BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Junaid ne yace “Muyi fata kawai d’ora shayin nan ba kullum zai ce sai mun d’ora ba, dan in kullum ne akwai matsala wallahi.”
“Shawara mai kyau.” Ammar ya fad’a daga bayansu, saida ya k’araso yace “Yanzu ku haihuwar da aka min ita ce ba zaku iya tayani farin ciki ba duk kuke k’ananan maganganu, sai yaran sun girma kuma kuce zaku dakesu wai sunyi ba daidai ba, to duk uban da bai tayani murna yanzu ba yace zai dakar min yara Allah shari’a ni dashi daga nan har tahatas-sara.”
Junaid ne yace “Allah ya baka hak’uri duniyar Amna, farin ciki mu ai mun fika dan mu aka ma haihuwa.”
Kallon jamil yayi yace “Jamalun (rak’umi, amma ya cuceka) shiga ciki ka samo k’atuwar tukunya da wake da shinkafa ka d’ora mana, zanje yanzu a samo mai yanda zai ishi kowa har ayi wanka dashi.”
Jamil take ya b’ata rai kamar zaiyi kuka, shi kuma meya had’ashi da dafa wake da babbar tukunya? A ransa yayi tsaki ya shige cikin gidan kamar ya kwamtsa ihu, kallonsu yayi su kuma yace “Kuyi da jiki mana kuna abu kamar yan mata.”
Amar ne ya kallesa a ransa yace “Yau ni naga ikon Allah, kuma ba damar magana wannan jaraba.”
Hannu ya tara musu yace “Mai makullin mota ya ban.”
Junaid da makullinshi ke tare dana d’aki ne ya mik’a mishi yace “Dan Allah yanda na baka motar nan lafiya ka dawo min da ita lafiya, kar kaje ka ja min jarfa ka sani zuwa ofishin yan sanda ko gendarmerie.”
Hararanshi yayi yace “Wato ga Ammar masifaffe jarababbe d’an masifa d’an bala’i wanda aka haifa ana tsaka da yak’in duniya na farko.”
K’wafa yayi ya shiga gidan Amar yace “To me ya rabaka da abinda ka fad’a d’in.”
Yana d’aukar motar ya fito da gudu da gangan yayi kansu hakan yasa su watsewa daga wurin a tsiyace, yana wucewa ya zuro kai ta k’ofa ya musu gwalo, kai dukansu suka girgiza, bai d’auki lokaci ba ya isa asibitin, ya samu Ummy da ma’aikaciyar dake aikin kwana a asibitin sun gama kimtsa Amna duk abinda take buk’ata sun mata tare da yaran, har an shiga da ita d’akin hutu ta kwanta tare da duka yaranta, su Hajia ne suka musu sallama suka tafi sai Husseina aka bari da Ummy su kwana anan, har Hamna zata shiga mota yace “Ki bari zamu tafi tare dake.”
A lokacin babu wanda ya iya tanka masa dan ba k’aramin shan kunu yayi ba, hatta Ummy sai taji tsoron ko da hararansa bare tace a’a, ita kanta Hamna ta tsorata sosai sai kawai ya shige ya barsu, ko da suka koma ciki Ummy ya tambaya abinda suke buk’ata, magunguna ta rubuta wanda zasu taimaka mata ya siyo ya dawo, lokacin sukayi saida safe suka fito shi da ita.
Tunda suka d’auki hanya babu mai magana sai Hamna dake addua’r Allah ya kaisu lafiya, saida suka kusa kaiwa gida ya taka birki ya jingina bayanshi a kujera, kanshi na kallon sama kamar ba zaiyi magana, tunda taga haka ta fara sallalami da duk addua’r da ta zo bakinta, tana tsaka da addua’rta taji muryarshi irin babu wasa a ciki yace “D’azu kinyi maganar yara uku, me kike nufi da abinda kika fad’a?”
Saida ta zaro ido tsabar tsoro kafin ta k’ank’ancesu a ranta tace “Yayin da wasu ke zuwa duniya lokacin wasu ke barinta, Hamna kuma ta wannan hanyar k’arshenki zai zo.”
Ba tare data kalleshi ba cikin b’ari da rawar murya tace “Ba..ba abinda na…ke nufi, ina tambayarka ne kawai.”
D’agowa yayi ya daki sitiyarin motar da k’arfi ya kalleta yace “Hamna na miki kama da sakarai ne?”
Haba wane mutum, ai sai ta fashe da kukan da babu hawaye tana girgiza kai tace “A’a, a’a yah Ammar, dan Allah kayi hak’uri ka kaini gida.”
Cikin tsawa yace “Idona zaki kalla ki min magana.”
Da sauri ta kalli fuskarshi sai kuma tayi k’asa da kanta tace “Dan Allah kayi hak’uri karka cutar dani.”
Bayan wuyanta ya shak’o ya matso da fuskarta gaf dashi yace “Ni zaki rainawa wayo Hamna, tun a waccen lokacin naga alamun ciki a tare dake, kwanciyar hankalin Ummy kawai yasa nayi shiru, amma yau ba zan barki ba sai kin fad’a min gidan uban da kika kai min ciki na.”
Yanzu kam kuka ta fara na k’warai sosai har hawayen na shiga bakinta sun jik’e leb’enta sharkaf, ganin bata da niyyar magana yasa shi sakinta ya kuma dukan sitiyarin motar da k’arfi har wata razananniyar oda ta fito, k’amewa ta sakeyi ya kalleta cikin jin haushi yace ” Hamna bana son dukanki, ke kad’ai ce bana jurar ganin cutuwarki, ki taimaka ki fad’a min ya kikayi da cikin nan Hamna, idan kuma kin zubar dashi ne kamar yanda nake tunani ki fad’a min.”
Kallonshi tayi cikin kuka jin ya fad’a mata mafitarta, sunkuyar da kai tayi tace “Kayi hak’uri yah Ammar.”
Lumshe ido yayi a k’alla tsawon minti biyar yana saita nutsuwarsa, saida ya daidaita kansa ya kalleta yace “Nayi hak’uri da me? Da cikin nawa da kika zubar?”
Da sauri ta d’aga masa kai alamar eh, rintse ido yayi ya yamutse fuska kamar zaiyi kuka, ya d’an jima a haka kafin ya bud’e ido yana sauke ajiyar zuciya ya kalleta yace “Hamna kinsan me zai hana ni sake miki wani cikin a yanzun nan?”
Fik’i-fik’i ta masa da ido ta kuma kallon titi ba tace komai ba, d’orawa yayi da cewa “Saboda yer uwarki ne, wallahi ba dan Amna ba da saina miki wani cikin naga abinda zai faru, ke ko da zaki zubar dashi ne saina k’ara miki wani sai dai mu tabbata a haka, amma…”
Kallon titin shima yayi cikin nutsuwa ya ci gaba da cewa “Ina ganin mutumcinta sosai, ina girmama al’amarin Amna har zuciyata, ina ganin k’imarta da darajarta a idona, ta kasance wacce tafi kowa kusanci dani, ta zauna dani sanda kowa ke kirana mahaukaci da ganin rashin tarbiyata, ta zauna dani ta fahimce ni ta shanye komai daga gareni, ta juri dukana ta shanye bak’ar maganata tayi dariya ga fitsarata, duk sanda na zalinceta bata tab’a fitar da k’walla a idonta ba sai dai tayi kukan da babu hawaye, duk sanda nayi niyyar dukanta bata guduwa sai dai ta tsaya wurin ta shiga bani hak’uri, wannan haukan nata na birge matuk’a. Ki sani yau kinci albarkacin yer uwarki, ba dan haka ba da sai kin gane kurenki na zubar min da ciki da kikayi, amma ko yanzu ma zaki gane kuren naki.”
K’wafa yayi mai k’arfin gaske tare da tayar da motar ya fara ja, suna tafiya ya juya ya kalleta, ganin har yanzu bata saki jikinta ba sai share hawaye take, wani uban rank’washi ya gaura mata akai yana fad’in “Shegiya ‘yar bak’in cikin tsiya, wai yaron ne da zaki haifo min kike jin haushi da hassada, a ganinki da ki haifo min shi gwara kin min asararshi, to Allah ya isa Allah saiya saka min wallahi dan ba yafe miki zanyi ba, mai bak’ar zuciya kawai.”
Tunda ya rank’washeta ta baje baki tana kuka, cikin jin haushi ya sake shirga mata k’ulli a baya yana fad’in “Dan ubanki rufe min baki, Allah kinci sa’a bana son dukanki da saina karya k’asusuwanki yau a garin nan.”
Hamna dai da yake muguwa ce k’ala ba tace masa saida suka isa gida tana wannan kuka kamar an mata mutuwa, a k’ofar gida ya tsayar da motar ya bud’a zai fito ita mata fito fuska rufe da hijabi, nufa yayi wajensu Junaid dake zaune suna hira suna aikin daya sa su, saida ta bud’e k’aramar k’ofa zata shiga dama wandon bacci ne gareta ta kalleshi tace “Ammar mugu Ammar azzalumi mai bak’ar zuciya, Allah ya isa Allah ya saka min duk cut…”
Da gudun bala’i ta k’arasa shiga ciki kamar zaki ya biyota ta haye sama, Ammar daya bita da kallo su Amar ne suka kwashe da dariya, kallonsu yayi a k’ufule yace “In ban muku wanka da tafasashen shayin nan ba ku ce ba namiji bane ni.”