BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

D’auke hannun yayi ya k’ara gyara zama ya k’ura mata ido yace “Amna, yau gani ni dake a d’aki d’aya a matsayin mata da miji, wannan wani al’amari ne daga ubangiji, domin kuwa a rayuwata ban tab’a tunanin zaki zama matata ba, sai dai ina farin ciki da kasancewarki matata d’in, dan zan iya cewa ko Ummy data raineku bata kaini saninku ba, yarinyar kirki ce ke, dan haka ina fatan Allah ya bamu zaman lafiya.”

Cikin sanyanyar murya tace “Ameen.”

K’arawa yayi da cewa “Amna, nasan kuna zuwa islamiyya, zan iya sanin zurfin karatunki?”

Ba tare da sun had’a ido ba ta fara mishi bayanin matakin karatunta, kallonta yayi yace “Amma me yasa baki fara karanta arba’una hadisi ba har ki fahimce shi sannan ki fara bulugul maram? Duk littafin hadisin da zaki karanta idan baki karantashi ba ba zaki fahimci abubuwa dayawa ba, domin kuwa wasu malaman sunce gaba d’aya kafatanin musuluncin yana dunk’ule ne a cikin hadisai k’waya talatin, kuma wad’annan hadisan guda talatin suna cikin littafin arba’una hadisi, yayin da wani malamin shi kuma yace ai gaba d’aya addinin ma yana cikin hadisi guda d’aya ne tak, kuma wannan hadisin shima yana cikin littafin, kinga kenan indai har kina so ki fahimta zaifi miki ki fara dashi, idan kikayi nasarar kammalashi saiki fara da muwadd’a, kin gane?”

A hankali ta jinjina kai alamar eh, mik’ewa yayi tsaye yace “Ki d’auko ledar ce ki juye abin ciki a faranti.”

Mik’ewa tayi ita ma ta d’auko ledar shi kuma taga ya fita, ita ma fitowa tayi inda ta tabbatar nan ne madafa ta shiga, d’auko faranti tayi da cup biyu ta dawo, har ta juye ta zuba komai shiru bai dawo ba, bakin gado ta zauna tana jiran ya shigo taji yanda zasu k’are dashi, ai kuwa yana shigowa ta kalleshi lokaci d’aya ta sauke idonta k’asa, farin dogon wando ne jikinshi na zallar kad’a da farar singlet, saida ya aje wayarshi a hannu ya k’araso yana fad’in “Wai ke me kike nufi? Kunya ce kike ji? Ina ce dai tare muka rayu gidan nan, kin sanni tun lokacin ina yawo da gajeran wando, haka nima na sanki tun ina saka miki wando da kaina, to kuma miye na wannan nok’ewar, dallah tashi ki canza kaya ki zo ki ci abinci cikinki yayi nauyi, idan ba so kike ki b’ata min rai ba yanzu na karya miki k’afafu.”

Tashi tayi da sauri ta nufi wajen kaya ta kuma nufa ban d’aki, ganin duk ta diririce yasa ya kama hannunta har ban d’aki, gashi dai sun shigo kuma babu alamar zai fita, cire mata hijabin jikinta yayi da d’an kwali ya jefosu kan gado dan bai rufe k’ofar ba, juyata yayi ya kama zip d’in rigarta ya cire, sake juyota yayi ya kama rigar zai zageta ta k’asa, da sauri ta d’an rik’e rigar tana kallonshi a tsorace, kallonta yayi gira a had’e yace “Meye? Amna kina so na ci uwaki ne a daren nan?”

A hankali ta girgiza masa kai idonta har sun cika da k’walla, ko a jikinshi sai ma kama rigar da yayi ya zuge mata ita ta k’asa, sunkuyawa yayi ya fitar da rigar daga k’afafun ta ya d’ago, Amna da tuni tasa hannayenta ta rufe jikinta ta rintse ido, kamar daga sama taji yace “Wow, ‘yar k’anwata ce ta zama haka? Lallai kun girma, gobe dole naje na yiwa kakarku godiya, domin kuwa ta min zab’in daya dace dani, kamar tasan irin yanda nake son matata ta kasance.”

Sunkuyar da kanta ta sake yi shi kuma bai kula ma da tsiyar da take ba, rumgume hannayen shi yayi a k’irji yana k’are mata kallo, duk da ta rufe abubuwa dayawa amma bai hana shi gane wasu abubuwan ba shima, fad’in k’ugunta da cikinta yasa mazaunanta suka zama masu d’aukar hankali, fuskarta ya koma kallo d’an k’aramin bakinta da kurmin idonta, wata tausassan dariya yayi a daidai lokacin Amna ta gaji da yin shiru ta bud’a ido a hankali, suna had’a ido ta sake rufe ido ta juya baya, hakanne ya bashi damar kallon kayan da suke d’aukar hankalinshi, jefo rigar yayi bata ko sauka akan gadon ba, rumgume ta yayi ta baya yasa hannun dama yana shafa mazaunanta, har ga Allah inhar zai fad’i gaskiya a lokacin daya ruk’unk’umeta saida yaji yanda jikinta ke rawa, amma kuma tsikar jikinta duk ta tashi, dan kar ya saba mata da tsoronshi yasa ya taushe abinda yake ji a lokacin, sakinta yayi yace “Maza kiyi wankan ki fito ina jiranki.”

Bata iya cewa komai ba saida taji ya rufo mata k’ofar, ajiyar zuciya ta sauke idonta na zubo da hawayen da suka mak’ale, da k’yar ta iya wanka ta fito, nan ma ta sameshi kwance akan gadon kamar jiranta yake, saukowa yayi ya bud’a wajen kayanta ya shiga bincika, wata riga ya samu iya gwiwa tsayinta fara k’al tare da wandonta a jikin rigar, d’aukowa yayi ya juyo gareta tana zaune tana shafa mai ya rufe robar man yace “Kina shafawa ne saboda jikinyi kiyi tsantsi na kasa kama ki da kyau, muguwa.”

Ita dai k’ala ba tace ba sai turare daya d’auka yana ta fesa mata har saman kai da bayanta saida ya feshe, mik’ar da ita yayi tsaye ya cire wandon daga rigar ya durk’usa k’asa irin dai yanda ake wa yara in za’a saka musu wando, k’in d’aga k’afar tayi hakan yasa shi d’agowa ya kalleta, cikin razananiyyar muryarta tace “Dan Allah yah Ammar.”

“Dan Allah me?” Ya fad’a ba tare daya daina kallonta ba, sake marairaicewa tayi tace “Zan saka da kaina, kayi hak’uri.”

Tsaki yayi yace “Malama d’aga min k’afar ki kafin na tsagaki gida biy…” Tun bai k’arasa fad’a ba ta d’an d’aga k’afa a hankali ta zura, kasa d’aga d’aya k’afar tayi ta fashe da kukan shagwab’a tace “Dan Allah yah Ammar ka barni zan saka, wallahi ni…”

Tsaye ya mik’e yace “Ke me?”

Bayan hannu tasa tana murza ido tace “Kunya nake ji wallahi.”

“Kunya?” Ya fad’a da k’arfi, ta hudar yatsunta taga yana k’ok’arin kwance d’aurin zariyar wandonshi yana fad’in “To bari na tub’e nima ki ganni sai ki daina jin kunyar, kinga kenan anyi 1-1.”

Da saurin bala’i ta sunkuya ta rik’e hannayenshi tana fad’in “Yi hak’uri yah Ammar dan Allah, ba sai ka cire ba.”

Kallonta yayi ya tab’e baki inda ta k’urawa fuskarshi ido, tunani take wai haka kowane ango keyi a daren farkonsa? Ko kuma ita ce amaryar da tayi wannan rashin sa’ar? Ita kam da zai barta ta kwanta ta huta da taji dad’i, amma bata ga alamar hakan ba a tare dashi, yana cikin d’aurawa yaga irin kallon da take masa, ba tare da sanin abinda take tunani ba yace “Tunani kike wannan wane irin daren farko ne?”

Girgiza kai tayi ta sunkuya cike da dubara ta saka wandon nan dan dama tana sanye da rigar wanka, tana tunanin yanda zata saka rigar cikin sa’a shima saiya zauna gaban farantin data zuba naman nan, da sauri ta saka rigar ta cire waccen ta d’auki hijab ta saka, juyowa yayi zai mata magana yaga ta saka hijab, kallon da yake mata ne ya fahimtar da ita me yake nufi, “Ki cire shi ko na ci uwaki.” Tasan ko magana zaiyi abinda zai fad’a kenan, dan haka ta rufawa kanta asiri ta cire ta aje ta zauna, kamota yayi ya zaunar da ita kan k’afafun shi ya d’ebo naman ya saka mata a baki, tun tana jin kunya tana sunkuyar da kai har ta daina tana karb’a, tace ta k’oshi tayi magiya ya barta haka amma yace ta k’oshi sosai ko ta iya…(al’amarinka ya fara damuna), haka suka kammala suka sake tsabtace kansu kafin suka kwanta, duk da tayi nesa dashi saida ya mirgino ya rumgumeta ta baya ya d’ora hab’arshi a wuyanta ya zagaya hannayenshi ta bayanta, kamar wanda za’a rabashi da ita haka ya rik’eta sosai, Amna dake jiran taji abinda zai faru sai kawai ji tayi numfashinshi ya sauya alamar bacci ya d’auke shi, saida ta k’ara d’aukar wani lokacin kafin ta iya samu ita ma bacci ya d’auke ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected