BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Juyawa tayi zata fita ya rik’o ta tare da shan gabanta, zaiyi magana ta nuna shi da yatsa fuska a had’e a murtuke tace “Zaifi ka rufe bakinka, idan mun had’u a lahira a mana hisabi.”
Cikin takon k’arfi ta juya ta fita daga d’akin ya bita da kallo, dafe kai yayi ya zauna bakin gadon yana shafa kanshi, da sauri ya kalli wayar dake k’asa tare da d’aukar ta ya kunna, ganin wannan vidéon yasa ya jefar da wayar yasa hannu yana shafa gemunshi, ya d’auka abin yayi sauk’i amma sai yaji bud’o k’ofar daya sake hargitsa masa lissafi, mik’ewa yayi ya juya yana kallonta, ganin ta nufo kanshi da wuk’a a hannunta yasa shi saurin tunkararta yana neman rik’e hannayenta, da yake masifa take ji da bala’i saita zame tare da wawura mishi wuk’ar sai a damtse, cikin sautin wahala ya dafe wurin tare da juyowa gareta ya furta “Ashhhhhh.”
Ido cikin ido suka kalli juna ta masa murmushi tace “Wallahi da haka zan dinga yankan namanka har ka mutu, Abbas ni zaka wulak’anta.”
Tayi kanshi ya cabko hannun mai wuk’a ya murd’e sosai yasa d’aya hannun mai ciwo wanda jini ke zuba ya fizge wuk’ar, jefar da ita yayi ita ma ya cillata kan gado ya nuna ta da yatsa yana fad’in “Sameera ki saurare ni mana, ya zaki dinga abu kamar wata marar hankali? Kar kisa na ji miki ciwo a banza mana, shin zina a kaina aka fara? Ko kuma kin saurareni na fad’a miki abinda ya faru ne? Haka kawai zakkk…”
Bai k’arasa ba ta mik’e da k’arfi tana girgiza kanta gashinta duk ya yamutse tasa hannayenta ta tura shi baya, bubbuga k’irjinta tayi cikin disashewar murya tace “Ni ce marar hankalin? Kai ne mahaukaci bani ba, kai da ka zubar da mutumcinka wajen k’aramar yarinya, kai ko kunya baka ji ko kunya ba? A cikin gidanka ka shigo da karuwa, shine harda k’aryar cewa wai ka bigeta ne a hanya shine ka taimake ta, kaji kun…”
Wuyan rigarta daya finciko yasa ta yin shiru, saida ya kai bakinshi saitin nata bakin yace “Kisan me kike fad’a min Sameera, bana son maganar banza, ki zauna ki saurare ni.”
Ya k’arashe da sakinta yana nuna mata kan gadon ta zauna, fashewa tayi da dariya ta nufi wajen dressing miror d’in shi ta d’auki kwalbar turare mai kyau da tsadar gaske ta buga a madubin tace “Wai umarni kake bani? To ai yanzu ni bana ganinka da wani mutumci ko kad’an wallahi, kai Abbas ba…”
Marin daya zabga mata a fuska yasa ta dafe kunci tana kallonshi, da yatsa ya sake nunata yace “Wallahi ni banyi lalacewar da har haukanki zai k’are a kaina ba, Sameera kisan ni mijinki ne bai kamata ki d’aga muryarki sama da tawa ba bare har ki dinga fad’a min duk shirmen da ya zo bakinki, tabbas ina sonki, amma son da nake miki ba shi zaisa na miki shiru ki ci mutumci na ba, wallahi tsaf zanyi k’asa k’asa dake a wurin nan, iskancin banza kawai, zuciya kanki farau, ko ke kad’ai ce me zuciya a k’irji? An fad’a miki kowa baya jin zafi ne? Wallahi ba dan tausayinki ba da rashin sabo a gare ni da dukan tsiya zan miki har ki dawo hankalinki, amma duk da haka zan iya hukuntaki ta hanyar data fi dacewa dake.”
Hannunta ya kamo da niyyar wurgata kan gadon sai kuwa ta d’auko wata kwalbar turare doguwa, cillata yayi kan gadon ya bi kanta ya haye yasa k’arfi ya b’arka rigarta rantsetsen leshenta wanda yaji kud’i da d’inki mai kyau, shi kanshi yayi mamakin yanda ya iya raba rigar biyu saboda kark’on leshin, zai fizge bras d’in ta yaji saukar kwalbar nan a kanshi wanda take jini ya sake gabce mishi a kai, gefenta ya fad’a ya dafe kai ya rufe ido sosai, mik’ewa tayi cikin k’arajin murya tace “Wallahi ka gama kusanta ta Abbas, indai ina raye ba zaka sake shigar da banzar…”
Jin an shigo d’akin ne yasa ta shiru ta kalli k’ofar, Khalifa ne ya shigo wanda hayaniyar iyayen nashi da jin lallai ba lafiya ba yasa shi shigowa, a hankali ya tako har ya tsaya gabanta yana kallonta, a tsawace tace “Lafiya? Meya kawoka?”
Juyawa yayi ya kalli Abbas daya d’ago ido d’aya ya kalli Khalifa, matsawa yayi kusanshi yace “Dady ciwo kaji?”
D’auke hannunshi yayi wanda yasa jini sake gangarowa har yana neman rufe mishi ido ya mishi murmushi ya girgiza kai alamar a’a, juyawa yayi ya kalli Sameera dake k’ok’arin cire rigarta yace “Ammie meya samu Dady?”
Tsayawa tayi daga shirin gyara rigar ta nuna mishi k’ofa tace “Dan ubanka fice min a d’akin nan kafi na ji maka ciwo.”
Wani kallo Abbas ya mata na mamaki, shi kanshi zai so Khalifa ya fita danya nuna mata shi ba sa’anta bane har yanzu, cikin sanyin jiki Khalifa ya juyo ya kalli Abbas yace “Dady dan Allah ku daina fad’a, duk gidan nan fa ana jin muryoyinku, mun saba ganin kuna rigima da fad’a, amma waccen fad’an naku yana saka mu nishad’i wani lokacin ya kuma bamu dariya, amma wannan ba kamar kullum ba, dan Allah Dady karka biyewa Ammie.”
Kanshi ya dafa zaiyi magana Sameera tace “Iyee! Khalifa ni zaka wa iskanci? Wato halin ubanka ne zaka d’auka ko? Shine ma zaka ba hak’uri ba ni ba? Kasan me yayi kuwa? Bara ka gani to.”
Jujjuyawa ta fara kamar mahaukaciya tana neman wayar nan, can ta hangeta kusa da k’ofar toilet inda Abbas ya cillata, da sauri ta d’auko ta bud’a vidéon nan zata tunkaro Khalifa tana fad’in “Dubi tsiyar da mahaifinkkk.”
Marin da Abbas ya wanka mata lafiyaye a kumatu yasa ta sakin wayar ta fad’i ta kaiwa k’ofar toilet d’in karo, a fusace yasa k’afa ya take mata k’afafu biyu ya juyo ya kalli Khalifa ya nuna mishi k’ofa yace “Fita anan, ka umarci k’annan ka ku je gidan Naseer.”
Jiki a sanyaye Khalifa ya nufi k’ofa yana kallon mahaifiyarshi dake yashe k’asa, saida ya kai k’ofa zai rufe yace “Dan Allah Dady k…”
A tsawace Abbas yace “Ka fita nace.”
Da sauri ya rufe k’ofar sai hawaye, da gudu ya fita neman taimako gashi kuma Ammie bata nan, a k’ofar gida ya samu Abba ya sanar dashi babu lafiya a ciki fa, a sukwane suka taho tare…
Yana ganin fitar Khalifa ya cakumi gashinta ta baya ya buga kanta da bangon wurin, hakan ya haddasa mata sakin k’ara mai k’arfi da sauri kuma ya sunkuya ya sa hannunshi ya rufe mata baki, da k’afa ya tura k’ofar ban d’akin ya sake cakumar gashinta ya jata cikin ban d’akin, yana zuwa k’aton bahon wankan dake cike da ruwa ya kinkimeta sai kuwa ji kake tamjam ya sakata ciki, da k’arfi ta yunk’uro tana neman tsira ya tausa kanta ciki, hannayenshi ta shiga k’ok’arin b’anb’arewa daya taushe mata kai, amma dayake Abbas yana son ya koya mata hankali ta gane shine gaba ba ita ba, a kullum tana tunk’aho da jiji da kanta da zuciyarta da jarumtarta, rufe ido yayi ya k’i sakinta yana kallon yanda take son ta fito ta numfasa, amma ya kawar da kai daga kallonta yana fad’in “Wai ba kasheni zakiyi ba? To ni zan fara kashe ki in ya so mu had’u a lahira a mana hisabin,.”
Kallonta yayi yace “Wai ni kam ba kece Sameera mai zuciya ba da d’aukar fansa? To ina zuciyar ta ki? Shin ba kece ba kya yafiya ba duk abinda aka miki sai kin rama? To gani ki rama mana, ki fito ki rama nace.”
Saida yaga ta galabaita sosai ya saketa ya juya zai fita daga toilet d’in, da k’arfi ta yunk’uro ta zuro kanta waje tana tarin wahala da kakarin amai, juyowa yayi yana kallonta wani tausayinta ya baibayeshi da tuna cewa fa shine mai laifin, dawowa yayi ya tallabota ya d’auko ta ya fito da ita har kan gado ya direta, kallon fuskarta yake yana gyara mata gashinta daya had’e wuri d’aya yana zubar da ruwa, tallabo fuskarta yayi yana kallon cikin idonta cike da rarrashi yace “Dan Allah Meerah ki kwantar da hankalinki muyi magana, ni da ke yan uwan juna ne kuma miji da mata, ki bani had’in kai mana mu fahimci junanmu, shin kina ganin wannan abinda kike har kina so ki kashe shine mafita? Sam, zaki iya rayuwa ba tare da ni ba?”