BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Duk yanda ta so rufe jikinta kasawa tayi saida ya mata zigidir kamar yanda ta fad’o duniya, ba zato ba tsammani taji bakinshi a kan kan…
*Ma’assalm*
*Alhamdulillah*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI_ (sai Allah)
*6* _JIHADI_
*7* _K’ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K’ADDARARMU_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura…)_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
*AHALI NA*
©
*TAURARIN NIGER..*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
✪{T . N}✪️
https://www.facebook.com/Taurarin-Niger-100155928500614/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_38_
Da k’yar ya rabu da ita ya d’ago kai ya kalleta, hawaye sharkaf a fuskarta, kuka taka sosai kamar dukan tsiya ya mata, wurga idonshi yayi irin ya damu d’in nan tare da ja baya, juyowa yayi ya fito daga ban d’akin yana fad’in “Zo nan.”
Bata kula shi ba saida ya fita, rigarta ta mayar sannan ta wanke fuskarta ta fito, k’ura mata ido yayi harta zo ta zauna kusa da inda ya nuna mata, k’asa tayi da kanta bata da niyyar kallonshi, dan haka ya jawo farantin nan gabanshi ya d’auki wuk’a ya fara yanka lemun yana sha yana kallonta, lokaci lokaci yakan saci kallonta amma ta k’i d’agowa, aje lemun hannunshi yayi ya kamo nata hannun ya taso wa ida, zaunar da ita yayi akan cinyar shi hakan yasa ta rintse ido sosai, wuk’ar nan ya d’ora mata a wuya yace “Kalle ni.”
Tana bud’a ido taga wuk’a ce ya aza mata bata san lokacin data kwamtsa k’ara ba tasa hannayenta ta rufe fuska, lumshe ido yayi sanda siririyar muryarta ta daki kunnuwanshi, gaba d’aya jikinshi saida ya amsa, bud’e ido yayi ya aje wuk’ar ya d’auki lemu, janye hannayenta yayi yasa mata lemun a baki, amsa tayi tana sake sunne kanta, cikin taushin murya yace “Amna, kafin a d’aura aurenmu na d’auka ni dake zamu zama kamar abokan juna ne, amma gashi daga jiya zuwa yau naga sai k’ara tsorata dani kike, ba haka nake so mu zama ba Amna, ina so naga kin zama komai tawa wacce zan iya samun farin ciki a wurinki, ina so ki zama sirrin farin cikina, zan so ki zama maganin damuwata, Amna burina shine ki zama mai share hawaye na a duk sanda suka kwaranyo, Amna ki zama aminiyata kuma abokiyar shawarata, Amna *banda kowa*, sannan *banda komai*, babu wanda yake *kusanta ta*, ina so ki zama tare dani a kowane hali kuma a kowane yanayi, na sani Amna gidan nan ko kuma nace duk ahalinmu suna min kallon wani mahaukaci kuma marar kunya fitsararre marar tarbiyya, amma…amma…”
Sunkuyar da kai yayi yana furzar da wata zazzafar iska daga bakinshi, rawa muryarshi keyi kamar zaiyi kuka, zuciyarshi bugawa ta fara yi da sauri sauri, ya jima kanshi na kallon k’asa kafin ya d’ago yana kallonta sai dai basu had’a ido ba, bud’a baki yayi a hankali yace “Amna ni ba mahaukaci bane, ni ba marar tarbiyya bane, sannan ina da kunya da nutsuwa, duk abinda nake yi ina sane nake yin shi, da gangan nake yi da fatan samun kusanci a wurin iyayena, amma…”
Da sauri yasa bayan hannunshi ya goge yar k’wallar data taho mishi, da sauri ya turata gefenshi ta fad’a kan gado shi kuma ya mik’e tsaye, juya mata baya yayi yace “Har yanzu ban yi nasara, na d’auka zasu iya zama dani suji dalilin da yasa na zama haka, sun kasa fahimta har yanzu, babu mai iya gane ina jin yunwa ko na k’oshi, to tayaya ne zasu iya fahimtar abinda ke zuciyata, na zab’i na fara fito dashi ne dan kar ciwon zuciya ya kama ni a k’arshe na mutu, bansan ya zanyi da su ba.”
Juyowa yayi ya kalleta wacce ita ma ta k’ura mishi ido yace “Na gaza Amna.”
Ban d’aki ya shige ya barta zaune, k’urawa k’ofar ido tayi tana tunani da nanata abinda ya fad’a, ta d’an jima a haka kafin ta d’aga kafad’u tare da tab’e baki ta mik’e ta koma madafa, girkin data jima da d’orawa ta ci gaba daga inda ta tsaya, sai dai jikinta a matuk’ar sanyaye yake tana tunanin halin da mijinta ke ciki, meye damuwarsa? Meye tsakaninshi dasu Ummy? Meye ainihin abinda ke faruwa? Hak’ik’a ko ita kafin yanzu tana jin yana matsa mata ne sosai, tana ji babu kunya a al’amuransa, yana da k’arancin nutsuwa wani lokacin, kenan duk yana sane yake yi? To me yasa? Me yasa namiji kamar Ammar ke saurin zubar da hawaye? Bayan ita shaida ce akan jarumtarsa wacce ke tattare da masifa da bala’i, a sanin data mishi ko baka nemi jaraba da shi ba shi zai nemeka da ita, a sanin data mishi baya da saurin kasawa haka, mutumin ne dake tsaye tsayin daka wajen ganin ya ci galaba akan abokin karawarshi, to amma meya raunata zuciyarshi har haka? Wannan amsa ce daya kamata tasan amsarta, domin yanzu alhakin farin cikinshi na wuyanta ne, da haka ta k’arasa girkinta ta fito ta gyara wurin cin abincin, ta nufi hanyar da zata sadata da d’akinta taga ya fito daga d’aya d’akin cikin k’ananan kaya, amma abun mamaki bai yarda ya had’a ido da ita ba.
Ya nufi hanyar fita tayi saurin cewa “Yah Ammar.”
Tsayawa yayi ya juyo ya kalleta amma baice komai ba, shagwab’ar da fuskarta tayi kamar ta jarirai tace “Abincinka fa.”
Har ga Allah da ya so irin d’aurawer nan, amma yanayin da tayi da fuskarta saiya sashi sakin murmushi, domin kuwa abinda ya zo masa a rai ita ce Hamna, wato Hamna tafi k’warewa wajen shagwab’ar bubbuga k’afafu, ita kuma wannan gaba d’aya take canza fuskarta da yanayinta idan zatayi ta ta shagwab’ar, d’aga gira yayi yace “Kenan saida kika dafa abincin?”
Nufowa kanta yayi yana k’ok’arin cire belt d’in shi yana fad’in “Idan na rugurguza miki jiki gobe ba zaki sake bijirewa abinda na fad’a ba.”
Tana ganin ta durk’ushe ta had’e hannaye biyu tasa kusa tana fad’in “Dan Allah yah Ammar kayi hak’uri ba zan k’ara ba wallahi, idan kana so ma yanzu sai nake na zubar da wanda na dafa, dan Allah karka dake ni wallahi bana son duka a jiki na.”
Ganin ya kawo daf da ita amma bai cire belt d’in ba yasa ta rintse ido, yana zuwa yasa hannayenshi ya tallabota yana dariya yana kallon fuskarta, ganin bata bud’a idon ba tsabar tsorata da tayi yasa shi rumgumeta jikinshi yana fad’in “Amna yanzu fa na gama fad’a miki, shin idan ban zolayeki wa zan zolaya?”
Shiru tayi daga kukan da take rerawa ta bud’a ido ta d’ago kai ta kalleshi, yanda idonsu suka had’u ne yasa kowannensu jin wata wutar tsartsatsi ta bulbulo daga zuciyarsu, murmushi ya dalla mata ya tallabe fuskarta yace “Irin rayuwar da nake so muyi dake kenan Amna, mai cike da mutuntawa, farin ciki, annashuwa, k’aunar juna, tsokana da zolaya.”
Sunkuyar da kanta tayi a cikin k’irjinshi, shi ma kuma yana jin haka saiya k’ara kwantar da ita yana shafa kanta yana sauke mata numfashi a kai, sanyanyen turarenshi mai tayar da tsikar jiki da kuma kwantar da hankali take shak’ar k’amshinsa, luf tayi kamar mai son yin bacci tare da zura hannayenta ta baya ita ma ta d’an rik’e shi amma ba sosai ba, tunanin duniya take a daidai wannan lokacin.
Ammar dai, yayansu dake matuk’ar firgita lissafinsu, wanda basa fatan a kai mishi k’ararsu idan sunyi laifi, wanda ko babu laifin ma zai iya kunyataka ya tsinka ka a cikin jama’a, yau ita ce a k’irjin shi a matsayin mata? Bata tab’a kawo haka a ranta ba, dan a wajenta abune da ba zai yiwu ba, tayi tunanin tsaf zai nuna ta yace baya sonta, ta d’auka zai kalleta ne yace Allahya tsare shi da aurenta. Kai ita kanta fa taso tace bata son shi, amma ganin shi bai furta ba yasa ta yin shiru da fammun d’inta, dan idan har ta kuskura kalmar bana sonka ta fito daga bakinta, to tsaf zai iya tisata a gaba da tab’arya yace sai yaji dalili, wannan dalilin ne ita kuma yasa bata iya fad’a ba. Tana wannan duniyar taji ya d’ago kanta ya kalleta yace “Kin iya girki ne dama?”