BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cike da gadara tsohuwar tace “To, kashe waya.”

Cikin sanyin jiki Zeinabu ta datse kiran ta sake kiran lambar colonel, yana ganin lambar ta yayi murmushin da ba kowa zai iya gane murmushi yayi ba ya d’auka, cikin wani irin amon murya da ba zaka fahimci yanayin da mai ita ke ciki ba yace “Ai na d’auka ba zaki kirani ba, ashe dai ina da rana ta.”

“Ni ba abinda yasa na kiraka kenan ba, na kira ne na fad’a maka Inna ta kirani yanzu, bansan dalilin daya hanaka cika alk’awarin daka d’auka ba a wannan watan da har ta kira ni take k’ok’arin tayar min da hankali.”

Daga b’angaren shi ya amsa da “Kin kira ne kenan dan ki min fad’a ko me? Saboda ke ce uwata zaki tsareni kina fad’a min maganar nan.”

Ita ma a hassale tace “Amma ai kasan kai ka d’auki alk’awari ko? Dan haka dole ka cika.”

“Idan na k’i fa? Dukana zakiyi? Wai ko dan kinga bana kusanki ne zaki nemi ki min iskanci?”

Murmushi tayi kamar a gabanshi tace “Ba ma zaka yarda ba wallahi, tunda ka fara dole ka kai k’arshe tunda laifinka ne koma menene.”

Wai, colonel Hussein da yake ji kamar ya ganta gabanshi ne ya harzuk’o yace “Laifi na? Laifi na ma kike cewa? A waccen ranar ni nace kiyi abinda zai tayar min da hankali? Ko kuma tursasaki nayi? Ba da amincewarki komai ya faru ba?”

K’asa tayi da ta ta muryar tace “Duk da ba tursasani kayi ba ai ba kana nemana na amince maka ba, sannan bani na ce ka kirani inda kake ba, da kuma na zo kaga zan tayar maka da hankali me ya sa ba kayi gaggawar korata daga wajenka ba?”

D’orawa tayi da “Duk kai ka ja mana wallahi, ba dan kasa tsoron Hajia a ranka ba da yanzu muna rayuwa cikin salama, amma tsoron wanda baida wutar da zai samu ya saka mu sai aikata laifi muke akan wani laifin.”

Rintse ido tayi saboda jin k’arar ya bugi wani abu da yake nuna mata da ita ce a kusa da ita ya kaiwa wannan haura, datse hak’oran shi yayi ya rasa bakin magana, ina ma zai ji an kawo masa hari ta baya ko ya samu damar huce wannan haushin, jin baiyi magana yasa tace “Ni duk ba wannan ba, kayi azamar turawa Inna kud’in ta kamar yanda kukayi da ita, dan ni dai ba zan so asiri na dana yarona ya tonu ba a wannan lokacin, gaskiyar magana kenan.”

“Kutumar bala’i.” Inji colonel a cikin zuciyarshi dan har yanzu ya kasa sakin hak’oran shi, “Wannan ma ai raini ne, Zeinabu umarni ne take bani ko me? Ni? Ni? Ina!” Buga wayar yayi a bango ta baje tare da kai wa bangon naushi, Zeinabu dai ta fad’i abinda ke ranta ta kashe waya ta dawo falo.

Jibril ne a d’akin kakarshi bayan ya gama cin abinci suna hira, kallonta yayi da fara’a a fuskarshi yace “Yar tsohuwa, insha Allahu idan aure na da Amna ya tashi da kaina zan tuk’aki ki kaini wajen dangi Baba, dan wallahi ina so na gansu sosai.”

Tunda yayi maganar nan ta had’e fuska tayi shiru, jin shirun yasa yace “Hajia, wai a wane gari dangin mahaifin Baba suke? Na gaji da tambayar Umma akan wannan.”

Ba alamar wasa ta kalleshi tace “Kenan ni ce yanzu zaka dama? Malam tashi ka fitar min daga d’aki.”

Da mamaki ya kalleta yace “Hajia, kema damuwar ce kamar yanda Umma ke damuwa a duk sanda na mata magana makamanciyar wannan?”

Cikin d’aga murya tace “Ban sani ba Jibril, kuma in har baka son gayyato fushina to kayi gaggawar janye wannan k’udirin naka na son ganin dangin mahaifin mahaifinka.”

Mik’ewa yayi da tsantsar mamaki yace “Saboda me? Meyasa Hajia baku so ana…”

“Na ce ka fita.” Ta fad’a da k’arfin gaske, juyawa yayi jiki a sanyaye ya fita yana tunanin meke faruwa, fitowa yayi k’ofar gidan da tunanin shiga motarshi daya bari anan, Junaid ya had’u da shi zai shigo hakan yasa ya tsaya ya fito suka gaisa, Jibril ne yace “Na ga yau sai wani farin ciki kake mutumina, ko dai Maryama ta amince ne?”

Wani murmushin ya sake yi yace “Bata amince ba, amma dai na gano hanyar da zanbi nasa ta amince.”

“Wace hanya kenan?” Ya tambaya da zumud’i, da murmushin gefen labb’a yace ” *Zan je garinsu, sannan na shirya tsakaninta da mahaifiyarta da sauran danginta.”*

Da fara’a Jibril yace “Eh to kuma fa ka zo da dubara, kana shirya tsakaninsu zaka ga ta amince kosu su amince da kai.”

Kallonshi yayi yace “Amma dai zaku rakani ko?”

Zaro ido yayi yace ” Ni da wa?”

Hararanshi yayi yace “Kai da zaratan ‘yan uwa na mana.”

“Har da Ammar?” Cewar Jibril, ba wasa yace “Har da shi mana, ai watak’ila ma ya mana anfani fiye da kai, dan in mukayi sa’a muka had’u da wani tsagera a cikin dangin mai taurin kai shi zai mana maganinshi.”

Juyawa Jibril yayi zai nufi motarshi yana fad’in “Shikenan to sai kuje babu ni.”

Da sauri ya rik’o shi yana dariya yace “Kai haba daga wasa, kai fa zaka nuna mana hanyar ma tunda ai kasan hanyar *Gouré*.”

Cak ya tsaya ya juyo yana kallon Junaid, Goure, wannan yarinyar? Tana nan har yanzu? A ina take? Ina zanje na sameta? Rik’e hannun Junaid yayi yace “Da gaske kake? Yaushe zamu tafi?”

“Eh to, ni ko gobe ma zan iya tafiya, amma ka bari mu fara jin ta bakin su Ammar da Amar.”

Hannunshi ya kama zuwa cikin gidan yana fad’in “Muje ciki muyi magana da Ammar yana nan, Amar idan ya shigo zamu fad’a mishi kuma kasan ba matsala zai bamu ba.”

Wucewa sukayi ciki Junaid na fad’in “Wai duk wannan saurin na miye haka? Kamar wanda zaije ganin tashi budurwar.”

Wani murmushi Jibril yayi, dan haka kawai ya ji kamar ana fizgarshi da yaje garin, yana so ya Allah ya sake had’a shi da yarinyar nan, suna zuwa suka saka Ammar tsakiyarsu Junaid ne yace “Babban yayanmu, dama wata alfarma muka zo nema, dama yarinyar nan da nake so ce ta fad’a min garinsu, to akwai yar matsala tsakaninta da iyayenta, shine nayi shirin tafiya neman aurenta wajensu tare da shirya tsakaninsu, to bana so ne naje ni kad’ai gaskiya, nafi so muje tare da ku dan su san ni d’an dangi ne.”

Ammar da hankalinshi ke kan waya saida yaji ya kai aya kamar mai ciwon haure yace “Ina da abinyi.”

Yana fad’a kuma ya mik’e ya shiga d’akin shi, Junaid ma ya mik’e yana tab’e baki sai ga Amar ya shigo, nan suka fad’a mishi kuma kamar yanda suka sani dama ba zai basu matsala ba, shirya yanda tafiyar zata kasance sukayi kafin kowa ya nufi d’akin shi.

*Zanyi magana, amma ba yanzu ba.*
03/06/2020 à 23:33 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

_*MASOYA NA*_

_Bismillahir rahamanir rahim_

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_6_

Ma’arufa ce da Ma’aruf a d’aki kowa da wayarshi yana dannawa, kwance take akan katifa mai tufun gaske shi kuma tashi katifar bata da maraba da bargo, kallonta yayi yace “Ke wai kin fara shirin tafiyar ne gobe ko kuma kina nan kina jan jikin?”

Ba tare data kalleshi ba tace “Ba gobe zan tafi ba.”

Ba tare daya daina kallonta ba yace “Saboda me?”

Kai tsaye tace “Saboda akwai wasu kud’i da Labo zai bani gobe idan ya zo, kuma ina so na shiga kasuwa na siyo sabbin yadin da za’a min sabbin riguna dogaye, tunda waccen gurguwar tace mutumin ba wai harkar matan banza yake ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected