BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mik’ewa tayi tana k’ara share hawaye tace “Mu tafi kawai.”

Wucewa tayi ita kuma zata wuce Junaid yace “Iklima dan Allah zan iya sanin labarin Maryama? Dan na fahimci abun na damunta kuma kamar tana yi ne ba da son ranta ba.”

Rik’e hab’a tayi tace ” Ni! Rufa min asiri, wallahi ba zan iya fad’a maka komai ba a game da ita har saita bani izini.”

Kallonta yayi yace “Bima’ana dai kinsai komai?”

“K’warai kuwa na sani.”

Saida ya kalli Maryama dake tafiya ko d’an kwali babu a kai sai riga da siket d’in ta na atamfa ko waiwaye babu yace “To dan Allah inhar ke masoyiyarta ce ta gaskiya ki fad’a min asalin Maryam, ma’ana garinsu, iyayenta, inda da inda suke zaune, idan kika min haka kin gama biyana a rayuwa, ni kuma zan tabbatar na gyara rayuwar k’awar ki da yardar Allah.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Ina k’aunar Mari, kuma ina sonta da shiriya kamar yanda nake so wa kaina, ni labari na bai kai na ta muni ba, dan ni na fito ne da son raina, hasalima ina gari d’aya da iyayena, amma ita na ta labarin akwai tausayi ciki, kuma sau da dama ina cewa ta sake komawa gida, watak’ila mahaifiyarta ta yafe mata, amma sam bata saurare na saboda tayi hushi ita, dan haka zan fad’a maka komai daya shafeta ko da hakan na nufin zamu samu matsala, nasan daga baya zata fahimce ni kuma ta yafe min.”

*Bara muji tarihin Mari.*

Nuna mishi dakalin tayi tace su zauna, bayan sun zauna ta saita nutsuwarta tace “Maryama ‘yar asalin garin *Gouré* ce dake yankin *Diffa*, tana rayuwa kamar kowa ita ma tare da iyayenta, ita kad’ai suka haifa a duniya, dan haka suke matuk’ar sonta musamman mahaifinta, tana samun duk wani abu da take so a duniyar nan, mahaifinta na nuna mata gata duk da cewa ba mai k’arfi bane, tana karatunta na islamiyya da boko, suna tsaka da rayuwarsu cikin farin ciki wata rana mahaifinta yayi had’ari da moto, munanan raunikan daya samu ne suka jaza mishi kwanciya jinya na tsawon shekara biyu kwance a gida, k’afafun shi basa takuwa haka ma ko zama baya iya wa sai kwanci, wannan rashin lafiyar tashi ita ta jijjiga Mari da mahaifiyarta, ta kai ta kawo sun cinye duk wani abu da suke da shi, yan uwa kuma babu mai k’arfin da zai iya d’auke musu wannan nauyin, sun shiga matsi da takura ta yanda Mari har karatunta ya samu matsala, da haka suke rayuwar babu dad’i, rana tsaka sai wani ciwon ya taso mahaifinta a gaba, bayan sun kaishi babbar asibiti ne aka tabbatar musu da hantarshi kuma ta samu matsala, yana buk’atar aiki da gaggawa, haka ma k’ashin bayanshi a karye yake, da k’yar dangi aka samu aka biya kud’in da aka mishi radion (scanning) d’in ma, hakan yasa ido suka raina fata akan kud’in da za’a mishi aiki, gashi ance aikin hantar sai a *zinder* za ayi, kwanansu biyu a asibiti suka ce zasu sallamesu tunda basu da niyyar biyan komai, a yammacin ranar Mari tayi kuka sosai saboda ikrarin da sukayi na sallamarsu, bayan sallah magriba mahaifinta ya dinga wani abu kamar na fitar rai, hakan yasa hankalinsu tashi Mari tana kuka tace ita zata fita ta nemo kud’in, babu wanda ya kula da ita saboda kowa ya rud’e, tana fita kuma ana iska hadari ya had’e gari, sam wannan bai dameta ba haka ta d’auki hanya ba tare da sanin ina ta dosa ba, tayi tafiya mai tsayi aka sako da ruwa kamar da bakin k’warya, ruwa ake sosai tare da iska mai k’arfin gaske, kan hanya babu kowa sai motoci dake wucewa suma ba akai akai ba, duk motar da ta zo wucewa haka zata daga hannu tana neman su tsaya, amma babu mai kallonta bare tasa ran a taimaketa, cikin hakane wata k’aramar mota mai kyau ta zo wucewa a hankali, kamar a mafarki tana d’aga mishi hannu harya wuce sai kuma ya yo baya baya ya tsaya, saurayin matashi ne a cikin motar da ganinshi kamar mai hankali, zuge glas d’in motar yayi ita kuma ta lek’a cikin kuka tace…

“Dan Allah malam ka taimake ni kamar yanda Allah ya taimake ka, mahaifina ne bashi da lafiya yana asibiti kwance, ka taimaka min dan Allah karya mutu.”

Kallonta yayi yace “Wane asibiti yake.”

Da sauri tace “Babba, babba ce.”

Jim yayi kafin ya bud’e mata k’ofar yace “Shigo muje ko.”

Da sauri ta shiga ta ja k’ofar ta rufe, kallonshi tayi tana tattare hijabinta tace “Nagode.”

D’an motsa bakinshi kawai yayi ya tada motar ya wuce, ita kuma sai tattare kayanta take saboda a jik’e suke sharaf har zuba ruwan keyi, yanda suke tafiya a hankali haka ma rywa suke fara dama dama, amma abinka ga ruwan sama sai kuwa wasu ruwan suka sake gabcewa da k’arfinda yafi na baya, hakanne ya tilasta mishi paka motar ya kalleta yace “Ruwan nan sunyi k’arfi dayawa, mu jira su rage sai mu tafi.”

Kai kawai ta d’an jinjina mishi dan ita da a k’asa take babu abinda zai tsayar da ita, a hankali taga yana k’ara kwantar da kujerarshi baya idonshi a lumshe, da ganinshi zaka san kamar akwai abinda ke damunshi shima, lokaci lokaci sai Mari ta juya ta kalleshi amma shi idonshi rufe kamar zaiyi bacci, tunanin mutumin dake son taimaka mata shima a damuwa yake yasa Mari cewa “Mmm…ala..m l…afiy…a? Ko baka da lafiya ne?”

Sam Mari bata tab’a fahimtar muryar da tayi magana da ita ba zata sake d’aukar hankalin mutumin, a hankali ya bud’e ido saboda yanda tayi maganar ya sake tayar mishi da tsikar jikinshi, tasowa yayi daga kwanciyar da yayi ya sake kallonta zaiyi magana, sai kuma ya kalli jikinta wanda ke jik’e da ruwa duk jikinta ya bayyana, duk da zaune take amma saida ya sake jin wani abu, take a wurin shed’an ya fizge shi yaji ya rasa duk wani k’arfin kare kanshi daga abinda zuciyarshi ke raya mishi daya aikata.

A hankali ya kai lallausan hannunshi ya jawo hannunta da yayi sanyi saboda ruwa, bai sauke hannunta a ko ina ba sai kan hantsar wandonshi, yana jin tafin hannun mace ya sauka a inda ke mishi k’aik’ayi sai kawai ya lumshe ido ya sake matse hannunta had’e da nashi hannun, ita kuma da tsoro ya rufeta fizgo hannunta tayi tare da sakin k’ara, da sauri ya kalleta idonshi jawur dasu sai lumshesu yake, cikin k’ak’aro magana yace “Bbbbanda lafiya, ki ta…ima..ka min.”

Cikin firgici ta juya da k’arfi ta kama hannun motar zata bud’e ashe tun shigarta ya rufeta ruf, juyowa tayi ta fashe da kuka tace “Dan Allah malam kayi hak’uri karka cutar dani, neman taimakon ne na…”

Yanda ya k’ura wa bakinta ido da fuskarta ne yasa yake ayyana kyawunta, bai bata damar k’arasawa ba ya fizgota ya had’e bakinshi da na ta, matseta yayi sosai a jikinshi yana kiciniyar yaye mata hijabi, dukanshi ta fara da hannayenta tana tura shi baya tana so ta raba bakinsu, yana jin haka amma kamar bashi take duka ba duk da kuwa har abincinshi take kuma yana jin zafi, sam baya hayyacinshi bare ya fahimci warin da kanta keyi wanda baya samun gyara saboda rashin kud’i gashi kuma ruwa sun dake shi, yanda suke kokawa yasa bai iya cire mata hijabin ba, dan haka ya kwantar da kujerarta ya bi kanta ya taushe ta, yanda take bille bille da neman taimako ne yasa ya raba bakinsu ya kaishi saitin kunnanta ya rad’a mata “Kiyi shiru ke, ba wani abu bane ba, ni zan taimaki mahaifinki har ya samu lafiya, zan baki kud’i masu yawa idan kika barni, kuma fa ke kika tambayeni…”

Yana cikin maganar kuma yake fito da kayan aikinshida hannu d’aya, hannun yasa ya janye siket d’in ta yasa hannu ya shafi cinyarta, jin hakane yasa ta mishi wata bangaza har saida ya kaiwa k’ofa karo, tashi tayi zaune tana neman hanyar arcewa, cikin jin zafi ya sake haye ruwan cikinta ya fara tattare mata siket d’in, ihu ta fara wanda yasa shi rufe mata baki da hannu d’aya, yanda ya sakar mata nauyi ta ji ko numfashi ba tayi da kyau yasa ta saduda cikin kuka tace “Dan Allah malam ka taimake ni kar ka cutar dani, ni fa taimako kawai na nema wurinka, mahaifina yana can rai a hannu Allah karya mutu bana kusanshi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected