurayin daya sunkuya ya d’auki wayarshi, kasancewar sun san juna yasa ya figzi wayar ta shi, ganin lambarta rau akan écran d’in daya fara tsagewa yasa shi goge lambar ya cilla mishi wayar, rashin sanin zai cillo mishi yasa bai rik’e ba wayar ta sake fad’uwa k’asa, rai b’ace saurayin yace “Ammar meye haka? Ya zaka fasa min waya?”
Gwa da gwa ya kalleshi yace ” Ita data saki ta fashe murmushi ka mata ka ce ba komai da yake mace ce ita, amma tunda ni gardi ne shine zaka nuna min karuwanci ko, to na fasa *Abdu* ci min uwa.”
D’aga hannu Abdu yayi yace “Allah ya baka hak’uri, wuce.” Ya fad’a dan yasan shi fa k’aramin aikin shine a wurin su zubar da kwadon rashin kirki, gashi dai mutum mai ilimi da aji amma wani lokaci kamar jahili.
Wucewar ko yayi ya ratsa mutanen suma, duk k’ok’arion shi na son ganota ya gagara, dan haka ya dafe k’ugu yana tunanin abinyi, duk da akwai maza wurin amma mata da iyaye sunfi yawa sai tarin yara, murmushi yayi ya nufi wajen mc dake sako baitoci, yana zuwa ya d’an mishi magana a kunne kamar abun arzik’i, hakan yasa mc d’in mik’a mishi amsakuwar (micro) d’in hannunshi ya tsayar da wak’ar dake tashi a wurin, Ammar kuma wayarshi ya ciro ya d’anyi danne danne kafin ya saita wajen sautin wayar ya jona a micro d’in, yana danna play sai ji kake
*Tatatatatatatatatatatata!!!* k’arar bindiga, ba mata ba da suka fashe da k’ara da ihu har maza wanda ke tsaye zaune yayi, wanda ke zaune kuma ya fad’o daga kan kujerar, yara ma ihu suka saka inda wasu kuma yaran ke ganin kawai nishad’i ne sai kuwa suke da tafi, lokacin da wasu suka rage tsayi ta hanyar durk’ushewa da yin kwance lokacin ne ya hango kankana da ita kuma tsoronta na ganinta da boss zaiyi, kallon mc yayi ya mik’a mishi micro ya kashe satin wayar tashi ya wuce wajenta, ta juya dan son ganin ina yake sai kuwa sukayi tozali.
Tsoron daya gani a idonta a lokacin ya sani da zai auna jininta zaiga ya hau, matsawa yayi daga gabanta fuska ba annuri yace “Wuce muje gida.”
Ita kam da a gida ne tasan zata samu masu ceto, amma anan? Kuma yace su tafi gida? Tab’idjam! Hayaniya ce ta kaure a wurin na son sanin abinda ya faru, ganin babu mai kulasu hakan ne ya bata damar saka kuka tace “Dan Allah yah Ammar kayi hak’uri ka bari har muje gida, a kan motona na zo fa.”