BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Had’e hannayenshi yayi yana mammatsawa yace “Ba damuwa, zanyi.”

A kauce ta kalleshi jin yace wani wai zanyi, ko me zaiyi? Oho! Banza tayi dashi kawai dan babu anfanin b’ata yawun bakinta a kanshi a yanda take gani, kallon fuskarta yayi yace “Ummy, dan Allah meye tsakaninki da Abba da har zai miki kishiya? Kishiyar ma kuma wai wannan yarinyar wanda ba komai had’a ki da ita zai ja miki ba sai zubar da aji.”

Kallonshi ita ma tayi tace “Na d’auka angama maganar nan, meye kuma na taso da ita? Kaga bana son tashin hankalin, aure ne za’a d’aura shi gobe, banda matsala da hakan, mahaifinka ya auri ko mace uku ce ma ya kawosu duk a goben, ni dai ina son zaman k’ark’ashin kulawarshi, dan haka wannan ba matsalarka bace.”

A tsanake ya kalleta yace “Ummy, ki fad’a min idan akwai laifin da kika masa? Ni zan masa magana ya fahimta, amma bai kamata ya miki kishiya ba a yanzu.”

Nuna shi tayi da hannu a zafafe tace “Kaga, ni dai a sani na ban masa wani laifi ba, ka daina maganar nan kawai idan ba so kake a fitar da uwarka ba a lokacin da za’a shigowa da mahaifinku amaryarsa ba.”

Mik’ewa yayi yana mayar da hannayenshi aljihu ya kalleta yace “Ummy tambaya nayi kawai ko akwai wani laifin da kika masa ne, dan ni a gani na a shekarun da kuka d’auka tare bai kamata ace kishiya ta biyo bayan haka ba.”

Tsaye ta mik’e ta nuna mishi k’ofa tace “Fitar min a d’aki na, kaje kayi duk abinda zakayi, amma ka sani wallahi idan ka ja min magana ba zan yafe maka ba, mutumin banza kawai, ni ce marainiyarka kenan zaka zo ka tsareni da maganar ko na masa laifi, idan ma na masa laifin saina zauna na fad’a maka? Ni kenan bansan ta yanda zan iya ji da matsalarmu ba har sai sakarai irinka ne zai mana magani, shi kaje ka tambayeshi mana idan kai marar kunya ne.”

D’aya hannunshi ya fito da shi ya kama yalwatattar k’asumbarshi yana shafawa, takowa yayi kusanta yana kallon idonta babu wani d’ar ko tsoro cikin taushin murya yace “Ummy, ko zaki iya tuna abinda ya faru muna da shekara goma sha shida a duniya ni da Amar? Mun samu matsala dashi akan riga, a lokacin Amar nada rigima sosai, ko abu nawa ne saiya nuna nashi ne ko yana son shi saboda yasan kowa zai goya masa baya, asalin rigar tawa ce, kuma ke ma kinsan haka saboda kinga alamar da nama tawa, amma sai kika rufe ido dake da duk sauran mutanen gidan kuka ce dole sai dai ni na hak’ura tunda nine babba, hakan ne yasa nima raina ya b’ace a cikin dare na yaga duka rigunan da reza, amma me zai faru? Washe gari Hajia ta mareni a fuskata ta zageni zagin da ko kare tayi wa saiya zubar da hawaye, ta kira ni d’an iska har ba adadi, ta kira ni shege munafiki mai bak’ar zuciya…”

Sunkuyar da kai yayi yasa yatsa d’aya yana share hawayenshi, ba tare daya d’ago ba yace “Zagin da yafi tsaya min a rai shine data kalle ni a gabanki a gaban idon mahaifina ta kira ni da *d’an Allah bani*, wai da tasan haka zan zama da ko da aka haifeni tasa an min allurar mutuwa, a wannan ranar ta fad’a ni, ni Ammar nine *annobar ahalinta*, zuciya nayi na fita farfajiyar gidan ina kuka, na wuni a wuri d’aya zaune da tunanin ko zan samu wanda zai zo ya rarrashe ni ya kwantar min da hankali, amma babu wanda ya zo kusa da ni, a lokacin mahaifiyata ce kawai nake ganin zata iya zuwa kusa dani kuma ta rarrasheni, ganin ke baki zo ba yasa ni naje har d’akin ki, Ummy me kikayi a lokacin?”

“Ina shiga kika rufe ni da wani fad’an wai na fita na baki wuri, haka kema kika sake kirana d’an iska mai ja miki magana, a k’arshe bud’a baki ki kayi kika ce wai na fice miki daga nan ba kya son gani na ko kad’an, Ummy kinsan meya hana ni barin gidan nan a wannan ranar?”

Ummy dake kallon yanda hawaye ke zuba a idonshi kasa amsa mishi tayi, dafe k’irjin shi yayi saitin zuciyarshi ya ci gaba yayi da cewa “Ummy *saboda soyayyarki ne*, ina ji a jikina kamar idan na tafi na barki a gidan Hajia zata ci gaba da k’untata miki, hakan yasa na hak’ura na zauna duk da zafin da nake ji a zuciyata, bayan faruwar hakan kwana shida na d’auka ina zuwa d’akin ki da nufin gaishe ki, amma sai kika ce ko amincin da nake nema miki ba kya so bare kuma gaisuwa ta, daga ranar ne ya zamana duk d’akin da zan shiga a gidan nan bana iya sallama, Ummy zan fara gaishe ki ranar da kika fara kallona kamar d’an da kika haifa, zanje wajen Abba.”

Yana fad’a ya juya ya fita da sauri sosai, fad’awa tayi kan gado dab’as kamar an turata, sai dai ta nemi hawaye ta rasa, maganganunshi ke dawo mata, kenan babu abinda yake mantawa? Zai fara gashe ni ranar dana fara kallonshi *kamar d’a*, kamar d’a? Ba ma d’ana ba? Tunawa da tayi yace zaije wajen lieutenant kuma tasan ba lallai su kwashe lafiya ba, dan haka ta mik’e ta d’auki wayarta ta fara kiran lieutenant, amma bai d’aga ba saboda wayar na silence yana ganawa da wasu manyan mutane, aje wayar tayi ta fito falo sam bata wani saka wani al’amarin a kai ba bare tayi tunanin halin da d’an nata ke ciki.

Yana fitowa ya samu Amna ta gaji da jiranshi, Hamna kuma ta d’auki moton ta tafiyarta, yana shiga taga ya had’a kanshi da sitiyarin motar yana sauke wata k’akk’arfar ajiyar zuciya, ya kusan minti biyar kafin ya d’ago ya jawo lotus d’in dake cikin motar ya goge fuskarshi da kyau, tayar da motar yayi suka fita daga gidan, saida suka fara tafiya ya kalleta wacce ita ma take kallonshi ganin sabon yanayi a tare dashi yace “Kinyi latti ko?”

Ganin idonshi jawur alamar kuka ba wai b’acin rai ba yasa saida gabanta ya fad’i, duk sai taji jikinta yayi sanyi tana son sanin meye damuwar, cikin taushin murya tace “Yah Ammar lafiya? Me yake faruwa?”

Kallonta yayi yana doka wani uban murmushi ya kuma kalli gabanshi ya ci gaba da tuk’i, har ta fidda ran zai mata magana sai kuma ta ji cikin wani yanayi dake nuna damuwar dake zuciyar mutum yana sakin murmushi yace “Amna meyasa zaki tambayeni me yake faruwa? Shin baki tab’a lura da abinda ke faruwa bane?”

Girgiza mishi kai tayi hakan yasa ya kalleta yace “Tunda kike a gidan nan kin tab’a jin wani Ammar Allah yayi maka albarka? Ko kuma zan fita kiji wani yace Allah ya tsare ko a dawo lafiya? Ko kuma kiji ance Allah ya taimake ka ko makamantan haka?”

Shiru tayi alamar zurfafa tunani da sauri yace “Karki ba kanki wahala, ba zaki tuna ba dan babu ranar.”

Ci gaba yayi da tuk’i harya sauketa, har zata shiga cikin makarantar yace “Ko na zo na rakaki ne? Kin makara fa sosai.”

Cikin sanyin jiki tace “A’a yah Ammar, kaje kawai, kai ma nasan ka makara a asibiti.”

Jinjina kai yayi alamar to ya fara k’ok’arin tayar da motar, kamar daga sama ko saukar ruwa ya tsinci muryar Amna cikin wani mugun yanayin da har k’asan zuciyarshi ta birgeshi tana fad’in “Allah ya kiyaye hanya yah Ammar, Allah ya baka abinda kaje nema, Allah ya tsare mana gabanka da bayanka, saika dawo.”

Tana fad’a ta d’aga masa hannu alamar bye bye ta shige ciki, da kallo ya bita yayin da yake jin wani farin ciki na nuk’urk’usar zuciyarshi, wani murmushi ya saki wanda shi kanshi ya manta rabon da yayi irinshi, ba tare daya daina murmushin ba ya ja mota sai asibiti.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Maryama da Iklima sun duk’ufa shirye shirye na gyaran jikinta da sauran abubuwan, kulawar da kakarta da kuma mahaifiyarta ke nuna mata kamar yanzu suka haifeta, haka ma Huda soyayya suke nunawa yarinyar sosai, wanda a yanzu Huda bata da aiki sai fad’in Abbanta Jibril wanda ya yanka mata saniya, yau ma asibiti suka shirya suka tafi aka cire mata robar da aka saka mata dan hana d’aukar ciki, a hanyarsu ta dawowa Iklima ke cewa “Yanzu Mari kin shirya haihuwa kenan da zaran kin shiga gidan?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected