BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Bai barshi ya k’arasa ba dan shi kanshi ko da ya ganshi a ranshi ma yace ai dole ya hak’ura, mik’ewa yayi cike da dauriya yana fad’in “Kai haba ba komai Elaji, tsautsayi idan ya wuni baya kwana ai.”
Hannunshi ya damuk’o ya rik’e sosai yana fad’in “Wallahi hakane, kawai wata waya ce aka min da nake da tabbacin ba lafiya ba, kasan ai ita yar gwamnan naku nake aure, to ita ce na baro gida da tsohon ciki, shiyasa hankali na baya kwanciya idan na fito.”
Murmushin dole ya mishi yace “Ah to Allah yasa alkairi, Allah ya raba lafiya, ba komai kaje kawai.”
Da sauri yace “A’a ka bari na aje ka asibiti ko?”
Shima da sauri yace “A’a wallahi ka barshi, ai banji ciwo ba.”
Mik’ewa yayi ya mishi sallama ya juyo zai koma mota, murmushi yayi murya k’asa k’asa yace “Da ubanka ne zai kaika asibitin, daka yarda ka shigo mota ta da nufin na kaika asibiti da sai dai a wuce da kai morgue daga nan, kad’an ma ka gani wallahi Ummy ta cece ku.”
Bayan ya dawo daga inda yaje gida ya wuce, yara na ganinshi suka ce ai sai dai ya koma dasu, da k’yar ya lallab’asu suka rabu, saida ya keb’e da Ummy yace “Ummy dan Allah ki yafe min duk laifin da kika san na miki, kina sane ko rashin sani.”
Da murmushi a fuskarta tace “Ba komai Ammar, na.
yafe maka duniya da lahira.”
“Nagode Ummy.” Ya fad’a yana musu sallama ya bar gidan, saida yaje ya samu Hamna ya shiga fad’a mata abinda ya faru dalla dalla sala sala, ita dai tayi dariya kamar cikinta zai fashe, daga bisani kuma ta raka shi addu’a.
*Rayuwa kenan*, abun kamar jiya ne aka fara sai gashi yanzu da aurensu *shekara uku* kenan, yanzun ma namiji ta haifa wanda ya ci sunan *Hassan* suke mishi alkunya da *Elhaj*, Ammar ya tayar da billi shi fa yan uku yake so ya haifa, Hamna kuma dake k’ok’arin cika alk’awarinta duk in yana tijara yanzu sai dai tayi gum da baki tana saurarenshi, in yayi ya gaji sai ya koma ya fara juye mata yana kiran ta raina shi ta d’aukeshi mahaukaci ne, duk da haka bata kula shi sai dai ta bar mishi wajen har sai ya gaji dan kanshi.
*Yau* hankalin Jibril in yayi dubu ya tashi, yarinyar da yake saka mata ido, yarinyar da duk inda zata je tare da dreba take, amma aka wayi gari da sunan taje école kawai ya had’e da ita a wani babban store tare da k’awayenta da kayan makarantarsu alamar daga can suka wuce, hakan na nufin tana fita daga makarantar kenan? Ya so mata dukan mutuwa sannan yaji daga ina suke kuma ina zasu je, amma Jamila ta shiga tsakani tace ba za ayi haka da ita ba, tunda tace abu suka je siya kuma su koma kawai ya hak’ura, amma tsoron kar wani ya mishi kutse a rayuwar yarinyarshi da kuma kiyaye maimaituwar tarihi sai kawai ya yanke wani tsatsauran hukunci a kanta.
*Sadiq* zaman d’a yake ga Husseina, ya yarda da yaron yana d’aya daga cikin masu kula mishi da mangazarshi da ake aje kaya, ganin tunda yan uwa ne kawai yasa shi cewa in yana sonta ya bashi aurenta, yaro ya ga banza ta ina zai bijire? Sai kawai yace yana so shima ya amince, kamar wasa sai manya suka shiga maganar akayi komai a gaggauce, inda yace zata kammala karatunta a gidan mijinta.
*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:40 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_78_
*Zo* ka ga uban amarya uban d’aurin aure Ammar, shi Jibril ya bawa d’aurin auren wanda hakan ya masa dad’i, Mari tayi jarabar a kai mata Huda ayi biki ranar bikin sai a dawo da ita, amma Jibril sam ya gama fita harkar Mari yace ai kawai ta zo in tana so amma babu inda Huda zata je, har Amar saida ta ma magana a waya wai ya lallab’ashi, amma shima hak’uri ya bata yace Jibril bai amince ba.
*Yau* d’aurin auren Huda, Ammar ya kashe d’aurin hula ya k’ayatu cikin babban riga ta wani gallelen boyel bleue bics, ya gama had’uwa da tsaruwa fiye da ma angon.
Hamna ma ta gama shiryawa cikin shaddarta gezna colour bleue omo zasu tafi tare, tsaye suke dukansu gaban madubi yana ci gaba da gyara zaman hularsa, ita ma kallabi ta gama d’auri ta d’auki turare zata fesa ya fige yace “Turaren me kike buk’ata?”
Kallonshi tayi tace “Cikin mutane fa zan shiga.”
Shareta kawai yayi ya aje kwalbar ya d’auki na shi turaren zai fesa, da sauri ita ma ta fige tana ja baya da gudu tana fad’in “Tunda ban saka ba wallahi kai ma ba zaka saka ba, duk mu tafi haka.”
Juyawa yayi ya kalleta yace “Hamna kawo min turaren nan.”
Hanyar fita tayi tana fad’in “Ba zan bayar ba Allah.”
Ko da ta fita d’akinshi ta nufa da niyyar shiga ta rufe ta d’auke turarukan dake nan, dan tasan su zai nema duk da dai yafi aikida wanda ke d’akinta, amma kafin ta rufe ya biyota yana tattare babbar rigar yana fad’in “Ke in rashin mutumcin kike ji saina kwab’e wallahi mu daku yanzu nan.”
Baya tayi tana fad’in “Me yayi zafi da zamu daku ni da kai? Turare dai ne ba zaka saka ba kai ma in dai ban saka ba.”
Ko da taga ya tafi a guje zai kamota saita tsorata kawai ta buga kwalbar k’asa ta kuwa fashe saboda akan tiles ne babu carpet wurin, bud’e baki yayi da ido yana kallon kwalbar.
Saida ya b’ata rai ya kalleta yace “Hamna ni kika fasawa turare? Ni Hamna, ai ko zaki ga rashin mutumci a gidan nan.”
K’uri ta masa da ido tana so tace ba dagangan tayi ba amma ta kasa, cire babbar rigar yayi ya aje kan gado ya tunkareta, ihu kawai ta saki dan ba zata iya guduwa ba kan hanyar fitar yake tsaye, saida ya tak’ark’are yasa k’arfi ya kimkimeta gaba d’aya, bai tsaya komai ba ya shiga wani irin juyin bala’i da ita yana hajijiya, tun tana ganin d’akin tana gane komai, har saida jiri ya d’ebeta ta dinga ganin d’akin na juyawa gaba d’aya.
A hankali taji kamar kanta zai cire duk tunani da lissafinta sun fara barin kwanyar kanta, rik’eshi tayi gam ta rintse ido tana jiran ranar da zai sauke ta, saida ya gamsu cewa ta kuru yanzu kad’ai ya direta k’asa, ganin wani luuuuu da tayi kamar zata kifa yasa shi b’anb’are hannayenta data rik’eshi gam, ai tuni d’aurin d’an kwalin ya rigata kaiwa k’asa duk suka watse a wurin, dafe k’asa tayi sosai saboda har yanzu juyawa ake da ita.
Rigarshi ya saka ya kalleta yace “Idan ki kayi wasa Hamna d’aurin auren nan da za ayi har da nawa za’a d’aura, kuma ke nake jira karki b’ata min lokaci.”
Saida ya kai k’ofa zai fita ya juyo yace “Amma Hamna Allah ya saka min wannan wulak’ancin da kika min, yanzu waccen turaren kike sona saka mai warin yan wuta?”
Hamna da a lokacin kad’ai ta fara jin dama dama kallonshi tayi tace “Kenan kasan k’amshin yan wutan?”
Saida ya wani had’e fuska yace “Ina d’an ji kad’an kad’an.”
Mik’ewa tayi tana ganin yana juya mata a hankali tace “A jikinka kake ji ko?”