BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ka had’esu ka sha da nono ko madara.

_Minanas_
_Hakk’in daka_
_Cukui_
_Zuma_

Saika had’esu kana sha da madarar shanu d’anya

_Kankana_
_Gwanda_
_Abarba_
_Pomme (Apple)_
_Zuma_
_Madara peak_

Kayi jus na su kana sha.

_Habba cokali 2_
_Garin rid’i cokali 3_
_Garin raihan cokali 4_
_Yayan zogale yanda kake buk’ata_

Ka zuba cikin dahuwar tantabaru mace da namiji.

_Dabino_
_Nonon rak’umi_
_Hulba_
_Ayaba_
_Abarba_
_Zuma_

Ka tafasa nonon rak’umin idan ya huce saika juye shi cikin markad’add’sn dabino da ayaba da abarba ka zuba garin hulba kasha.

*Kwana uku* daya rage kowace rana da shagalin dasu Sayyada suka gwangwaza, su da abokan Ammar sunyi shagali sosai ba kama hannun yaro, Hamna kam mulkinta take buga musu son ranta, har kamu akayi cikin gidan nan amma babu wanda ya ga k’afar amarya, anyi anyi ta shirya sai ma ta fashe da kuka dole aka k’yaleta, sai nan d’aki suka mata wanka turare, Ammar kam ko a jikinshi saida yaje gaban iyaye ya kwashi shokinshi ya duk’a suka fesa masa turare kafin ya bar wurin, wannan karan ma gabjejen sa ya aiko dashi ayi girkin biki tare da jus kamar za ayi wanka dashi.

*Ranassss*

Ya baje cikin shigar fararen kaya, lieutenant colonel da Gambo da Labaran duk shigar kala d’aya ce, su Amar Jibril da sauran dangi ma matasa kamarsu duk suna cikin fararen kaya, to anko ne da aka sa kowa yayi dan dole ko bai shirya ba, anan lieutenant ya bayar da auren yarsa inda Labaran ya karb’a wa d’ansa (kune gayyar tsi…), daga k’arshe dai an d’aura auren *Hamna Harouna Suleymane Gaga* da *Ammar Hassan Suleymane Gaga* akan sadaki jaka hamsin mafi k’arancin dan albarkar auren.

*Yanzu ciwon kaina zai k’aru ku taimaka min da panadol da paracétamol da doliprane a kusa.*

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:39 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_70_

 

*Biki yayi biki* ta bakin wani mawak’i, ba kid’a ba wak’a amma fa holewa ake, b’angarenshi ya sake tabka mishi gyara na rashin mutumci, haka kuma yana can ana gyara masa gidansa dan yace wannan ita ce abokiyar gwabzawa sai sun matsa daga kusan manya karsu kashe su basu shirya ba. Ita kanta Hamna k’awayenta sun mata bajinta sosai, dan har daga Niamey da Katsina wasu sun zo aurenta, taji dad’i sosai na ganinsu a kusa da ita a wannan lokaci.

Ko da magriba tayi Ummy ta tsaya tsayin daka wajen gyara amaryarta kuma surukarta, wata mahaukaciyar doguwar riga ta tsadadden tissue aka saka mata, yaji d’inki sosai mai d’aukar ido da d’aukar hankali, tun daga sama zuwa hannaye har gwiwa a matse yake, amma daga k’asa sai aka bud’e sosai yayi tsatsaye har yana jan k’asa, kwalliya ta d’auka daga wajen wata k’awarta ta ban mamaki, kwalliya ce daidai da fuskarta inda aka d’ora komai kan muhallinsa, d’aurin d’an kwali kam kamar ba hannu ne yayi aikin ba, dama duk wani abin da zata saka saida Ummy ta turare shi har da pant da bras d’inta, sannan ita ma aka sa ta zauna kan kujerar turaren bayan an turare mata jiki, abubuwan da Ummy ta k’ara bata tasha ta ci taji tana neman yin amai, tana daf da fashewa da kuka tana fad’in “Wallahi Ummy amai zanyi, ya ishe ni haka dan Allah.”

Da sauri mai kwalliyar tace “Rufa min asiri Hamna karki zubo da hawaye a idon nan.”

Hararanta tayi tace “Dallah kwalliyar me?”

Karb’a Ummy tayi tace “Shikenan to barshi haka, ai muna tare dake a gidan.”

Ummy zata fita daga d’akin wayarta tayi k’ara, ko da ta d’auka tace “Ango ya akayi?”

Daga inda yake yace “Ummy kun shirya? Mota fa na nan tafe d’aukar kankana.”

Saida ta kalli Hamna dake ta had’e rai k’awarta na cewa ta dinga murmushi dan Allah sannan tace “Me ye na sauri Ammar? Kuma nan da can d’in zata shiga mota? To ai ko hannu aka sa sai a tura motar k’ofar gidan.”

“A’a Ummy sarauniya ce yau, bari mota zata kaita.”

“To shikenan.” Ummy ta fad’a dan abar canzen, ta d’auka mota d’aya ce yake nufi da zata d’auki amaryar, amma abun mamaki da firgita tunanin mai rai sai jininin motoci suka ji, sanda aka fito ne suka ganewa kansu sarautar Allah, kai Umy ita dai a ganinta motocin nan bana abokanshi bane kad’ai kamar harda hayarsu akayi, mota ta bawa guda arba’in baya ta kusa kaiwa hamsin, to wace tsiyar zasuyi da su, in suka shiga ina za’a kaisu, to wata motar ma yanda ta zo haka ta juya ta koma bata d’auki ko sauro ba bare mutum.

Bakin duniya, da suka kwashi matan mutane gudu na idon duniya suka dinga yi dasu, aa fa gudun ma a cikin tsari suke yin shi, dan babu motar data fita daga layin da suke, saida suka lula suka kai k’uryar ali d’an sofo sannan suka kutsi hanyar da saida ta sada su da zarya ta k’arshen k’ashe-sheshe, yawo kawai sukayi mutune tun ana jin dadi su dai har wani ya fara k’orafi saboda dare ya k’ara yi, sai lokacin kad’ai suka koma aka aje amarya aka shigar da ita gidan ta.

Iyaye duk kanta suka taru inda suke mata nasiha kan hak’uri, saida kowa ya gama na shi Hajia da Husseina su dai suka fad’a mata ta zama mai d’auke kai daga lamarin bawan Allah nan, wannan taurin kai da fad’a masa magana kai tsaye ta kiyaye, tayi kamar yer uwarta har ta koma ga Allah ba’a tab’a jin ko sautin muryarsu ba da sunan tashin hankali, ita dai sauraronsu kawai take, amma ba zata iya abinda Amna tayi ba, wacce ta fad’a mata idan wani ya b’ata mishi rai saiya huce kanta ta hanyar darzata kan gado ko kuma ya mata wanka da ruwan sanyi ko sata cin abincin da batayi niyya ba, to ita yaushe zata iya da kwatirarsa? Ai ya kasheta ko ita ta kashe shi ne kawai.

A sannu sannu aka watse aka barta ita kadai, zaune kan gado tana k’arewa d’akin kallo, saida ta gama tas sannan ta mayar da fuskarta cikin babban mayafinta tana kallon hannayenta masu ban lalle, Ammar? Ammar? Mahaukaci ne fa suka had’ata dashi.

*Uwar Lalla kinji fa?*

*Yana* saman hanya tare da Amar na tuk’i sai su Junaid a baya lieutenant ya kira shi, d’auka yayi lieutenant yace “Kana ina Ammar?”

“Abba ina kan hanya.”

Cikin d’an jin kunya yace “Ka siye kaza ne?”

Murmushi yayi yace “Abba duk angon dake son jin dad’i dolenshi ai ya siyo kaza.”

Su Amar kallonshi sukayi sai Abba da yace “To ka siyo guda biyu ina son d’aya nima.”

Tafin hannu yasa ya rufe fuska wai kunya yana fad’in “Lah Abba na wallahi ka bani kunya, kai ma kaza kake so? Kenan dai uwata zata mana k’ane.”

Had’e fuska yayi yace “Kai bana son iskanci, ita kad’ai ce mai k’wan haihuwa? To da uwarka nake ni.”

Ido ya zaro cike da shak’iyanci yace “Kai Abba na Ummy fa, kayi hak’uri dan Allah kaje wajen uwa Zeitu.”

“Ammar.” Ya fad’a cikin muryar karsashi, a hankali yace “Na’am Abba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected