BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_31_
*Kubra* wacce take kamar ‘ya ga Alhaji ce ta zo gidan dan shafe amare da angaye da lalle, d’aya bayan d’aya ta shafawa amaren kafin ta nufi b’angaren samari, d’akin Ammar ta fara turawa a hankali, cikin sa’a k’ofar ta bud’e ta shiga cikin sand’a, amma saita samu Ammar zaune akan sallaya ya tank’washe k’afafunshi, d’agowa yayi yana kallonta da mamakin shigo mishi d’aki a wannan lokaci, ita ma kallonshi take ganin bacci pal a idonshi alamar bai samu baccin ba, murmushi ta sakar mishi tare da matsawa kusanshi rik’e da robar lallanta tana fad’in “Ammar idonka biyu? Ai na d’auka zan samu kana bacci ne ta yanda zan wankeka da lalle.”
Saida ya kashe mata kyawawan idanunshi kafin yace “Wanda bai ga annabi ba kuma ina shi ina bacci?”
Wani murmushin ta sake yi tace “Hakane, to naga hannunka.”
Kallonta kawai yayi bai bata hannu ba hakan yasa ta d’ebo lallen ta nufeshi da nufin shafa mishi a kai, da sauri ya mik’e tsaye yana rik’e farar jallabiyarsa ya dakatar da ita yace “Tsaya aunty Kubra, kar muyi haka dake fa, me zaki min da wannan sai kace wani mata-maza?”
Gumtse bakinta tayi tace “Lalle zan shafa maka, kuma dai kasan sai an shafa maka ne kad’ai zai baka damar angwancewa da yarinyata ko?”
“A al’adarku ba.” Ya fad’a cike da gatsali kafin ya d’ora da “Nuna min ina ne za’a shafa sai ki ban na shafa da kaina, gaskiya bana so jikina ya b’ace da wannan abun.”
Tab’e baki tayi tace “Naga yanda za kayi wanka da ruwan lalle kam.”
Lallen ta d’ebo a hannu ta mik’o mishi, yamutsa fuska yayi kamar yaga kashi tare da saka yatsarsa manuniya ya lak’ato lallen ya kalleta yace “Ina zan shafa to?”
“A kai.” Ta bashi amsa, a hankali ya d’an shafa shi a saman gashi tare da kallonta alamar tambayar sai ina, saida taja tsakin jin haushi kafin tace “Sa a tafukan hannayenka.”
Shima juya idonshi yayi suka kalli sama cike da birgewa tare da cewa “Kamata yayi ace mata kawai ke wannan abun, amma maza abun ba tsari.”
Wanda ya d’an rage a yatsarshi ya murje a tafukan hannayen yace “To aunty Kubra ni ma dai na shiga lalle, shikenan?”
Juyawa tayi ta fita tana fad’in “Amaryarka dai ta shiga, amma kai kam har yanzu da saura, in baka sake shafa lalle ba ko na wanke ‘yar sai dai na kaita d’akin wani amma ba kai ba.”
Murmushin gefen labb’a ya mata ya bita da cewa “Aunty Kubra kenan, idan ma kinyi haka da kanki ne zaki dawo da ita ai, dan sai nayi abinda da kanku zaku je ku d’auko ta ku dawo da ita hannu na.” Tana fita ya fad’a ban d’aki ya wanke kanshi da hannayenshi ya fito ya rufe d’akin shi ya tafi masallaci.
Kasancewar yau ba zai fita da wuri ba yasa bai dawo daga masallaci da wuri ba, inda amare su kuma safiya na wayewa kowace ta shirya dreba ya kaisu gidan da zasuyi wunin k’umshi, da k’yar Ummy ta had’a kan Amna da Hamna suka tafi tare dan har yanzu ba wani shiri suke ba, kusan k’arfe *08:24* ya shigo gidan, kai tsaye falon Hajia ya nufi, Hajia na zaune Husseina gefenta sai Ummy dake rubuta duk abinda Hajia tace mata wanda zasu buk’ata saboda hidimar, shigowarshi tayi daidai da fitowar Zeituna daga madafa rik’e da robar yaghurt d’in da yasan Hajia kad’ai ke shan ta a gidan saboda rashin zak’inta, abun mamaki yau ma dai kai tsaye madafa ya nufa amma kuma yana fad’in “Uwa kin tashi lafiya?”
Cike da nutsuwa da kuma girmamashi ta amsa da “Ina kwana, antashi lafiya?”
“Lafiya lau.” Ya fad’a yana shigewa madafar, Zeituna na zuwa ta sunkuya ta bawa Hajia madarar, tana karb’a ta juya ta nufi madafar ita ma, a cikin ma’ajiyar (store, mangaza) kayan abinci ta ji motsinshi dan haka saita shiga sarrafa indomie da k’wai, yana fitowa da carton d’in lemu a hannunshi dan ya saka a fridge ya ganta, kusanta ya matsa yace “Uwa girki ake yi?”
Ba tare data kalli k’wayar idonshi ba tace “Eh, na ga baka fita bane, shine zan d’ora maka indomie.”
K’ura mata ido yayi yana kallo kamar mai tunani kafin yace “Uwa, meyasa kika damu da bani abinda zan ci ne? Alhalin ni ban buk’aci haka ba, kuma ina da wayon da zan iya nemawa kaina idan ina buk’ata? Meyasa?”
Har yanzu ma ba tare data had’a ido dashi ba saboda kwarjinin da yake mata tace “Yah Ammar ba saida wani dalili sannan zan kyautata maka ba, kawai naga kai baka neman abincin ne alhalin akwaishi, sannan kuma babu mai tambayarka ka ci ko baka ci ba, sannan ko da anbayar a kaiwa ‘yan uwanka babu mai cewa ku ci tare, shiyasa nake tunanin ko kai d’in irin mutanen nan ne da basu damu da cikinsu ba.”
Take Ammar yaji hawaye na neman taho mishi saboda abinda ta fad’a, matar uba na! Matar dana rainawa k’ura wai ita ce ta damu da cikinshi har haka! Shi kam wai me yayi wa iyayenshi ne har haka da zafi? A k’alla ba’a k’asara ba yafi shekara d’aya da rabi rabon daya ci abincin gidan nan idan ka cire ruwa lemu, amma sau d’aya Ummy bata tab’a tambayarshi ya ci ko bai ci ba bare tace ya ci, sake kallonta yayi yana murmushi yace “Nagode Uwa.”
Ita ma murmushin tayi duk da kanta na kallon k’asa tace “Ba komai.”
Juyawa yayi zai fita har ya kai k’ofa ya dawo tare da cewa “Uwa zaki min wani taimako?”
Kallonshi kawai tayi alamar tana saurare kafin yace “Dama su Amar sun shirya zama ne a k’ofar gidan nan ranar biki, kuma sunce dole zamu gayyaci duka abokanan mu, har ma mun riga da mun had’a kud’in da zamu bayar a mana girki, shine nake so na ware nawa daban dan ni ba anan zan zauna ba, ko zaki iya mana girkin da zamu ci?”
Juyowa tayi sosai tana kallonshi da mamaki tace “Amma yah Ammar me yasa kai ma ba zaka zauna tare da ‘yan uwanka ba? Ina ganin kamar hakan zaifi armashi tunda kai ma ka bayar da kud’in ka.”
Murmushi yayi cike da nutsuwa yace “A’a, ina so na ware kaina ne.”
Jinjina kai tayi tace “Shikenan, za ayi insha Allah.”
Da farin ciki yace “Yawwa uwa, amma fa bana so kowa ya sani.” Jinjina kai kawai tayi ta ci gaba da girkinta shi kuma ya fita.
Tunda Zeituna ta shiga madafa Hajia tayi tsaki tace “Aikin banza, ni bansan meye manufar yarinyar nan akan waccen yaron ba, Allah yasa dai ba jan hankalinshi take son yi ba suja min abun kunya.”
Da sauri Husseina tace “A’u’zu billahi, haba Zeeya’atu, me yasa zaki fad’i haka kema kamar wata k’aramar yarinya? Dan Allah ki dinga kyautatawa mutane zato, kuma idan ita kince baki san halinta ba duk da shekarun data kwashe tana miki bauta, ai shi Ammar kinsan me zai iya yi da wanda ba zai iya yi ba.”
Wani d’an iskan kallo ta mata tace “Ina ce dai bansa dake a maganata ba, to akan me zaki tsoma mi bakinki? Kuma da kike fad’in haka ke kinsan halin Ammar d’in ne? Yaron da rashin kunyarshi ta bunk’asa ta yanda har gaban iyayenshi zai iya fad’in abinda yake so, shine kike so na kyautatawa zaton? Ke zaki iya rantsewa cewa Ammar baisan ‘ya mace ba?”
Girgiza kai tayi tace “Allah ya shiryaki, amma ni dai har zuciya ta na yarda da Ammar, shi kawai yaro ne mai k’iriniya mai kuma fad’in gaskiya duk a yanda ta zo, sai dai kar kowa yaji dad’i amma hakan bai dame shi ba.”
Hararanta Hajia tayi ta mik’e ta nufi k’ofar fita tana fad’in “Shiyasa na tsani ina zaune a zo duk a cika min falo, inba sa ido ba ga d’akinki ki zauna mana.”