BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali *Abbas* ya d’ago ya kallesu cikin nutsuwa da girmamawa yace “Abba, Umma, sam banyi tunanin wannan maganar zata iya rasa muhalli a zuk’atanku, Abba, ko fa ubangijin daya hallicemu baya kamamu da laifin da waninmu ya aikata, ina ganin kamar rashin adalci ne da kuma dacewa ace zamu hukunta *Abdul Malik* akan laifin da mahaifinshi ne ya aikata, duba da lokacin da abun ya faru ko kanshi bai sani ba, namiji ne shi ba kuma lallai yayi halayyar mahaifinshi ba, zamu iya cewa mu shaidane akan hallayarshi, bai kamata mu hanashi auren Raihan ba in har suna son junansu, ko ‘yar uwarshi *Husna* ta samu miji tayi aure a dalilin rabin rayuwarta da tayi a gidan nan, ni da hannu na na bayar da aurenta Abba, shin kuna ganin ya kamata ace mu mun hana auren d’an su da ‘yar mu saboda tunanin abinda mahaifinshi yayi? Bai dace ba hakan iyayena, kuyi hak’uri ku sawa yaran nan albarka, hak’ik’a idan kuka ce baku yarda ba za’a fasa dole, amma hakan ba zai mana dad’i ba.”

A hankali Sameera tace “Gaskiya ne Abba, kuma na ga ko shi kansa Abban ai mun yafe masa laifin daya mana, kuma kuyi hak’uri ku yafe masa sannan ku manta da baya, duba da mutumin nan yanzu baya raye a doron duniya.”

Kallon juna Abba da Umma sukayi kafin Abba ya sauke ajiyar zuciya yace “Shikenan, mun amince, amma abisa wani sharad’i guda d’aya.”

Sameera ma da Abbas kallon juna sukayi kafin Abbas yace “Wane irin sharad’ine wannan Abba?”

Ba alamar wasa yace “Sai in kun amince za’a yi wa yaron gwajin cuta mai karya gwarkuwar jiki da ma sauran cututtuka masu had’ari wanda akan iya d’auka ta hanyar mu’amula.”

Dafe kai Abbas yayi yana tunani, yasan halin gogon nasu in har basu amice ba to za’a fasa ne, dan haka ya d’an kalli Sameera wacce ita ma take kallonshi kafin ya kallesu yace “Shikenan Abba, mu ma mun amince.”

“Shikenan, Allah ya tabbatar da alkairi.” Cewar Abban, da “Ameen.” Suka amsa da shi.

Sai Abba daya mik’e zai fita daga falon yana fad’in “A dole wai sai an raba mutum da matarsa, ni ina son amaryata amma kuke son saita min kishiya.”

Dariya sukayi sai Umma da tace “Shi ya sa zanfi kowa farin ciki idan haka ta kasance, dan ko ba komai na rabu da kishiya d’aya.”

Suma mik’ewa duka sukayi suka nufi b’angaren nasu Abbas, masha Allah falon ya had’u iya had’uwa, gashi duk yaran dake d’akin kowa harkar gabanshi yake amma cikin nutsuwa, sai Raihan dake zaune kan kujera da littafi tana karatu, sai kuma Abdul dake gefe tare da k’aninshi *Jabir* suna danna wayoyinsu, duka zaune sukayi kafin Sameera tace “Ku tashi kuje ku kwanta dare yayi.”

Kusan duka yaran suka amsa da “Ok Ammie.” Mik’ewa sukayi inda kowa ya nufi nashi d’akin, Raihan ma tashi tayi sai Sameera ce tace ” *Mamana* zo nan.”

Cikin sanyi jiki da nutsuwa wanda ya zama halitar yarinyar ta taho ko kallon idon mahaifiyarta ba tayi ba harta zaune kusa da ita, Abdul ma da Ameer zasu mik’e Abba yace “Kai Jabir kaje, Abdul ka zauna zamuyi magana.”

Cikin tsananin fad’uwar gaba da fargaba ya zame ya zauna k’asa duk da Abbas yace ya zauna inda yake, shiru falon ya d’auka kafin Abba yace “Abdul, abinda yasa nace ka zauna dama ba wani abu bane, ni da iyaye da kuma mai sunan Mamana (Sameera) munyi wata shawara akan ku kai da Raihan, kunsan ance abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutse ba zai hango ba, to duba da hakane yasa muka fahimci kamar da wani abu tsakaninka da Raihan, shi ya sa na ce bara mu tambayeku muji ko kuna son junanku?”

Tsaro ne matuk’a ya bayyana a fuskar Raihan duk ta zaro ido, yayin da Abdul zufa ta fara tsatsafo masa saboda jin abun banbarak’wai, wasu kirce-kirce ya fara ya rasa amsar da zai bayar, hakan yasa Abba cewa “Ka yi magana mana Abdul, ba za’a tauyeka ba ai.”

Shiru ya sakeyi gabanshi na fad’uwa, Abbas ne yace “Abdul.”

A hankali ya d’ago yace “Fad’a min gaskiya, kana son Raihan?”

Raihan da taji abun wani iri tashi tayi da gudu ta haura sama ta shige d’akin ta suna kallo, murmushi Sameera tayi kafin tace “Ita ta amince, saura kai.”

Shima yunk’urawa yayi cike da kunya da murmushi ya nufi d’akinsu da suke sauka idan sun zo nan, Abbas ne yace “Bamu fahimci komai ba Abdul, hakan na nufin ka amince kenan?”

Juyowa yayi cike da kunya ya d’an jinjina kai alamar eh, da sauri ya k’arasa sama shima ya bi kusurwar da zata sadasu da na shi d’akin, Abba ne ya kalli Abbas yace “Amma ya kuka barshi ya tafi baku fad’a mi shi sharad’in ba?”

Abbas ne yace “Abba karku damu da wannan, na muku alk’awarin kawo muku sakamakon gwajin Abdul nan da kwana biyu insha Allahu.”

“Shikenan Allah ya yarda.” Suka amsa da “Ameen.”

Umma da Abba b’angarensu suka koma inda Abbas ya wata kusurwar wacce ka d’auka wani sabon gida ne a ciki, sai Sameera da ta haura sama ta shiga d’akin Raihan, tsaye ta sameta ta saka kayan baccinta tana caje gashinta, zaune tayi bakin gado harta juyo ta kalleta tace “Ammie ke ce?”

Murmushi kawai ta mata, takowa tayi ta zo ta zauna tana turo baki gaba cikin shagwab’a ta rik’o hannun Sameera tace “Ammie, wai akan me Dady yake magana ne?”

Murmushi sosai Sameera tayi tace “Wai baki fahimci me yake magana akai ba? Kee ‘yan matana fad’a min gaskiya kedai.”

K’ara had’e rai tayi tace”Ammie, da gaske na ke fa.” Shafa kanta Sameera tayi tace.”To in tambayeki mana? Tsakani da Allah Abdul baya birgeki?”

Saida ta juya idonta kafin tace “Ammie, yana birgeni mana, kamar yaya na d’auke shi fa.”

Tana ci gaba da shafa kanta tace “To ba kya jin wani abu a game da shi a zuciyarki? Misali idan kin ganshi, ko kuma yayi nesa da ke?”

B1 tare da sanin mahimmancin abinda take tambayarta ba tace “Ammie ba na jin komai, kawai dai ina sonshi a matsayin yayana.”

Kallon fahimta ta mata sosai tace “To kina ganin zaki iya aurenshi? Ma’ana zaki iya yin rayuwar aure da shi ta har abada?”

Ido ta d’an zaro tace “Ammie, irin rayuwar da kuke da ke da Dady? Da kuma Mammy da Papy?”

Saida ta kama kumatunta tace “Good girl, haka na ke nufi.”

Dariya ta bushe da ita ta fad’a k’irjin Sameera ta rumgumeta tana fad’in “Ammie ni kunya nake ji, bana so na yi aure na barku, ina so na ci gaba da zama da ku a gidan nan.”

Sosai ta rumgumeta tace “Hakan na nufin Mamana ta amince kenan?” K’ara tusa kanta tayi a k’irjin ta ba tace komai ba, dan haka ta d’ora da “To karki damu, indai kina son zama tare damu ai abune mai sauk’i, Dadynki zai iya ware muku part na musamman.”

Kunya ce tasa Raihan tashi ta shiga toilet da gudu, binta tayi da kallo kafin ta mik’e tace “Ni na tafi saida safe, ki fito ki kwanta ke ma.”

Daga toilet d’in ta amsa da “Good night Ammie.” Saida ta shiga d’akin sauran yaran duk ta samesu sukayi saida safe kafin ta wuce nasu sashin, saida sukayi rigima da Abbas kafin ta yarda ta kai Ameer wajensu Ammie ya kwana, dan cewa yayi wani cikin zai mata dan yana so tayita haihuwa, haka fa rayuwar gidan nasu take tafiya ba tare da tunanin wata rana bak’in ciki zai iya ziyartarsu ba, ta b’angare d’aya kuma maganar Abdul da Raihan na nan daram, sai dai har yanzu Abbas bai iya maganar gwajin da za’a wa Abdul ba saboda yana ganin rashin dacewar hakan, su Ammie kuma basu sake mishi maganar ba tunda ba abu bane na gaggawa, sai dai kuma Raihan kunyarta tayi yawa sosai ta yanda har yanzu ba wata shak’uwa bace tsakaninsu, dan ko tana zaune a wuri ya zo tashi take da kunya da nutsuwa ta bar wajen, Fadila da Ma’awa kad’ai suke sakewa dashi suna hira amma ita tana jinsu, duk da dai a zuciyarta tana jin yana birgeta, amma bata iya nuna mishi, idan ya koma gidansu ne kad’ai tafi sakewa da walwala, ta b’angare d’aya kuma suna karatunsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, yan watanni kad’an Abdul ya kammala secondary d’in shi Abbas ya turashi jami’ar madina, bayan wani lokaci kuma Jabir kuma shima ya kammala nasa inda ya zab’i yin karatunshi a jami’ar Ahmadu Bello, shima babu wata matsala da yake fuskanta saboda yana tare da magajiyar mahaifiyarsu *Safeena*, kwana tashi babu wuya a wurin Allah sai kuwa su Raihan suma suka samu shiga secondary.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected